Sashe 38
Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
koma kamar kowa." Ta furta a hankali sannan ta wuce akinta. Tana kwanciya babu jimawa bacci ya yi awon gaba da ita, cikin bacci ta ri a jin wani abu na yun urin fita daga cikin asanta tamkar a yana son fitowa daga asanta. Da sauri ta bu e idanunta a hankali ta furta. "Yau me nake ji haka a cikin daren nan?." Ta so ace safiya ko rana ce da ta yi turare miyagu ko ta an ji da in jikinta. Kwanciya ta sake yi sai dai a wannan karon bacci ya aurace mata, sakamakon yadda take jin duk wata ga a ta jikinta kamar ana fusgarta da arfi. A angare aya kuma wani irin zafi ne yake ratsa lungu da sa on cikinta, babu jimawa kuma ta ji wata irin iska mai da i na shiga jikinta wanda hakan ne ya yi sanadiyyar da bacci ya yi awon gaba da ita. Tun asubar fari Fulani Umaima ta so yi wa Sarki Abdul'aziz sallama don ta koma sashenta ta baza kunnuwa ta ji rahoton da zai fito daga angaren Fulani babba da Sailuba, amma gudun kada ya fahimci wani abu ya sa ta ha ura har sai da gari ya waye tangararan. Tana shiga akinta ta samu Basiru ya hargitsa mata aki yana bincike, da mamaki take bin shi da kallo don tun daga rumfa (Falo) har zuwa uwar aki a birkice yake. "Me kake nema da ka hargitsa mini aki?" Kafe ta ya yi da jajayen idanunsa fuska a tur une, kallon wayar idonsa ya hadda sa mata mummunar fa uwar gaba. Kammaninsa da na Boka Shaddas suka sake bayyana arara, har sai da ta ji wani kwarjini da shakkunsa ya mamaye ta. "Tambayarka nake me ka ajiye mini da kake birkita mini aki za ka auka?" Fulani Umaima ta sake tambayarsa cikin dakiya. "Wani littafi nake nema?" Ras! Gabanta ya fa "Kai ka ajiye shi?" "Ni da akin mahaifiyata sai na ajiye abu zan auka?" Da mamaki take bin sa da kallo, ba tun yau ba ta lura da tsagerancinsa. Duk da shi kansa Muhsin ba kanwar lasa ba ne wurin rashin kunya amma na Basiru ya dame shi ya shanye, dalilin haka ya sa ko ka an ba su cika ga maciji da Takawa ba. Saboda har Takawa Muhammad bai bari ba idan ya so tata masa rashin mutumci. Idan Fulani Umaima ta fara wassafa miyagun abi'unsa a zuciyarta har mamakin antar shekarunsa take yi da hatsabibancinsa. "Fice mini daga aki!" Ta furta fuska a ha "Duk ma inda kika oye shi sai na lalubo shi, saboda dole ne na cika umarnin mai gida. Don haka idan kere na yawo zabo na yawo dole watarana za a ha u. Ki rubuta ki ajiye ko da arzi i ko da tsiya sai na mallaka masa littafin nan." Yana gama maganar ya gegare ta ya wuce har yana bangazarta ya fice daga akin. "Duk rintsi kada ki sake wani ya wace littafin nan daga wurinki Umaima." "Ke ba kamar sauran kowa ba ce a wurina don haka na dam a miki wannan sihirtaccan littafin ki kula da shi." "Ina fatan dai kin yi wa littafin nan kyakkyawar ma oya?" "Ina sake jan hankalinki kada ki saki jiki da kowa a kan wannan littafin duk kusancinki da mutum koda an cikinki ne!" Ire-iren kalaman da Bamaguje yake furta mata kenan a lokutan baya idan ta ziyarce shi, ajiyar zuciya ta sauke ta shiga kiciniyar gyaran uwar akinta don ba ta barin kowacce Baiwa ta shigar mata aki saboda kayan tsubbace-tsubaccan da ta rataye. Sai da Jawahir ta aga rigarta ta ora hannunta saman tambarin cikinta ta yi kasa e kamar wacce take sauraron wani abu sannan ta furta, "Tsohuwar guba ce da ta bi ilahirin jiki da ruhinsa, ban san tsahon lokacin da ta auka a jikinsa ba amma ta riga da ta illatar da ruhi da gangar jikinsa." Jawahir ta ago ta kalli Mai gado. "Na san fa a za ki yi mini Inna amma da na sanar wa Fulani Babba don a nema masa magani." Shiru Mai gado ta yi tana nazari. "Idan kina dakatar da ita za ta daina sanar da ke halin da take ciki." Tsagin zuciyar Mai gado ta garga e ta. Sai da ta sake janyo Jawahir jiki sannan ta furta. "Jawahir duk cikin gidan nan babu wacce nake so nake auna har a raina kamar Fulani babba, to amma ki dubi matsayinmu a cikin gidan nan. Mu antattu ne da ba su da 'yan kansu ballantana galihu, ban da Allah Ya sa Fulani babba ta ja mu a jiki da bautar da za mu dinga yi irin ta su Laure ce. Furta irin wa annan maganganun matu ar suka fito sarari ba zai haifar mana da a mai ido ba, Idan kin yi mafarki ko wani tunanin ya zo miki ki same ni a aki ki ri a gaya mini idan ya so sai mu tattauna ni da mahaifinki." Ganin Mai gado ta bata warin gwiwa ya sa ta ji da i har ta fa a fara'arta a fili, fita ta yi don ta auro alwala Mai gado ta bi bayanta da kallo cikin jimami da matsananciyar damuwa. Sai da ta tabbatar su Jawahir sun tafi sussu ar gero sannan ta kira Umaru don su tattauna matsalar da Jawahir take son allo musu. "Malam ba ya ta haihu fa?" "Kamar yaya?" Ya tambaye ta fuska auke da damuwa. "Da alama zancan mahafiyar yarinyar nan na ci gaba da bayyana, idan ba ka manta ba da kanta ta ce mana 'yarta ce za ta bayyana surar jinsi da ta hallitar zuri'arsu baki aya." Duk abin da Jawahir ta fa a wa Mai gado tas ta kwashe ta gaya masa, shiru ya yi sannan ya furta. "Ki ci gaba da jan ta a jiki kada ki bari ta furta wata maganar da za ta kai ga jawo mana matsala, zan shirya fitar sirri akwai wani Mai magani da na ji Mai martaba ya sa an kar o wa Fulani magani a wurinsa." Sai da Mai gado ta ji haka sannan ta an saki ranta ta ci gaba da harkokinta. Sai da asuba ta yi sannan Fulani babba ta iya bu e idonta, ta yun ura da niyyar tashi lokaci aya ta ji jikinta tamkar an aure ta. Motsa afarta take son yi amma sai ta ji ilahirin jikinta ya yi mata nauyi dum! Kamar an danne ta da narkeken dutse, wani abu da ya sake aga hankalinta yadda take jin jikinta tamkar ba nata ba. Tana daga kwance ta fara walla wa Mai gado kira ita da Baiwa Zainaba amma shiru babu wanda ya amsa mata. Tana nan kwance hawaye ya fara gangaro mata don duk yadda ta so iya motsa jikinta abin ya gagara, sai da gari ya waye tangararan ta fara jiyo gwarancin Abubakar don ta tabbata yunwa yake ji. Babu jimawa ta ji sallamar Baiwa Zainaba, da sauri ta fara jera mata kira. Jin kiran ba na lafiya ba ne ya sa Baiwa Zainab ta fa akin da sauri. "Allah ya taimake ki ranki shi da Take zuciyar Fulani Babba ta karye murya na rawa ta furta, "Shigo Zainab." A hankali Baiwa Zainab ta shiga akin. "Zainab wata addarar ta sake rikito wa rayuwata, tun asuba idona biyu amma na gagara motsa koda an yatsana ne. Maza je ki kira mini Mai gado ki ce ta zo cikin gaggawa." SHU'UMAR MASARAUTA *Littafin ku i ne 500 idan kina bu ata za ki biya ta wannan Account in Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.* Tun da ya yi wa Baffajo tambayar irjinsa yake bugawa fat fat fat zuciyarsa tamkar za ta hudo irjinsa, fargabarsa aya kada ya ji mummunan labari a kan tushen asali da samuwarsa. "Kamalu da wa annan hannuwan nawa na tsinto ka a cikin kogon wata atuwar bishiyar kukar da ke cikin asurgumin wani dajin da ke cikin Rigar Ar o wanda ake kira da Dajin Wushushe da ke gefen oramar inya, a ranar da ake gudanar da babban bikin sha i tun safe na tashi da kasalar jiki ban san dalili ba don har na fasa fita kiwon Shanu sai kawai wata zuciyar ta shawarce ni da na bi bayan su Salele. Cikin udurar Ubangiji bayan na tafi sai wani irin zazza i ya rufe ni, don haka na nemi gefen bishiya na an kishinhi a don jikina babu wari. Kamar almara ina zaune sai na fara jin kukan jariri daga gefena, nan take na ciro guruna da layun da ke uguna don a tunanina ko mutanen nan dajin ne suke niyyar bu e mini idanu da tsakar rana, har na fara haramar yin turare sai idanuwan suka kai kanka kana kwance cikin kogon bishiyar kukar da kallonta ka ai sai da ya hargitsa mini kwanta. Wata irin juwa na ji tana yun urin aukata, idanuwana suka fara yi mini gizo har nake ganin bishiyar tamkar tana tafiya a bisa kanta. Kamar na wuce sai kuma nake jin zuciyata ta yi rauni ba zan iya barinka ba. Idan idanuwana ba gizo suke yi mini ba a lokacin da na fara tunkarar murgujejiyar bishiyar kukar, har gani na yi tamar tana matsawa baya da kanta. A haka na ci gaba da tafiya zuciyata na rawa har na ora hannuna a kanka na auko, sai dai abin da ya matu ar ba ni mamaki bai wuce ganin wani zagayayyan jini a saman kanka ba tamkar wanda aka ora hular sarauta. Wani abu da ya sake tsinka mini rai ganin na kai hannuna kanka don na goge jinin kai amma kuma sai na ga tamkar dan are yake a fatar jikinka, a haka na rungume ka har zuwa gida na kawo wa Innarka kai sai dai muna zuwa gida wannan jinin babu shi babu alamarsa. Ina tunanin hankalina ya kwanta sai kuma muka lura da wani ba on al'amari a tattare da kai wanda ba mu ta a ganin halittar an adam da irinsa ba." Lokacin da Mahaifiyar Fulani Umaima ta samu Umaima da bu atar Fulani Asabe ta zo da ita, tamkar dama tana son abin a ranta don