← Book details Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 89

Sashe 21

Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wayo ba yake aunar kyanwa don haka ya tsugunna da niyyar kai hannu kanta, da sauri ya ji an fisge shi gefe wa ansu surutai na tashi sama-sama a cikin kunnuwansa. Waigawa ya yi bai sake ganinta ba, ya ci gaba da tafiya. A jikin wata murgujejiyar bishiyar kuka ya hangi wata rantsatstsiyar karaga, "Je ka arasa kan karagarka." Ya ji an furta masa. Wani irin sanyi ya ji yana ratsa shi, jiki a sanyaye ya fara takawa da niyyar hawa kan shimfi ar da ke auke da karagar, ga mamakinsa sai ji ya yi wannan ba ar magen ta hanka a shi gefe aya. Ta ora wani mulmulallan abu mai kama da awai a kan karagar, sannan ta fara zagaye karagar cikin asaita. A can asa ya fa i kansa ya bugu da wani farin dutse take jini ya fara iga, dafa wurin ya yi cikin azaba sai gani ya yi magen ta araso tana lasar jinin da ke zuba daga goshinsa. Ta fara aga kanta tana da alamar tana son kai wa kansa farmaki wurin da ragowar jinin yake iga. Ganin ta dumfaro shi ya sa ya ci gaba da ja baya zuciyarsa na dakan luguje, ganin haka ya sa magen ta fara wata irin dariya fi inta na zubowa asa aya bayan aya. Duk wurin da fi ar ta fa a sai asar wurin ta rufta har ta yi tsalle za ta dam i saman goshinsa. Firgigit Kamalu ya tashi cikin matsanancin tsoro, firgici da tashin hankali. A lokacin dare ya tsala sosai, ban da munsharin mutanen akin da kukan tsuntsaye babu abin da yake tashi. Jin abu na gangaro masa a goshi ya sa ya kai hannunsa ga mamakinsa ya ji ya ta a abu, da sauri ya yun ura zuwa wurin aci-balbal in da ke kunne a gefen akin ya haske. Rass! Gabansa ya fa i, jikinsa ya auki karkarwa kamar mazari. "Jini!" Ya furta a ki ime. Yana shirin komawa ya tashi Baffajo ya sanar da shi abin da faru ya ji an dafa kafa arsa. "Wannan gidan ba irin kowanne gida ba ne, sai ka aura amarar juriya da jajircewa. Gadon gidanku ba a sansu da sarewa ba, ka zama jarumi mara tsoro a haka ne za ka waci kanka. Ka gode wa Allah da ba ta yi nasarar yagar naman jikinka ba, kuma kada ka auka za ta ha uri. Wannan da iyar mummunar manufa ca tunkafin haihuwarka, zan yi takaici warai matu ar ta yi nasara a kanka kamar yadda ta ci galaba a kan mahaifiyar..." Sam Kamalu baya fahimtar kalaman da farin dattijon ke gaya masa, cike da damuwa ya katse shi. "Don Allah wane ne kai? Ya aka yi ka san mafarkin da na yi?" Murmushi Dattijon ya yi, "Yaro man kaza! Da sannu za ka fahimci turbar da nake son ora ka, izza da asaitar jinin Sarki Muhammad Safwan ba za ta tashi a banza ba. Ba ni zan bayyana wa duniya waye kai ba, izza da tasirin jinin sarautar da ke jikinka ne zai bayyana wane ne kai. Ni Aminin Kakankakanka ne, ina bibiyar al'amarinka saboda wa ansu muhimman abubuwa da tasirinsu. Ta so mu je ka wanke ciwonka a wancan rafin, idan gari ya waye kada ka sanar da kowa mummunan mafarkinka hatta Baffajo da Inna wuro, domin wannan gidan sarautar cike yake da idanu mabanbanta." Tamkar ra umi da aka a haka Kamalu ya bi bayan tsohon yana gaba shi kuma yana biye da shi, lokacin da suka arasa bakin rafin wani irin sanyi ne ya fara ratsa shi har sai da jikinsa ya auki rawar ari. Kaf kaf kaf ha oransa suka fara rawa, ga wata irin juwa da take arin fisgar shi ko ta halin agowa ya yi a wahalce ya furta. "Ba zan iya ba, ba zan iya zuwa ba sanyi nake ji." Rufe bakin Kamalu sai dajjijon ya sa hannunsa a tsakiyar goshinsa, a hankali ya ji sanyin da yake ji yana raguwa, "Ba na jin da i a duk lokacin da ga karaya a wayar idonka, daga yau kada na sake jin ka furta kalmar gazawa. Tabbas za ka iya domin duk tsawon lokacin da muka auka lokacinka muke jira, mu je ka aiwatar da abin da yake gabanka." Dattijon ya fa a yana kama hannun Kamalu ya sanya afarsa ta dama a cikin rafin, wani irin zuuu! Ya ji har cikin kwanyarsa. Gabansa na fa uwa ya tsugunna a ebi ruwan ya wanke ciwonsa kamar yadda tsohon yake ba shi umarni, yana gamawa ya sake ba shi umarnin wanke fuskarsa ya ura masa ruwan a cikin kunnuwansa. Ruwan ya gani ya fara ka awa a hankali, daga baya kuma ya ga igiyar ruwan tana katantanwa da su. Yana shirin guduwa tsohon ya ri e shi tsam a jikinsa, ganin a kowanne lokaci yana iya halaka ya sa Kamalu runtse idonsa. Sannu a hankali ya ji komai yana lafawa, hakan ya sa shi bu e idonsa suka fara takowa suka fito daga ciki. Wani irin sauti yake ji cikin sigar kururuwa da neman auki, lokaci aya ya ji zuciyarsa na fisgar gangar jikinsa. Tafiya yake yi ba tare da ya san wurin da yake jefa afafuwansa ba har ya zagaya wurin da yake jin arajin sautin na kusantarsa a bayan akin Mai martaba. A saitin kusurwar yamma ya hangi wani mulmulallan abu ba i saboda duhu bai tantance takamaiman mene ne ba. Cikin dakiya da arfin zucuya ya sa ka hannu da niyyar tonowa take zoben hannunsa ya mamaye wurin da haske, a nan ya yi tozali da wani abu mai tsananin wari da siffar jarirai har sai da ya ji tamkar ya amayar da kayan cikinsa. Tsaki ya yi cike da jin haushin abin da ya aikata, shi kansa bai san dalilin da ya sa shi aikata haka ba, ya dai ji ba za iya ha ura ba har sai ya taimaki abin da yake cikin ashin asar. Koda ya koma sama da asa ya nemi Dattijon ya rasa, a bakin ofar akinsu ya hangi Baffajo yana kai wa da kawowa yana ganin Kamalu ya arasa yana tambayarsa inda ya je. "Baffajo fitsari ne ya tashe ni, na ga kana bacci shi ya sa ban tashe ka ba." Ya tsinci kansa da in fa a wa Baffajo gaskiyar abin da ya faru. Ri o hannunsa Baffajo ya yi tsam kamar wani zai wace shi suka arasa cikin akin, wallah ce ta ciko idanun Baffajo ya furta. "A wannan farautar da aka yi mana mun rasa Salele Kamalu yanzu haka ban san duniyar da ya nufa ba, don Allah kada ka yi yun urin abin da zai raba ni da kai, ka ga wancan rafin dai an ce hallaka mutane yake don Allah koda wasa kada na ga gilmawarka a wurin." Kamalu ya jinjina kai sannan ya koma ya kwanta cike da tausayin mahaifinsa. Tun da asubar fari aka tashi duka Bayin da ke sashen kamar yadda aka sunnanta musu, bayan sun idar da sallar asuba Uwar Bayi ta shiga raba wa sababbin Bayi aikin da za su gudanar, wa anda suka san aikinsu kuwa suka ci gaba orawa daga inda suka tsaya. Sai da rana ta fara fitowa sannan suka samu zarafin kai abinci cikin bakunansu, Mai gado ita da Inna wuro kusan ura suka yi wa kansu da sauran ba in Bayin da aka kawo su rana aya. Baiwa Fatsim na ganin yadda suke cin abinci ta saki shewa tana yi musu kallon she e ta furta. "Ahayye! Allah na dawo inji kishiyar mai yaji, duk wannan fele en da kuke yi gumi ce ba ta yi gumi ba. Amma da sannu za ku gane karatuna." Gaba aya babu wanda ya tanka musu, wata Dattijuwa da suka ji ana jira da Uwar tuwo ta arasa wurin ta ce, "Tun wuri ku cire kawaici da kara ku fara watar wa kanku 'yanci idan ba haka ba kowa takaku zai yi kamar takalmin sawarsa. Wannan gidan yana da matu ar bambamci da wuraren da kuka fito..." Sallamar Jakadiya ta katse ta, fuska a ha e ta dube su aya bayan aya. "Zan ebi sababbin Bayi gaba ayanku zan kai ku sashen Fulani Umaima tana son za ar wa anda suka yi mata domin tana bu atar arin masu yi mata hidima." Jin babu wanda ya tanka mata ya sa ta buga musu tsawa, jiki na rawa duka suka mi e sai Inna wuro da ke faman jera loma da sauri don ita idan tana cin abinci tana tashi duk da in abinci ba ta iya cinsa, ballantana a nan da abincin dare da suka ci ko ka an bai ishe su. Jakadiya ta le a ganin Inna wuro na zaune. "Ke ce shafaffiya da mai ba ki ji abin da na ce ba?" Baki na rawa Inna wuro ta sanar da ita uzurinta, ai kuwa lokaci aya ta ji an kwashe mata da dariya. "Ke a tsammaninki tun da kika shigo masarautar nan kina da sauran ikon da kanki? Ko kin manta matsayinki na Baiwa ne? Idan ba ki sani ba ki sani a yadda kika a cikin gidan nan sai yadda aka yi da ke, idan aka so ki kwana a tsaye dole ki kwana, gara tun wuri ki yakicewa kanki an guntun 'yancin da kike ta ama da shi." A sanyaye Inna wuro ta tashi, idanunta suka ciko da walla. A duniya babu abin da ta tsana sama da yarfi da tozartawa. Babu yadda suka iya haka suka bi bayan Jakadiya haka kawai Mai gado ta tsinci gabanta na matsanancin fa uwa, tun da suka nufi sashen Fulani Umaima Jawahir ke wani irin mutsu-mutsu har zuwa lokacin da Jakadiya ta sa suka jeru aya bayan aya. A hankali ta fara bin Bayin tana duba su a wula ance cikin yarfi da antarwa. Tana zuwa daidai kan Mai gado gabanta ya yanke ya fa i, ta dube ta a yamutse. "A sauko da wannan jaririyar." Ba musu Mai gado ta kunto Jawahir da jikinta ya yi wani irin sanyi kamar wacce aka ciro daga ara. Sauke idanun Fulani Umaima a kan wayar idon Jawahir ya haddasa mata matsananciyar fa uwar gaba, kalaman Bamaguje suka fa o mata. Ba ta
Chapter 21 · 0% Book details