Sashe 73
Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da ya zauna ya yi masa magana ta fahimta sai suka fahimci juna ya kuma ja shi har uwar aki ya nuna masa asalin wurin da suke rayuwa. Tun daga wannan ranar zumunci mai arfi ya shiga tsakaninsu, don an ce wani lokacin haka kakana zai ziyarce shi su sha hira kuma duk abin da ya ga Sarki Sadi u zai yi ba daidai ba zai yi masa gyara. Kuma an ce suna matu ar ba wa juna shawarwari akan abin da ya kamata da harkar masarautunsu, har dai tafiya ta mi a Sarki Sadi u ya kwanta dama. An yi sarakuna da dama daga jinsina zuwa naku a cikin masarautar nan har kawo lokacin da muka ha u da amini marigayi Muhammad Safwan." Idanun Dattijo Maharaz suka ciko da walla, ya an ha iyi yawu mai aci sannan ya ci gaba da cewa. Kafe shi da idanu Fargi ta yi tana mamakin yadda aka yi Shugaba ya gano gaba aya halin da take ciki, ta furzar da iska mai zafi sannan ta ce. "Ya aka yi kasan da haka?" "Kamar kin manta a gaban wanda kike Fargi?" "Shi ya sa na tambaye ka, don da wani ne ba kai ba sare kanshi zan yi." "Kin manta hukuncin wanda ya aikata abin da kika yi kisa ne a cikin zuri'armu?" Shugana ya wurga mata tambaya. "Ina sane da haka, kuma dalilin hakan ya sa nake son ruguje wannan mummunar abi'a ko al'adar da ba ta da amfani." "Idan na bayyana wa mutanen gari kin san take za su zartar miki da hukunci." A razane Fargi ta dubi Shugaba Zurufu, fuska da muryarsa ko ka an babu alamun wasa a ciki. "Idan kika ce da tashin hankali za ki biye masa tabbas za a yi biyu babu, zai sa a kashe ki kuma ki rasa abin cikinki. Tun wuri ki san abin yi tun talatarki ba ta are a raba ba." Zuciyarta ta wassafa mata bayanai. Sai da ta gyara zamanta sannan ta dubi Shugaba Zurufu ta ce. "Me ya sa za ka yi mini haka Shugaba? Ka san dai kai ne mai lulla a mini bargon sutura ya kake yun urin yaye mini wanda na lullu a wa kaina?" "Saboda tun farko kika bijire mini a kansa, ina nufin Sarki Sulaiman." Shugaba Zurufu ya yi maganar zuciyarsa fes don ya lura da samun nasarar da ya yi a kanta. "Yanzu me ye abin yi Shugaba? Ina son mijina kuma ina son abin da yake cikina!" Fargi ta furta tana zuba masa manyan idanunta. "Zan taimaka miki har ki haife abin cikinki ba tare da wani rai mai numfashi ya fahimci halin da kike ciki ba. Na rantse miki da gawurtar tsafina ko mahaifinki ba zai san da cikin jikinki ba ballantana ya san ranar da za ki haife shi." "Ina matu ar alfahari da kai Shugaba Zurufu..." "Amma da shara i." Shugaba Zurufu ya katse ta. "Wanne shara i ne? Matu ar zan iya masa na amince zan cika maka shi." "Za ki mallaka kuma ki sadaukar mini da dukkan tsafinki." A zabure Fargi ta mi e tsaye jikinta na karkarwa, "Kana nufin tsafin da nake rayuwa a doronsa?" Fargi ta jefa masa tambaya a imauce. Gya a mata kai Shugaba ya yi, wani tunani ya fa o mata ta koma ta zauna murya a sanyaye ta furta. "Kalamanka sun gigita ni Shugaba amma zan yi tunani game da wannan furucin naka! Ina son Tsafina, ina son mijina kuma ina son cikina! Dole zan za i abin da zai fi dacewa da rayuwata." Shugaba Zurufu ya ji da in kalaman Fargi, ta yi masa sallama cike da damuwa ta fice daga kogon tsafinsa. Tun a daren ranar Fargi ta nemi Sarki Sulaiman ta sanar da shi halin da take ciki dangane da abin da Shugaba ya ullo mata da shi, ya ka u matu a har sai da ya yi yun urin zuwa wurin Shugaba don ya ci masa mutumci amma Fargi ta dakatar da shi don ta san matu ar ya aikata wannan kuskuren Shugaba sai ya hallaka shi. "Fa a da aljani babu riba! Ka bar mini komai a hannuna, na san ta yadda zan ullowa al'amarin." "Na rantse da girman Allah matu ar ya ta a mini mata ko abin da yake cikinta sai na tozarta shi." "Ba na son jin haka daga gare ka gwarzona, kamar yadda na ce ka bar mini komai zan san hanyar da zan ullo masa ta ruwan sanyi." Jin shirun Mai gado da ya yi yawa ya sa Jawahir ta diro daga kan gado ta janyo ofar akin ta rufe, sannan ta le a can ashin gadon ta zaro littafin. Haka kawai ta ji gabanta na fa uwa ta haye can saman gadon ta bu e shafin baya, ta ga duk ya shafe babu ko igon rubutu a jiki. A hankali ta ci gaba da bu ewa har ta kai shafin da ya fara da rubutu, ta yi jim kamar mai nazari sannan ta ago ta ci gaba da karantawa. Sai da Sarki Hafiz ya kur i ruwan da ke gabansa sannan na ji ya ci gaba da cewa. "Na ji labarin an ce Kakana ne ya kai ziyara wurin wani babban boka, a binciken da yake yi masa ne ya tabbbatar da cewar Mahaifiyarki na auke da kwantaccan cikinki, kuma matu ar ya bari aka haife ki duk daren da ewa sai kin kar i kambun sarautarku ya dawo hannun zuri'ar mahaifinki. Dalilin da ya sa Kakana ya shiga binciken wurin da Mahaifiyarki take, kuma abin da bai sani ba tuni wani aminin mahaifinki aljani Sadi ya oye mahaifi da mahaifiyarki. Sakamakon tuni ya sanar da su abin da yake faruwa." Jin Sarki Hafiz ya yi shiru ya sa na dube shi, sai kawai na ji muryarsa ta yi rauni ya furta mini. "Ki yi ha uri da wannan furucin da zan furzo miki." A sanyaye na dube shi ina yun urin yin magana na ji ya ci gaba da cewa. "In ta aice miki labari an ce a ranar da al adarin zamanki a cikin mahaifiyarki ya are ita kuma a ranar Allah ya yi mata rasuwa, a yadda na ji labari an ce ko fuskarki ba ta iya gani ba ballantana ta san kalar hallitar da ta haifa. Mutuwar mahaifiyarki ba aramin aga hankalin mahaifinki ta yi ba, an ce sai da ya shafe sama da watanni yana jimamin mutuwarta. Daga lokacin da ta haife ki sai rainonki ya koma wurin mahaifinki da amininsa Aljani Sadi, kuma kin sha u matu a da mahaifinki kwatsam! Watarana ya wayi gari da ciwon ajali wanda a sanadinsa ne rai ya yi halinsa." A razane na dubi can gefen da nake ganin mutumin da a kullin yake ce mini shi mahaifina ne. Jikina na karkarwa na nuna wurin da yake tsaye yana sakar mini murmushi na furta. "Shi kuma wancan da nake kallo a matsayin mahaifina waye shi?" "Jawahir lafiya kika datse mini ofa?" Kalaman Mai gado suka katse Jawahir daga karatun littafin da take yi, da sauri ta rufe littafin ta tura shi can ashin gado sannan ta zare sakatar akin. "Inna wallahi sanyi nake ji shi ne na rufe akin, har kin dawo?" Mai gado ta kafe ta da idanu tamkar tana son gano gaskiyar abin da Jawahir ta gaya mata. Kai kawai ta gya a mata sannan ta wuce cikin akin, Boka Shaddas da ke la e a bayan akun nan Bayin ya yi wafa yana sake la ewa don ya ci alwashin a wannan ranar sai ya auke Jawahir ya kai wa Shugaba Zurufu ko ya fanso Basirunsa. "Allah ya gafarta wa aminina." Dattiji Maharar ya furta jiki a sanyaye. Kamalu ya arasa gabansa ya zauna a gefensa, cikin sigar lallashi ya furta. "Tabbas na fahimci abin da kake ji a zuciyarka Dattijo Maharaz, na fahimci haka ne bayan rashin su Inna wuro da na yi a kusa da ni. Addu'a ita za ka bi amininka da ita tun da duk mai rai mammaci." Jinjina kai Dattijo Maharaz ya ci gaba da cewa. "Mahaifina ya ba ni labarin cewar tun ina rarrafe muka ha u da Sarki Muhammad Safwan a lokacin da mahaifiyarsa take shiga da shi turakar mahaifinsa, wannan abota tamu ta kai har zuwa samartakarmu, duk inda aka ga Sarki Safwan za a ganni a wurin. Hatta wurin zance ni nake yi masa rakiya, don ko ita marigayya da ya aura ba ta ta a sanin ni ba jinsinku ba ne har sai bayan aurin aurensu. ar irin sha uwar da muka yi da Marigayi abin zai auke mu lokaci mai tsayi, amma abu aya na sani ni da shi aminai ne da muke fatan saduwa har ranar gobe iyama." "Ma shaa Allah! Allah ya cika buri Dattijo Maharaz." Mahaifin Fulani Umaima ya furta zuciya a karye. "Ba tun yau ba mahaifina ya sanar da kai tasirinka a cikin masarautar nan, ya sanar da ni bincikensa ya nusar da kai wanzuwarka. Shin ka tuna wurin da na kai ka Kamalu? In da na ce ka auki ta o ka shafa a bangon wurin?" Da sauri Kamalu ya furta. "Na tuna Dattijo Maharaz." "Duk wanda ya samu sanar aiwatar da duk abin na sa ka aiwatar ana yi masa kyakkyawan zaton kasancewa Shugaba kuma Sarki a Masarautar Huddam, ashe ala ar da ke tsakaninmu da kai ba ta wuce gurbin da Futhussam yake arin ajiye ka ba. " Dattijo Maharaz ya sake numfasawa sannan ya ci gaba. Dalilin da ya sa ba a shan kowanne irin Nono a masarautar nan ranar juma'a bai wuce wani mummuna sa ani da ya gifta tsakanin wata jikar Rabo da wani Sarki da aka ta a yi daga cikin jinku ba, wannan fa an har sai da ta kai ta kawo iyayena sun shiga ciki kuma a ranar aka tattarawa 'yar fulani kayanta aka fitar da ita daga Masarautar nan. To sai dai kafin ta tafi an kai ruwa rana da ita, har sai da ta kafa wannan shara in na haramta shan Nono a ranar juma'a kuma babban kuskuren da Sarki Rufa'i ya aikata da kai tsaye ya amince da bu atarta. An ce ta ce duk wanda ya