← Book details Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 89

Sashe 48

Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

soyayyarta ta kewaye duniyata, ta ruhin da nake ta ama da shi. Ruhin da a kullin yawon zabarin nemanta yake ko zai yi tozali da ita domin ya samu sau in zugi da ra in da ke tare da shi, sai da kash! Da alama ban yi dacen ajiye warya a gurbinta ba, ban santa ba ban san asalinta ba. Ni dai abu aya kawai na sani ina sonta, ina aunarta! Ina jin ta a cikin jiki, zuciya da hantata. Ba na jin zan ci gaba da rayuwa matu ar babu ita, a duk bugun numfashina yana fita ne tare da kewa, bege da wadayin tozali da ita." Fulani Umaima sakin baki da hanci ta yi cike da mamaki tana kallonsa, lokaci aya kuma tsoro ya kamata don tana gudun kada wata ta asirce mata a don ko akuyarta ba za ta bari a asirce ballantana Yarima guda mai jiran gado. "Wace ce ita?" Fulani Umaima ta tambaye shi a ta aice. Idanu cike da wallah ya furta, "Ban santa ba! Ban san wace ce ita ba a cikin gidan nan! Ganin da na yi mata na biyu shi ne wannan abin da ya faru da ni." Muhsin ya arasa maganar yana nuna wa mahaifiyarsa hannunsa, ganin yadda hanunsa ya kwaile ya one da wuta ya sa ta mi e zumbur. "Waye ya yi maka haka?" "Ina tsammanin ba mutum ba ce!" Muhsin ya furta a sanyaye. "A ina take?" Fulani Umaima ta sake wurga masa tambaya, nan take Muhsin ya zayyanewa mahaifiyarsa duk abin da ya ta a faruwa tsakaninsa da Jawahir, shiru ta yi tana nazari sannan ta sake kai idanunta kan hannuwan Muhsin. "Tashi ka je duk abin da yake faruwa zan kamo bakin zaren, mu bar wa zuwa wayewar gari ka san Mahaifinka a yanzu yana cikin halin jimamin rashin matarsa. Amma mu yi ha uri zuwa an wani lokaci. Muhsin ya mi e jiki babu wari har ya zai fita ya hangi wani aramin on kan mage, da mamaki ya tsugunna ya auke yana juyawa. "Me ya kawo wannan abin cikin akin nan?" Rass! Gaban Fulani Umaima ya fa i. "Za ta iya yuwa an'uwanka ne ya shigo da shi, ba ni nan idan ya dawo zai mini bayanin dalilin da ya sa ya kawo mini shi aki." Fulani Umaima ta yi maganar tana kar on kan magen da ke hannunsa wanda Bamaguje ya ta a ba ta da jima ta sa alewa a kusurwar akinta. Tun da Muhsin ya fita Fulani Umaima ta saka zaune ta kasa tsaye, damuwa goma da ashirin ta cunkushe zuciyarta. Ta rasa wacce za ta fara magancewa, matsalar Basiru da ke neman gagare mata ko ta littafin da ya auke mata? Ko kuma ta wurin Yarima Muhsin da ta lura ana neman zautar da shi ta ashin asa. "Galadima ko Ciroma." Ta furta a fili. "Na tabbata cikinsu akwai mai niyyar salwantar mini da rayuwar Yarima, kuma har abada ba za su yi galaba a kaina ba matu ar ina da Bamaguje a fa in duniyar nan." Fulani Umaima ta arasa maganar cikin cin alwashi. Lokacin da Kamalu ya ji tambayar Galadima ya an so ya duburburce, Dattijo Maharaz ya dafa kafa arsa ya furta. "Ka ce masa ita karaga tana ga mamallakinta ne ba wanda yake son mallakarta arfi da yaji ba, jinin Marigayi Sarki Muhammad Safwan har abada ba ya bu atar tilastawa. Mai karaga yana ga abarsa duk rintsi duk wuya, kuma ko ba-da e ko ba-jima mai ita zai maye gurbinsa." Kamar yadda Kamalu ya ji haka ya sanarwa da Galadima. Take ya lura da yanayin firgici da tashin hankalin da ya shiga, lokaci aya Galadima ya ji afafuwansa na namenan gagarar aukar nauyin gangar jikinsa. Ganin haka ya sa Dattijo Maharaz ya ja hannun Kamalau suka fice daga cikin soron. "Wane ne shi? Ya aka yi ya san wannan furucin tsohon furucin, an waye shi da zai fa i wannan maganar mai tasiri ga wanda zai iya ba untar karagar Masarauta?" Da sauri Galadima ya bi bayansu amma sama da asa ya nemi Kamalu ya rasa. Dattijo Maharaz da Kamalu suna fita suka ci karo da Baffajo da yake ta bulayin neman Kamalu, da sauri ya dam i hannunsa suka auki siiririyar hanyar da a ta sada su da sashen bayi. A wannan lokacin Dattijo Maharaz ya so sanar da Kamalu tushen labarinsa da asalinsa, amma sanin firgicin da ke tare da Baffajo dangane da maganar da Kamalu ya ji daga gare su ya sa ya ale shi sai bayan wani lokaci, amma ya ci alwashin a ha uwarsa ta gaba zai fe e masa biri har wutsiya. Idan ya so duk wacce za a yi sai a yi tsakaninsa da zuri'a da suka yi kane-kane a cikin rayuwar Kamalu. *SHU'UMAR MASARAUTA* *25* *Littafin ku i ne 500 idan kina bu ata za ki biya ta wannan Account in Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.* Kiran sallar asubar farko ne ya farkar da Sarki Abdu'aziz daga nannauyan baccin da ya yi awon gaba da su, haka kawai ya ji jikinsa ya yi masa nauyi da tsami kamar wanda aka yi wa duka. A angare aya yana mamakin yadda bacci ya yi awon gaba da su duk da irin mummunan halin da suke ciki, a hankalin ya mi e ya fita ya auro alwala yana shigowa ya ga Mai martaba mahaifin Fulani babba ya tashi. Da kanshi ya zuba masa ruwa a buta ya ajiye masa, sannan ya koma gefe ya zauna ya zuba wa gawar Fulani babba idanu da ke kwance babu motsi. "Sarkina watarana fa daga mu biyun nan za mu koma mu uku, daga haka fa sai a gan mu har da jikoki ko?" "Ina matu aunarka Sadaukina, shi ya sa nake addu'ar Allah ya sa na riga ka mutuwa don ba zan iya jure rashinka ba." "Don Allah a duk lokacin da kake gaban gawata ina son ka shaida Wa Ubangiji ni mai biyayyar aure ce kamar yadda kake fa a, ko ro a mini yafiyar laifukana ka kuma nema mini salama a cikin makwancina." Lokaci aya kalaman Fulani Babba na tsahon shekarun baya suka dawo masa, a lokacin ba su fi shekara biyu da aure ba don ko Fulani Umaima bai aura ba. "Ke 'yar aljanna ce Fatima! Ke mai biyayyar aure ce Fatima. Allah ya gafarta miki Ubangiji ya ni'imta makwancin da za mu kai ki, amma me ya sa za ki tafi ki bar ni? Me ya sa mutuwarki ta shammace ni..." Kuka ya ci arfin Sarki Abdul'aziz dalilin haka ya gagara arasa kalaman bakinsa, har yanzu gani yake mutuwarta tamkar mafarki ce da yake fatan farkawarsa a kowanne lokaci. Sai a yanzu ne yake tuna irin zaman 'yan marinar da suka dinga yi tsakaninsa da ita yana mamakin musababbin faruwar haka. Wani irin aci ya mamaye zuciyarsa tare da nadama, da-na-sani da kaicon cusgunawar da ya yi mata, babban takaicinsa bai wuce yadda nadamar ta zo masa a lokacin da ba za ta yi masa amfani ba. "Taso mu je masallaci sun shiga Sallah, sai ha uri Abdul'aziz kuka ba zai dawo mana da Fatima ba." Mahaifin Fulani babba ya yi maganar yana janyo hannun Sarki Abdul'aziz, masallaci suka wuce kowannensu zuciya babu da "Lafiya kika aika kirana da wannan farar asubar Sailuba? Wallahi ba aramin fa ar mini da gaba kika yi ba, mene ne yake faruwa?" Jakadiya ta yi maganar asa- asa. Kalaman Jakadiya a madadin su sanyaya zuciyarta sai kawai ta fashe da matsanancin kuka, da sauri Jakadiya ta matsa wurin Sailuba tana zama a gefenta wani irin wari ya mamaye hancinta. Da sauri ta ja baya tana an toshe hanci gabanta na tsananin bugawa. "Wani me ye wannan yake wari Sailuba?" Da mamaki Sailuba ke kallon jikinta don ita babu wani da take ji, sai da ta share hawayenta sannan ta furta. "Inna tun daren jiya nake tsula fitsarin kwance ga wani ruwa mai oyi na fita daga asana, ina zuwa ban aki na yi wanka na ga kwarkwata na fa owa daga kaina na shiga uku Inna ina tsoron kada irin ciwon Fulani ya same ni." "Jakadiya ni warkice daidai da ugun kowacce shegiya, ki rubuta ki ajiye Umaima ba kanwar lasa ba ce kuma ko an ci birnin kura ba a ta a ba wa ingarman kare dillanci. Wallahi ni Umaima sai na muzanta rayuwarku na maisheku antattun marasa amfani." Take kalaman Fulani Umaima na baya suka dawo cikin kunnuwan Jakadiya, wani irin matsanancin tsoro ya dirar mata. "Fitsari fa Sailuba? Kina nufin fitsarin kwance?" Sailuba ta gya a kai tana share hawaye. "To ai ni yanzu ma wani irin warin ja a na ji kina yi, na san wannan ba zai wuce sharrin Umaima ba. Wato dai abin da nake zargi ya tabbata, ta gama da Fulani babba yanzu za ta dawo kanki." Sailuba ta zaro idanu a firgice. "Na rantse da girman Allah, kwarankwatsa dubu da oriya ko zan yi yawo tsirara sai na nuna wa Fulani Umaima ta tsokano tsuliyar autan dodo. Sai na nusar da ita duk girman bishiyar kuka bagaruwa ce babba, ni Jakadiya na yi artabu da wa anda suka ninke Umaima a fanin hatsabibanci da tsafi na yi galaba. Wallahi-wallahi sai na shammace ta; ta angaren da ba ta ta a tsammani ba. Sai na cusa mata ba incikin da har abada ba za manta da shafina ba, kuma sai na ana mata azabar da ruwa ko teku bai isa ya sanyaya mata u ubar da take ciki ba. Ki kwantar da hankalinki Sailuba matu ar ina numfashi, sai Umaima ta dur usa da gwiwoyi biyu a gabanki tana neman afuwarki." Yarjejeniyar da Fargi ta ulla tsakaninta da ba en aljanun ita ta sake ba ta damar samun aukaka mafi rinjaye a cikin dajinsu, har ya zama ayyukan tsafi da dama sun koma hannunwanta sai dai idan ta ga aikin ya yi mata sai ta mi a wa Shugaba Zurufu ya tayata. Wannan aukakar da Fargi ta sake samu sai ta sake ninka iyayyarta da ke cikin zuciyar Shugaba, har ya fara ke antacciyar shawara da shugabannin aljanu domin su ba shi mafitar
Chapter 48 · 0% Book details