← Book details Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 89

Sashe 43

Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'ya'yanta aka ci ku in da amarya, kenan sai a ce ita don me za ta mutu a wannn lokaci? Shin dama idan ka yi ha uri a kan abu dole ne sai ka ga sakamako? Sam ba haka ba ne, akwai abin da za ka ga sakamakonsa wani abin kuma sai dai Ubangiji ya yi maka tukwici a kan ha urin da ka yi, tun da dama Ya ce shi yana tare da masu ha uri. Ita rayuwa sai wani ya rasa wani yake samu, kuma mutuwar wani tashin wani ce. A lokacin da wani zai mutu sai ka ga a lokacin ne shaharar wani take bayyana.* *Masu cewa ya kamata Kamalu ya ji da in mahaifiya, su kuma 'ya'yan da suke tasowa a gidan Marayu ba su da kowa ya za su yi da rayuwarsu, shin muna tuna irin yanayin da suke ji a zuciyarsu? Ballantana Kamalu ya samu iyayen goyo na gari, masu ba shi kulawa. Wasu fa mahaifiyarsu na haihuwa take mutuwa kuma su taso cikin tsangwama kenan sai a ce don me?* *Wasu na ganin ana nuna wa Fulani Umaima asirinta na yin tasiri kullin, kun manta duk mai bin bokaye da 'yan tsubbu gani yake a kullin duk abin da ya faru asirinsa ne yake tasiri? Duk fa wanda ya mutu dama lokacinsa ne ya yi sai dai ya kasance da sanadi, abin dariya wasu har cewa suke wai arfin boka fi arfin Allah? Kun manta da hadisin da ke magana akan samuwar bawa tun yana cikin mahaifiyarsa, ana addara wa Bawa duk abin da zai faru da shi tun yana cikin mahaifiyarsa? Dama can Fulani babba a wannan ga ar ajalinta yake sai ya kasance da sanadin Umaima, ko ciwo fa wani bai isa ya saka maka ba sai dai idan dama can Allah ya addari hakan zai faru da kai. Kuma a baya a wurare da dama an nuna asirin nata yana sanyi har Fulani babba ta samu kusanci ga mijinta.* *Kun saka ni rubutu da farar safiya da dogon sharhin da ban shirya ba ba fa ku ka ai kuka ji mutuwar Fulani ba ni ma ta dake ni wallahi, to amma kun san an ce wata shari'ar sai a lahira don haka Fulani dai babu ita sai mu ga Umaima za ta samu yadda take so ko akasin haka? Kuma idan muka bar Fulani Babba ta rayu ai Umaima ta ci banza da yawa arshe sai a ce ta nemi yafiyarta kuma Fulani babba ta yafe? Haba ai gara duka su yi nadama a lokacin da nadamar ba za ta yi amfani ba.* *Yanzu dai a samu wata ta toyo mana wainar sadaka sai wasu su wakilce ni a rarrabawa ma ota, don yanzu haka makaranta zan tafi.* Tamkar ra umi da akala haka Kamalu ya ci gaba da bin Datijjo Maharaz sai dai babu wanda yake tankawa wani, suna gab da shiga wani soro mai duhu Kamalu ya ji gabansa ya bada rasa! Har sai da ya sa hannuwa biyu ya dafe irjinsa, tun da ya zo duniya bai ta a jin fa uwar gaba irin wannan ba. Runtse idanunsa ya yi yana sauke ajiyar zuciya, Dattijo Maharaz ya matsa kusa da shi ya kamo hannunsa na dama. "Ka yi ha uri Kamalu! Ina mai ara ba ka ha uri a duk yadda rayuwa za ta zo maka, da duk labarin da za ka ji a nan gaba. Ban so haka ta kasance a tare da kai ba sai dai ka san ita rayuwa abokiyar tagwaitagar addara ce, ka sa a ranka duk abin da ya faru da kai shi ne mafi alheri. Na so a ce fuskokinku sun sadu da juna koda sau aya ne, amma haka kundin addararku ya zana muku. Ka yi ha uri na tabbata lokaci na tafe da sau i zai zo a gare ka." Shiru Kamalu ya yi yana sauraron Dattijo Maharaz a tunaninsa sai ya yi tsammanin yana ba shi ha uri ne silar abin da ya ji daga wurinsu Baffajo. "Babu koma Dattijo Maharaz kuma ina godiya da gudunmawar da kake ba ni. Na amince zan bi ka ne kawai don yayewar damuwar da nake ciki, a baya ban san wa annan tarin matsalolin ba Dattijo Maharaz." Kamalu ya arasa maganar cikin raunin zuciyata. Ta cikin wannan zauren mai duhu suka shiga a tsammanin Kamalu za su fita ta cikin gida ne, sai kuma ya ga sun illa bakin wani an rami mai auke da ta o, daga gefe kuma a wata 'yar gajeriyar katanga jikinta auke da sawayen hannuwan mutane. Da mamaki Kamalu ya furta. " Ina ne nan Dattijo Maharaz? Wannan sawayen hannun su waye?" Kamar saukar aradu haka Sarki Abdul'aziz ya dira a cikin akin Fulani Babba, Mai gado ta ago ta dube shi take ta ji wani unci da haushinsa sun mamaye ta. Uffan ba ta iya tanka masa ba ta auke kanta gefe. "Ka gafarce ni ranka shi da e bisa mummunan al'amarin da ya fa o mana." Baiwa Zainaba ta fa a jiki a sanyaye. Bai amsa musu ba yana tsaye wayar idonsa na kan gawar Fulani babba, a hankali ya fara aga afarsa ya isa gaban gawar tata ya tsugunna a gefen gadon. Hannunsa na rawa ya sa ya bu e yaye zanin fusakarta ya kai kunnensa saitin irjinta. Wani abu ya ji ya danne irjinsa, kamar aramin yaro ya ara kansa a gefen irjinta hawaye bibbiyu na zuba. Daga Mai gado har baiwa Zainaba suka sunkuyar da kansu asa suna zubar da wallah, motsin da suka ji a gefensu ne ya sa suka ago Fulani Umaima ce a tsaye tana bin akin da kallo. Ganin kukan da Takawa yake yi a jikin gawar Fulani babba ya sa ta ta e baki cikin takaici, sai da ta arasa gaban gawar sannan ta rushe da wani irin kuka. Yadda Fulani Umaima take kuka har da majina sai ka rantse mutuwar Fulani babba ba aramin dukanta ta yi ba. Jakadiya da Sailuba ne suka shiga sai dai ganin irin kukan da Fulani Umaima take yi ya sa suka yi turus, lokaci aya suka kalli juna hatta Mai gado sai da ta fahimci Fulani Umaima kukan makirci take yi. "Ya Allah ga baiwarka nan Allah ka ji anta ka gafarta mata, kaico rayuwa Fatima ta tafi ta bar ni." Takawa ya furta a imauce. "Me ya sa za ki tafi ki bar ni Fatima!" Ya yi maganar a zauce. "Mtsswww, aikin banza!" Fulani Umaima ta fa a cikin su ucewar baki don ba ta ta a tsammanin zancen zucin da take yi zai fito fili ba." A hargitse Mai martaba ya waiga wurinta amma da yake ta san kanta sai ta juya wurin su Mai gado da ke zaune a asa ta furta. "Ku tashi ku fita mana ku bar mutane da abin da yake damunsu." Da sauri su Baiwa Zainaba suka fice jiki na rawa. Tsanarta ta sake mamaye zuciyar Mai gado, auke kansa ya yi don a tunaninsa a kan maganar da ta yi wa su Mai gado ne take yin tsaki. "Allah ya taimaki awisu, Ubangiji ya kwanta makwancin Fulani. Na ce ko za a yi mini izini na fitar da sanarwar wannan babban rashim da aka yi mana?" Kai kawai ya iya gya a mata, Jakadiya ta fice da sauri. Shi kuwa Abubakar yana can gefe a zaune sai bin su yake da kallo aya bayan aya, kamar wanda ya ga sabuwar hallita haka ya tsaya yana kallon Takawa saboda rashin saninsa da bai yi ba, Mai martaba ya rufe Fuskar Fulani sannan ya arasa wurin Abubakar. "A lokacin da mahaifiyarka take raye babban burinta bai wuce ta ga warkewarka ba, ta fuskanci alubalen rayuwa a wurina duk silarka sai dai kuma Ubangiji ya auke ta a ga ar da kake ci gaba da neman kulawarta. Allah ya gafarta miki Fatima ha a na yi babban rashin da har abada ba zan manta shi ba, na yafe miki duk abin da kika ta a yi mini a rayuwa duniya da lahira." Wani haushi ya mamaye zuciyar Sailuba, ita kuwa Fulani Umaima ban da jefa masa harara babu abin da take yi. "Ka gama iyayinka ina nan zaune za ka dawo ka same ni." Ta furta a zuciyarta sannan ta saki murmushi sakamakon kallon gawar Fulani Babba da ta yi, da kuma ta tuna a yanzu magani aya ne ya rage mata ta arasa aiwatarwa wanda za ta cusawa gawar Fulani aurarriar fatar a gabanta sai farinciki ya mamaye ta. Mai gado tana tafe tana kuka saboda tashin hankali duk wanda ya tambaye ta ba ta iya koda furta masa kalma aya, akinta ta fa a ta zauna a gefe gado nan take ta sake rushewa da sabon kuka mai cin zuciya. A rayuwa bayan mutuwar mahaifanta wannan ce mutuwa ta farko da ta ta a ta, sun yi wata irin sha uwa da Fulani ko ka an ba ta nuna mata kyara a matsayinta na shugabarta. Jin kukan da Mai gado take yi i ci ya i cinyewa ya sa Jawahir ta an zuro kanta daga cikin zanin don har lokacin jikinta bai daina karkarwa ba. "Inna... Innaaa me yake faruwa?" Jin yanayin muryar Jawahir ya sa Mai gado ta waiga, sai da ta share hawayenta ta furta. "Me yake damunki Jawahir?" Kamar mai jira sai kawai Jawahir ta fashe da kuka, Mai gado na shirin kawo hannun Jawahir ta ji wani irin zafi zaauu da jikinta ya yi. Da sauri ta yaye zanin a hargitse ta furta. "Ba ki da lafiya ne Jawahir." "Inna wallahi wannan matar ce, tsoro nake ji Inna kar ta kashe ni." irjin Mai gado ya yi wata irin bugawa da arfi. "Wace ce Jawahir? Ki kwantar da hankalinki In shaa Allah ba za ta yi miki komai ba." "Inna kin ga cikina fa, Allah mutuwa zan yi." Jawahir ta arasa maganar tana bu ewa Mai gado cikinta. Zumbur Mai gado ta mi e jikinta na karkarwa, tambarin cikinta ne ya da a yin wani irin ja a an tsorace Mai gado ta mi a hannu tana son ta awa zuciyarta na harbawa. Da yar ta yi ta maza ta ora hannunta a jiki wani irin zuuuu ta
Chapter 43 · 0% Book details