Sashe 47
Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bar mini komai a hannuna, daga yau daga rana mai kamar ta yau ita da 'ya'yanta ba za su sake aga baki a kan sarauta da mulki a cikin gidan nan ba." Mahaifiyar Umaima ta yi maganar cikin cin alwashi. "Fiye da haka na san za ki aikata ranki shi da e. Ba don kada na ko a ki har ki ga kamar zuga ce nake yi miki ba, da sai na ce a kaf fa in duniyar nan babu wanda ya kai ni sa'ar samun mahaifiya." Murmushi mahaifiyar tata ta saki. "A kan farincikinku zan iya aiwatar da komai domin komai ba komai ba ne a wurina." Basiru ya saki murmushin farincikin jin da in yabon da Boka Shaddas ya yi masa, fuskarsa ta sake fa aton hancinsa ya sake bajewa yayin da fakekiyar fuskarsa ta ara bajewa. "Ni mai biyayya ne a gare ka hatta rayuwar mahaifiyata idan ka na bu ata sai na auko maka ita." Basiru ya fa a cikin nuna bajinta. uri Boka Shaddas ya yi yana kallonsa ha e da nazartar halaye da abi'un yaron. Lokaci aya ya ji irjinsa ya buga don gani yake tamkar yaron ya fi shi bushewar zuciya da rashin imani, amma gudun kada Basiru ya fahimci wani abu ya sa ya sakar masa murmushi sannan ya ebi wani ruwa mai yau i ya zuba a kan littafin. Lokaci aya littafin ya fara fitar da wani farin haya i sannan ya kai hannu ya bu e shi, daidai wurin da Fulani Umaima ta tsaya da karatu ya bu o don haka ya saki shu'umin murmushi ya ago ya dubi Basiru. "Tabbas mun taki babbar sa'a domin Mahaifiyarka, ta ci arfin karatun littafin. Da ace mun yi bori da sanyin jiki da tuni wani zancan ake ba wannan ba, sakamakon gab take da kammalawa kuma tana kammalawa za ta kai matu ololuwar nasara. Daga haka ta mayarwa da Bamaguje littafinsa, ka ga kenan da mun tashi a tubar babu kuma babu wata amfana da za mu yi." Basiru ya yi wa Boka Shaddas jinjina da hannu. "Ba za ta ta a yin nasara a kanmu ba." Boka Shaddas ya jinjina kai sannan ya an fara duba shafin da ya ci karo da shi. "Duk da kasancewar zuri'ar mahaifinki sun fito ne daga zuri'ar Bargi su ne suke mulkar yankin nan baki aya, wato kakanninki sune da sarautar masarautar nan. Kuma hakan ba ya hana su yin rayuwarsu ta bakin teku da koguna ba ne, dalilin da ya har suka samu kyakkaywar ala a tsakaninsu da jinsin Aljanun cikin ashin ruwa wa anda ake kira da Jinnul-Gawwas. Har ta kai sun bu e musu su kan gansu suna iyo a cikin ruwa kamar yadda mutane ke shiga su yo su in kifi, a irin wannan lokacin ne idan tsautsayi ya gifta da ajali sai ka ga sun janye mutum can cikin ashin ruwa sai sun gama zu e jininsa sun wale wasu hallitu na jikinsa sai su turo shi sama, wannan lamari sai ya fara damun mahaifin Kakanki har ya samu Sarkin Aljanunsu na ruwa suka yi doguwar tattaunawa suka tsayar da matsaya, a kan sun daina cin kowannen bil'adam na wannan yankin sai shekara-shekara, za su ci mutum uku sa anin a baya da suke cin babu adadi. Ganin hakan ne ya kawo masala shi ya sa mahaifin kakanki ya amince, kuma da yake Sarkin jinnul-gawwas Dattijon warai ne sai ya tsawatar wa da sauran wa anda suke asansa ba tare da wani ya karya al awarin da aka zartar ba." Sai da na sauke ajiyar zuciya ina mamakin wannan mur an labarin da Sarki Hafiz yake ba ni sannan na furta masa. "Amma wannan labarin da kake ba ni kana ganin zai auki shekara nawa? Kuma ya aka arke tsakanin mahaifiyata da an gidan Aljani Darri? Ya aka yi mahaifina ya yi galaba a kan mahaifiyata har ya tarwatsa soyayyar da ke tsakaninsu wacce ka ce tuni mahaifiyata ta dam a wa an autan aljani wu a da nama na soyayyarta?" Murmushi Sarki Hafiz ya sakar mini, yayin da Fuskar Fulani Hawwa kulu take a tamke kamar magaribar inya. "Me kike ci na baka na zuba ne Hidaya? Ai duk gaggawar kwarto ya jira mai gida ya gusa kuma duk gaggawar ungozoma ta bari a haife." Murmushi na sakar masa sannan na ji ya ci gaba da cewa. "An sha gwagwarmaya matu a tare da ba in artabu kafin auren mahaifiyarki da mahaifinki, kuma tun lokacin da aka aura auren iyayenki ofofin bala'i da na masifa suka fara bu ewa a cikin masarautar nan. Sannan kuma babu takamaiman adadin shekarun da zan iya sanar da ke domin ni kaina Kakana bai sanar da ni ba, abu aya na sani shi kansa Kakana yau kimanin shekararsa ashirin da biyar kenan da mutuwa, kuma labarin auren mahaifiyarki zai iya kai wa tsawon shekaru talatin kenan tun da a bayanta an yi sarakunan da suka shu A hargitse na dube shi cike da matsanancin mamaki har sai da ya gane mamakina arara a fili, "Me kake shirin sanar da ni Sarki Hafiz? Da bakinka ce iyayena babu wanda ya fito daga cikin jinsin jinnu, amma kuma ya aka yi na kasance mai arancin shekarun da ko sha biyar ban kai ba. Shin ya aka yi haka ta faru? Yanzu haka ina mahaifana? Me ya sa ba sa cikin masarautar nan?" Boka Shaddas ya rufe littafin ha e da kallon ofar kogon tsafinsa, sakamakon jin maganar wata ba uwarsa da ta kawo masa ziyara. Bai amsa mata ba sai da ya arasa har wurin da kayan tsafinsa suke sannan ya jefa littafin cikin wata ar tukunyar asa nan take littafin da tukunyar suka ace Lokacin da Fulani Umaima ta arasa ofar akin Takawa babu abin da yake tashi sai kukan tsintsaye da ananan dabbobi, cikin san a ta an banka a labulen akin sannan ta hura maganin hannunta. Komawa ta yi ta tsaya tana kallon abin da zai faru don ba taa yi tsammanin abin da Basiru ya fa a zai tabbata ba, a hankali ta ga Sarki Abdul'aziz da Mai martaba sun fara hamma babu jimawa kowannensu ya ungire bacci ya yi awon gaba da su. Wani uban tsalle Fulani Umaima ta buga cikin farinciki ta fa akin, sai da ta rufe akin ruf sannan ta arasa wurin da gawar Fulani babba take kwance sannan ta fara kunce aurin da ke wurin afafuwanta. Kafin wani lokaci tuni ta ware likkafanin cikin farinciki ta ciro wannan aurarriyar fatar wurin Bamaguje ta tura mata a cikin asanta, nan take gawar ta fara wani irin karkarwa sannu a hankali wani ba in haya i ya fara fita daga jikinta yana bi ta ofar yana fita kai tsaye haya in ya wuce sashen Sailuba. Kamar yadda Bamaguje ya gaya mata sai da haya in ya gama fita sannan Fulani Umaima ta mayar da likkafanin ta aure ba tare da ta cire wannan aurarriyar fatar ba. Ta karka e jikinta sannan ta fice daga akin, tana jin ta tamkar ta riga da ta gama da matsalolin gabanta na duniya gaba aya. Tun daga tsakar gidanta ta fara cin karo da kayan akinta a warwatse tamkar zaratan jarumai goma ne suka yi dambe a wurin, irjinta ne ya yi wata irin bugawa nan take jikinta ya auki karkarwa tamkar mazari. Kamar kazar da aka tsamo daga ruwa haka Fulani Umaima ta shiga akin jiki a sa ule tana fatan kada Allah ya sa zarginta ya tabbata da take yi a kan Basiru, cak ta tsaya wuri aya tana jin wani irin abu yana mamaye tsarga mata tun daga tafin afarta har zuwa tsakiyar kanta sakamakon hango akwatin arfenta da ta yi a yashe a asa, komai ya tarwatsa da alama babu komai a cikinta. Kamar wace take jin tsoron ta awa haka ta arasa a arare, ta zauna da ar irin zaman 'yan bori a asa hawayen da ta rasa na mene ne ya fara bin kuncinta. "Allah wadaran hali irin naka Basiru! Ban san ya zan yi da kai ba wannan wanne irin yaro ne mai taurin kan tsiya." "Ummi me yake faruwa?" Muhsin ya furta daga bakin ofa. Jin tambayar Muhsin ya sa ta fashe da kuka tana jin zuciyarta na zafi. Mamaki ne ya kama Muhsin ya bi akin da kallo sannan ya arasa gaban mahaifiyarsa, a sanin halin mahaifiyarsa ya san rasuwar Fulani Babba ba zai aga hankalinta har ta aikata wa akinta haka ba. "Muhsin aninka ya zame mini ala ai dubi yadda ya yi mini da aki, ni ya raina ni ba zan ta a yin magana ya saurare ni ba." Ajiya zuciya Muhsin ya sauke sannan ya furta, "Ummi sai dai fa ki yi ha uri, amma daga ni har 'yar uwata babu mai hali ko abi'a irin na shi. Kin san kowanne yaro da yadda Allah ya halicce shi wata ila nan gaba zai daina." "Sai yaushe Muhsin? Yaushe kake tunanin Muhsin zai kintsu, rannan fa kamar ya aga hannu ya dake ni." Jin haka ya sa Muhsin ya an ta e baki. "Ina Ru ayya?" Ya wurga mata tambaya. "Na ha a ta da baiwa Inna wuro." Fulani Umaima ta yi maganar tana ru o hannun Muhsin. "Muhsin ina jin tsoron ganin girman aninka domin a yanzu ko shekara sha hu u ba bai yi ba, amma ya gagare ni..." Ihun da Muhsin ya yi ne ya katse ta, ya matsa baya yana yarfe hannu cikin azaba. "Me ya faru Muhsin? Lafiyarka kuwa?" Wani irin kallo yake bin mahaifiyarsa da shi, jiki a sanyaye ya jingina da bango nan take ta ga idanunsa sun ciko da wallah. A tsarace ta kalle shi don ta san abin da zai sa Muhsin wallah ba aramin abu ba ne. "Ummi!" Ya ambata da wani irin yanayi, Fulani Umaima na shirin amsawa ya ci gaba da cewa. "Ta shammaci zuciyata a lokacin da zuciyar tawa ta sakankance a nisan kiwon da za ta yo kalacin abin da za ta ciyar da kanta, ta mamaye gangar jiki da ruhina a lokacin da ban yi zato ba. Kwatsam soyayyarta ta mamaye ni har ta kai komai da kowa na gudurata idan ba tunaninta ba, babu zato