Sashe 8
Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
wa kanki hankali, kina nufin mu za mu ci gaba da surfen kina can kina kalle-kalle banza da wofi? Wallahi kika bari muka surfe na cikin turmin nan sai dai ki surfe wannan kwano ukun ke ka ai." Kalaman Safare suka katse ni, da sauri na waiga wurinsu kowaccensu ta sakar mini harara kamar idanunsu zai fa o. A zuciyata na furta. "Ko dai su Safare ba sa ganin wannan saurayin?" Daga bayana na ji ya sake ta o ni. "Ba za su ta a ganina ba, saboda wasu muhimman abubuwa. Ke ma akwai dalilin da ya sa kike rayuwa a cikin Masarautar nan har kike mu'amala da su. Ki ci gaba da ha uri kin san idan aski ya zo gaban goshi ya fi zafi." Yana gama furta mini wa annan kalaman na neme shi na rasa. Wata irin azaba ta riyarci afata sakamakon wurgo mini ta arya da su Safare suka yi, na sunkuya cike da azaba ina matsa afata. "Ga shi nan ki yi ki surfa ragowar, kuma kin fi kowa sanin halin Uwar tuwo matu ar aka gama surfen aka bar ki a baya za ki yaba wa aya za inta." Idanuwana na kai kan waryar da ke cike da gero har kusan kwano uku, tausayin irin wuyar sirfen da zan sha ya mamaye ni. Dole anwar na i, na sunkuya na auko ta arya kafin na ago na ji saukar bulala a tsakiyar bayana, azaba ta sa na wurgar da ta aryar ina ihu ha e da soshe-soshe. Ragowar mutanen da ke wurin babu wanda ya motsa ballentana na saka ran wani daga cikinsu zai kawo mini auki, sai da Uwar tuwo ta gaji da dukana don kanta sannan ta nuna ni da murtukekiyar dorina. "Ki yi gaggawar arasa surfen gabanki idan ba haka ba wallahi sai na sa Balele ya kai ki akin duhu, shegiyar yarinya da idanu kamar na wamai." Tun ba ta arasa zagina ba na suri ta aryar da a tsaye ta kusan tsayina, jiki na karkarwa na fara daka cike da tashin hankali. Ganin haka ya sa Uwar tuwo ta yi gaba tana buga wa sauran Bayin da ke tsaitsaye tsawa, da tafiyarta babu jimawa wa ansu zaratan samari biyu suka kewaye ni. "Shugaba wannan ba aikinki ba ne." Mamaki ya lullu e ni domin ko a mafarki ban ta a cin karo da su ba, haka kuma suturun jikinsu bai yi kama da kayanmu na bayi ba. Na sake mamakin kalamansu da suke kirana da shugaba. Tsaye na yi ina bin bayan Uwar tuwo da kallo samakon har lokacin ina hango ta sai da ta an yi nisa da ni, takaicin dukan da ta yi mini ya mamaye ni na fara ayyana da ina da hali sai na kar i doriyar hannunta na zane ta ita ma ta ji irin abin da muke ji. Ihun da na ji Uwar tuwo na yi ne ya dawo da ni hayyacina, na kai wayar idona wurin cikin mamaki nake bin ta da kallo. Kamar yadda na ayyana haka Uwar tuwo ke tsalle tana ihu, hatta ni da nake nesa da ita haka na ri a jiyo sautin saukar dukan da ake yi mata.Ta jima cikin wannan halin sannan ta fa a gefe aya tana sauke ajiyar zuciya, kamar wacce aka ce na waiga ina juyawa wurin turmin na yi tozali da abin da ya daskarar da ni. Gaba aya geron da ke wurin an surfe shi an dake mini tas, tsoro ya mamaye ni da ganin wannan lamarin. Duk da ba sabon abu bane a wurina na ji kalamai daga cikin zuciya, amma a wannan karon na razana, "Kada ki tsoro ta Shugaba domin firgici ba hali ko abi'ar ahalinku ba ne." Jin haka ya ara mini warin gwiwa na auki atuwar waryar na ora ta a kaina da yar, kafin na arasa wurin da Uwar tuwo ke kwance tuni Bayi suka taimaka mata aka kai ta can angarenmu na Bayi. Kallo aya za ka yi wa Bayin da ke wurin ka fahimci kowa ya sha jinin jikinsa, don babu hayani tsit wurin ya yi kamar an yi mutuwa. Kamar kullin idan kowannenmu ya dawo daga sashen da yake yi wa hidima, mukan taru a sashenmu na Bayi. Zaune muke gaba aya a tsakar gida, wasu daga cikinmu na zaune kusa da yayyansu suna wasa. Wa anda suke da arta shekaru kamar nawa da ba su wuce sha uku ba suna kwance a jikin iyayensu, idanuwana suka ciko da walla sakamakon ganin ni ka ai ce wari aya ba ni da makusanci. Ko da ba ni da iyaye ya kamata wasu su tausaya mini su aunace ni kamar yadda na ga wasu Bayin da aka samo marasa iyaye ake kula da su, me ya sa na kasance mai ba in jini kowa ba ya aunata?" Ba zato daga gefen kunnuwana na ji an furta mini. "Ke kike da kowa Hidaya! Kada ki karaya domin lokacin na nan da za ki tabbatar da haka." Abin ka da mai shirin kuka an jefe shi da kashi awaki nan take hawaye ya fara kai-kawo a wayar idona. Jiki a sanyaye na mi a zuwa gaban Jakadiya na tsugunna, da mamaki gaba aya suka juyo suna kallona. Ban damu da irin alubalen da zan fuskanta ba, babban burina bai wuce ni ma na san wace ce ba. "Lafiya kika zo kika saka ni a gaba kamar tsohuwar mayya?" Gabana na dakan lugude na tattaro kalaman bakina da na guntso na fesa mata. "Don Allah Jakadiya su waye iyayena?" Kamar ha in baki haka na ji sun tuntsire da dariya, sai da suka yi mai isar su sannan Jakadiya ta nuna wurin da Uwar Bayi ke zaune. "Akwai tarin bayanai dangane da samuwarki, ki tafi wurin Uwar Bayi za ta warware miki zare da abawa." Cike da warin gwiwa na mi e cikin sassarfa na isa gaban Uwar Bayi, na baje tagwayen kunnuwana ina sauraron makoma da tushena. Ajiyar zuciya Fulani Umaima ta sauke ta kai hannu ta rufe shafin littafin ba don ta gaji da karatun wannan hargitsattsan labarin mai cike da rikitar da kwanyar mai karatu ba. Mayar da littafin ta yi cikin akwatinta sannan ta auko turaren da take amfani da shi a duk lokacin da za su yi wata mu'amala da Mai martaba. A cikinta ta soke shi sannan ta rufe akinta ta fice kai tsaye ta wuce sashen sarki Abdul'aziz, haka kawai ta ji gabanta na fa uwa ba tare da ta san dalili. Babban tashin hankalinta bai wuce kada la anin jikin Takawa ya wargaza mata shiryayyan shirin ta a kan Maimuna ba. _Ummou Aslam Bint Adam_ 07062062624. *SHU'UMAR MASARAUTA*