← Book details Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 89

Sashe 88

Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya sa ya ci gaba da cewa. " "Ubangiji shi ka ai ne abin bauta saboda bai haifa ba kuma ba a haife shi ba, Shi ka ai tal ba shi da abokin tarayya. Annabi Muhammad S.A.W BawanSa ne kuma ManzonSa ne, Ubangiji ba ya mutuwa ba ya tsufa don haka ku ji tsoron Allah ku hau turbar addinin Musulunci." "Muna goyon bayan wannan Addinin kuma a shirye muke mu kar e shi hannu bibbiyu." Gab aya mutanen wurin suka amsa masa. Farincikin su Sarki Sulaiman ya bayyana a fili Dattijo Maharaz zai yi magana suka ga Sarki Sulaimanu ya fara zubar da wallah. "Yanzu shi kenan Fargi ba ta rabauta da samun wannan Addinin ba? Kaico rayuwa ban so haka ba. Na so a ce ta rabauta amma kullin gaya mini take za ta kar i Addinin Musulunci idan lokaci ya yi Allah ya ji anki Fargi." Jin haka ya sa Jawahir ta fara zubar da wallah, Sarki Abdul'aziz ya dafa kafa arsa sannan ya ce. "Sarki Sulaimanu ita rayuwa duk yadda ta zo wa Bawa dama can Allah ya addarar masa ita a haka, tun ran gini tun ran zane. Dama can Allah ya addari Fargi ba za ta kar i kalmar Shahada ba, amma kuma wani ikon Allah sai ya zama silar ta ne Al'ummarta za su rabauta da shi, koda Fargi tana raye aka yi haka idan ba ta da rabo ko duniya za ta ha u a kanta ba za ta kar i Addinin Musulunci ba. Mu manta da rayuwar baya mu fuskanci ta gaba, ina ganin haka zai fi Sarki Sulaimanu." Rufe Bakin Sarki Abdul'aziz Alaramma ya ora da cewa. "Akwai wani jan hankali da zan yi gare ka Sarki Sulaimanu da sauran mutanen wurin nan, duk da a yanzu girma ya kamaka. Ka sani kuskure ne babba yaro ya auri yarinya ba tare da sani ko amincewar iyayenta ba. Wallahi-wallai tun da Allah ya addari yarinyar nan Jawahir za ta fito tsakanin kai da Fargi da ka sanar da iyayenta babu abin da zai hana faruwar aurenku sai ikon Allah. Sau-tari akwai abin da idanunmu suke rufewa akai wanda ba alkairi ba ne amma idan muka yi ha uru muka yi addu'a sai kuma mu ga abin ya zo mana ta ruwan sanyi." Ya waiga wurin Mahaifinsu Fargi sannan ya ce. "Babu camfi a addinin Musulunci ko tsubbu, don haka ya zama wajibi ku zubar da duk wasu tsubbace-tsabbace da tsafe-tsafe hatta wannan abi'ar ta hana auren bare dole ku soke ta. Domin kuna ganin irin abin da ya haifar, ga dai yarinya har ta girma shin kun isa dakatar da addara ne?" Lokacu aya suka ce. "A'a." Alramma da Malam Liman suka ci gaba da yi musu nasiha mai ratsa zuciya daga arshe ya la anta musu kalmar Shahada yana fa a suna maimaitawa. Mahaifi , mahaifiyar Fargi da yayyanta suka rungume Jawahir suna kuka gwanin ban tausayi. Babban Malami ya umarci su Sarki Abdul'aziz da su koma Masarautarsu shi zai koyar da su yadda ake wankan shiga Musulunci da sauran hukunce-hukunce da suka shafi addini. Sarki Sulaimanu kai tsaye ya ce zai tafi da Mahaifan Fargi don idan suka tafi da Jawahir suma ba su yi musu adalci ba, saboda ya lura da tsantsar soyayyar da suke yi wa mahaifiyarta, kafin su kai ga tafiya labari ya iso gare su Shugaba Zurufu ya ca a wa kansa wu a ya mutu har lahira. Mai martaba sai da ya tara duka matansa sannan ya sa aka kira masa Yaya Halima, tun da ta shiga akin gabanta yake fa uwa don ta san tatsuniyar gizo ba ta wuce ta i ba. Sai da ya yi sallama suka amsa sannan ya dube ta ya ce. "Halimatu ga iyayenku a zaune muna so mu ji hukuncin da kuka yanke?" Idanunta suka ciko da wallah ta ce. "Allah ya taimake ka ba na i maganarka ba ne, amma duk lokacin da na tuna mijin Fatima zan aura sai hankalina ya tashi, ni fa yaya ce a wurin Fatima Sarki Abdul'aziz kuma sirikina ne..." "Gaba aya a kalamanki babu hujja Halimatu, ya kamata mu zubar da al'ada mu kama abin da Addini ya zo da shi, babu inda aka ce don anwa ta mutu yaya ba za ta auri mijinta ba, amma idan kuna ganin ba ku aminta ba; ba za mu yi muku dole ba." Mai martaba ya katse ta. "Na amince ranka shi da e har cikin raina." Murmushi ya bayyana a saman fuskokinsu. "Allah ya yi muku albarka." Yaya Halima ta amsa da Amin. A wannan ranar Mai martaba ya rubuta wasi a ya aika ta Masarautar Huddam wurin Sarki Abdul'aziz, na amincewa da aura masa Yaya Halima a matsayin matar aure. Tafiya suka yi mai nisan gaske har sai da suka kwana a hanya sannan suka arasa, a lokacin da suka isa Masrautar Huddam cikin zumu i Mai gado ta nufi sashenta domin sanar da Malam Umaru sabon labarin ban al'ajabin da ya faru a garinsu Fargi, sai dai turus ta yi sakamakon ganin mutane ana yun urin fito da makara auke da gawa a ciki. Kamalu na ganinta ya matsa gefe yana zubar da wallah. "Baba ka na ina?" Muryar Jawahir ta kara e wurin a lokacin da ta taho da gudu, ita ma turus ta yi tana bin mutane da makara a hannu da kallo. "Kamalu mai ya faru?" Mai gado ta tambaye shi a ru "Ki yi ha uri Mai gado, dukkan mai rai mammaci ne dukkanmu can ne arshenmu. Malam Umaru jinya ta are wa'adi ya cika..." "A'a Baffajo ba dai Umaruna ba, Umaru a raye na tafi na bar shi ka bar fa a mini ya mutu." Mai gado ta katse Baffajo a firgice. Da sauri Jawahir ta tunkari Kamalu, hawaye na zuba ta furta. "Don Allah da gaske ne abin da Baffajo ya fa a?" Gya a mata kai ya yi jin haka ya sa Jawahir ta rushe da matsanancin kuka. Sai da aka yi wa Mai gado nasihohi da ban baki sannan ta matsa gaban gawar Malam Umaru ta fara yi masa addu'a, ta ora hannunta a saman jikinsa kuka ya ci arfinta. "Ina fargabar ranar da zan mutu na bar ku ke da Jawahir Mai gado, don Allah ko ba na raye kada ki yi wa yarinyar nan ri on sakainar kashi." "Kin san ranar aurin auren Jawahir In shaa Allahu duk wanda zai aure ta inki iri aya zan yi mana ni da shi." "Mai gado me ya kamata mu fara siya na auren yarinyar nan ne?" Ire-iren maganganun Malam Umaru na baya suka dawo mata cikin kunnuwanta. Inna wuro ce ta janye ta sannan aka fitar da gawar. Sarki Abdul'aziz shi kansa ba aramin ka uwa ya yi da jin mutuwarsa ba. Shi ya sallaci gawar da su Sarki Sulaiman sannan aka wuce da shi gidansa na gaskiya. Sai da suka yi wanka suka huta suka ci abinci sannan Sarki Sulaiman ya bu aci tafiya da Jawahir a cewarsa bayan wani lokaci zai dawo da ita, saboda so yake ta san dangi kowa ya santa, da farko Mai gado ta so nuna rashin jin da inta hakan ya sa Jawahir ta i amincewa da bin Mahaifinta har sai da Mai gado ta an tsawatar mata. Gaba aya suka unguma har mahaifan Fargi suka nufi masarautar Sarki Sulaimanu. Sarki Abdul'aziz da saurah Fadawansa suka yi musu rakiya har bayan gari. Sai dai kafin su tafi Sarki Abdul'aziz ya tabbatar wa da Sarki Sulaimanu Mahaifan Fargi za su ci gaba da zama a cikin Masarautar Huddam gaba aya. on Mai martaba da ya arasa wurin Sarki Abdul'aziz ba aramin faranta masa rai ya yi ba, don haka ya samu Waziri da sauran 'Yan uwan mahaifinsa wa anda suke raye ya tura su domin su yi duk abin da ya dace. Da yake ya san hannunka ba ya ru ewa ka yanke ka yar sai da ya sa aka yi wa su Ciroma da Galadima magana, Ciroma ne ya amince da zuwa domim shi tuni ya zubar da makamansa amma Galadima ko kyakkayawar amsa bai bayar ba. Wani abin farinciki suna isa Mai martaba ya sa aka aura auren Sarki Abdul'aziz da Yaya Halima, sannan a wannan ranar masu kawo ta suka nufi Masarautar Huddam. Sarki Abdul'aziz bai yi mamaki ba domin ya san Mai martaba mutum ne mai karamci da dattako, wa ansu sababbin akuna da aka gina aka gyara wa Yaya Halima ta tare a ciki. Nan da nan labarin auren Sarki Abdul'aziz da Yaya Halima ya kara e cikin masarautar Huddam, ba in da suka rako ta Takawa ya sa aka ha a musu Sha tara ta arzi i. Da Sailuba ta ji labari tamkar ta ha i yi zuciya ta mutu saboda ba inciki, da gayya 'yan matan da manyan matan Bayi suka din ga shiga suna yi mata habaici saboda ba inciki, sai ta rushe da kukan nadama da da-na-sanin abin da Mahaifiyarta ta ja mata, don ta san har abada ta on da ta yi musu ba zai ta a gogewa ba. Kuma a washegarin da aka kawo Yaya Halima ne Sarki Abdul'aziz ya na a Inna wuro a matsayin Jakadiyarsa, wannan matsayin sai ya zo musu a bazata daga ita har Baffajo. Takanas suka zube a cikin fadarsa suka shiga zabga masa godiya, shi kansa Kamalu ba aramin da in hakan ya ji ba don ya san fiye da haka ma su Inna wuro sun cancanta. Bayan da Sarki Sulaimanu ya gama gabatar da Fargi babu mutum aya da ya amince da kalamansa ciki kuwa har da Mahaifiyarsa, kuma nan take ananan maganganu suka fara tashi wasu ma suka fara gulmar Sarki Abdul'aziz ya haifi Shegiya babu aure, takanas ya sa aka kira masa Jakadiya da Waziru wa anda suka zame masa Shaida, da farko Waziri har zuciyarsa ta fara wassfa masa ya aryata Sarki Sulaimanu amma da ya tuna auyen da suka je da amininsa da ya zama waliyin Fargi, za su iya furta gaskiya nan take ya zayyane gaskiyar abin da ya sani. A hakan ma Mai babban aki ba ta yadda ba sai da ta sa aka tashi wa ansu manyan Fada zuwa garin da Waziru
Chapter 88 · 0% Book details