Sashe 69
Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sannan ya arasa bakin Shurim da ke akin nan take ace. Aljanin da ke cikin surar Baiwar Maimuna ya mi e ya yi wa Sarki Abdul'aziz sallama, kai tsaye ya wuce akin da aka wuce da su Fulani Umaima. Cike da al'ajabi su Inna wuro suka russuna suka yi wa Takawa da Kamalu sallama, ta ri e hannun Jawahir Takawa ya sa Dogarawan ofa suka yi musu rakiya har zuwa can sashensu na Bayi. A cikin zuciyar Sarki Abdul'aziz yana cin alwashin wannan ne kwana na arshe da su Baffajo za su sake yi a sashen Bayi. *SHU'UMAR MASARAUTA* *36* *Littafin ku i ne 500 idan kina bu ata za ki biya ta wannan Account in Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.* Duk da Fargi ta san cikin da take auke da shi, sai ta nuna wa Shugaba Zurufu sam ba ta san abin da yake nufi ba. "Shin ka fara zargina ne Shugaba Zurufu?" Tambayar da ta wurga masa kenan don ta atar da hankalinsa. Sai da ya saki murmushi sannan ya furta. "Yaro man kaza! Shin kina ganin za ki iya oye mini halin da kike ciki ne Fargi? Kin san waye ni don haka wannan tambayar ina ganin ba ta da alfanu a gare ni. Shin wane ne mamallakin cikin jikinki?" Gabanta ne ya yi mummunar bugawa ta tattaro mayafin jarumta ta yafa wa kanta, sannan ta furta. "Ba ni da masaniyar abin da kake nufi shugaba." Fargi ta furta tana barin wurin fuska a ha e. Ka a kansa ya yi ya saki murmushin da shi ka ai ya san manufar yin sa. "Ta yaro kyau take ba ta arko, shi dai ciki an duma ne don haka sannu-sannu ba ta hana zuwa." Hankali a tashe Fargi ta nausa daji sai da ta yi tafiya mai nisa ta an hura huta sannan ta yi wani turare, tana kiran sunayen wa ansu gungun manyan aljanu wa anda suke taimaka mata a game da 'yan tsaface-tsafacenta. A cikin munanan hallitarsu suka bayyana a gabanta, "Wacce irin damuwa gare ki?" "Shubana Zurufu shi ne matsalata! A yanzu haka ina auke da juna biyu, kuma take-take da yanayinsa na nuna mini yana son banka o laluben sirrina." "Zan yi miki aiki a kansa amma kin san taurin kai irin na Zurufu, don haka za ki yi mana yanka. Ina nufin ki zubar mana da jinin jarirai sababbin haihuwa guda uku, za ki ba mu fararen ra uma biyu sauran aikin ki bar mana komai a hannunmu." an tsorace ta dube shi sannan ta ce. "Dole sai ta haka? Haba Aljani Huburu ka san babu asarar rayuka a tattare da ni, ban ta a kisa ba tun da na wayi gari a halwar tsafin da Shugaba ya horar da ni." Fargi ta furta cike da damuwa. "Dole sai an zartar da haka Fargi, idan kuma ba kya muradi sai mu yi miki fatan sauka lafiya." Ajiyar zuciya Fargi ta sauke sannan ta yi musu sallama. Ta koma gidan mahaifinta. "Fargi akwai abin da yake damunki na ga kwana biyu kin ashe, yanayinki ya sauya. Me yake damunki?" Mahaifiyarta ta wurga mata tambaya tana kafe ta da idanu. Shiru Fargi ta yi tamkar ba za ta yi magana ba sannan ta ce. "Kwana biyu ba na jin da i ne amma yau na ji warin jikina." Ta furta tana sunne kai asa. "Ba ni hannunki mu gani." Rass gaban Fargi ya fa i, ba ta da za i don haka ta mi a wa mahaifiyarta hannunta. Sai da ta duba tafin hanunta sannan ta saka hannu ta gwale wayar idonta. A imauce ta sake ta tana ja da baya cikin tashin hankali. Ganin haka ya sake firgita Fargi ita ma ta an ja da baya idanunta suka ciko da walla. Sai da Mahaifiyarta ta rufo ofa da windon cikin bukkarsu sannan ta sake jan hannun Fargi suka koma bakin gado suka zauna. "Wa kika bu ewa sirrinki har haka ta faru? Me ya sa za ki yi mana haka Fargi bayan kin san matsayin da kike da shi a garin nan? Shin kin za i ki tashi daga gurbinki na shugaba ki koma bautacciya bayan kin yi aure? cikin waye a jikinki Fargi?" Mahaifiyarta ta wurga mata tambayoyi yayin da Fargi ta sunkuyar da kai tana jin irjinta yana bugawa. Bayan kowa ya watse sai ya rage daga Sarki Abdul'aziz sai Kamalu, Muhsin, Ru ayya da Yarima Muhsin. Kallon-kallo aka shiga yi tsakanin Muhsin da Kamalu. Abubakar kuwa yana zaune sai bin su yake da kallo. "Allah mun gode maka da ka nuna mana wannan rana mai tattare da farinciki ha e da acin rai. Ubangiji ka fi mu sanin dalilin da ya sa ka tsara mana wannan al'amari a gare mu, kuma muna ro on ka ba mu ikon cinye jarrabawar da za ta ci gaba da samunmu mai kyau ko akasin haka." Suka amsa masa da Amin. "Kamalu wannan an uwanka ne sunansa Muhsin, ga ayar anwarka nan Ra ayy." "Na jima da sanin Yarima Muhsin ko don rashin mutumcinsa, wannan ce dai ban santa ba." Kamalu ya furta a zuciyarsa. Amma a fili sai ya furta. "Na ji da in kasancewata da ku gaba aya ranka shi da e, har yanzu gani nake tamkar mafarki nake." Murmushi Sarki Abdul'aziz ya yi ya ce. "Haka Allah ya tsara Kamalu babu bawan da ya isa ya kaucewa addararsa. Kana da yayye mata da ke aure a wasu garuruwan, In shaa Allah zan sa a aika musu da takarda har zuwa dangin mahaifiyarku." Murmushi Kamalu ya saki, ha e da amsawa Takawa. Sannu a hankali Sarki Abdul'aziz ya dinga jan su Muhsin da hira don ya gusar musu da damuwar da ke unshe cikin zuciyarsu. Jefi-jefi Muhsin yake saka baki daga arshe ya mi e ya yi musu sallama ya wuce akinsa. Kamalu da su Ru ayya suka kwana a sashen Sarki Abdul'aziz. Tamkar wasu dabbobi haka aka dinga jan Jakadiya da Fulani Umaima aka wuce da su akin duhu, kamar wasu kayan wanki hakan dogaran suka watsa su ciki sannan suka janyo afar suka datse. Jakadiya ban da kuka da kururuwa babu abin da take yi, ita kuma Fulani Umaima sai ido da take bin su da shi da jinjina darasin rayuwa da mamakin wai yau ita ce Dogarai suke yi wa tsawa. "Allah ya tsine miki Umaima duniya da lahira, wallahi tarraya ta da ke ba ta amfane ni da komai ba." Jakadiya ta yi maganar cikin acin rai. "Wai kina ina ne ba na son na farwa wacce ba halaliyata ba." Buguzu ya furta yana laluben Jakadiya. Tashin hankalinta ne ya ninku suka ci gaba da wasan uya shi da Jakadiya, Fulani Umaima na shirin mayar wa da Jakadiya martani ba ta yi aune ba ta ji wata irin azaba ta ratsa saman kafa arta sakamakon cizon da Aljani Guzzu ya kafa mata a kafa a. Jini ne ya fara tsartuwa, cikin azaba Fulani Umaima ta kwarara ihu tana neman taimako. Cikin shammata ta sake jin ya sake zuba mata ha ora a gadon bayanta kuma duk wurin da ya sa ha oransa da naman jikinta yake agowa. Kasancewar arfin mutum da aljan ba aya ba tuni Buguzu ya turmushe Jakadiya ya kafa ha oransa a saman mamanta aya, tamkar wacce ake zu ewa jini haka Jakadiya ta dinga jin ana zu arta. Duk yadda ta so ta yakice Buguzu sai abin ya gagara, don haka ta shiga kuka har da majina tana neman auki amma ko motsi ba ta ji ba ballantana ta saka ran wani zai shigo ya kawo mata auki. "Ba zan kashe ki ba, sai na gama ana miki mummunar azabar da za ta gigita ruhi da gagar jikinki." Aljani Guzzu ya furta wa Fulani Umaima sannan ya ware faratan hannuwansa masu matu ar kaifi ya shiga karta mata a jiki yana wasa su tamkar yadda ake wasa wu e. Fulani Umaima tun tana iya gudun ceton rai har ta galabaita ta fa i tana jan ciki arshe numfashinta ya auke ta sume a wurin. Tun isar su Inna wuro sashensu na Bayi kyakkyawan labari game da Kamalu ya fara ya uwa, take sashen nasu ya kacame da hayaniya aka shiga tattauna maganar kowa yana mamaki da ta'ajibin wannan lamarin. Sai a wannan lokacin kowa ya samu damar furta damuwar da ke cikinsa dangane da Fulani Umaima, Bayi da dama suka shiga banka o miyagun laifukanta da suka sani na zahiri. Suka shiga tattauna umbin ha urin da Fulani babba ta yi a lokacin da take raye, har zuwa halin da Abubakar yake ciki na ban tausayi. Wannan ya tsinka zuciyar Jawahir da Mai gado suka shiga aki suka sha kukansu, ga dai ranar yabon Fulani babba amma ba ya raye. Sai da suka daidaita nutsuwar suka shiga wurin Inna wuro aka ci gaba da tayata barka. Don ko ba a fa a musu ba sun san a yanzu su Inna wuro sun yi musu fintinkau don suna da tabbacin Takawa ba zai bar su haka ba, sai ya gwangaje su da tukwici mai girma. Tun a daren wasu suka fara yi mata fadanci da nuna soyayya abin har mamaki ya ba ta don ta san wacce suke kashewa su binne a cikin gidan dama Mai gado ce, Sai da dare ya tsala sosai sannan su Mai gado suka yi wa Inna wuro sallama suka koma nasu akin. Asubar fari Masarautar Huddam ta wayi gari da samun mabambamtan labarai, wasu daga ciki sun samu labarin tun a daren ranar yayin da wasu sai da gari ya waye suka samu labarin abin da ya faru. Kuma tun da asubar Sarki Abdul'aziz ya sa aka rubuta takardu zuwa wurin mahaifan Fulani babba, Fulani Umaima da su Khadija domin a sanar da su abin da yake faruwa. Sarki Abdul'aziz da kansa ya za owa Kamalu kayan 'ya'yan sarakai na alfarma, ya umarce shi da ya sauya na jikinsa don kayan Bayi ba su kamace shi a matsayinsa na an sarki ba. Ba musu Kamalu ya kar a ya saka a angare aya yana sake tausaya wa rayuwarsu ta Bayi, don har lokacin jinsa yake tamkar bawa domin