← Book details Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 89

Sashe 63

Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

lokacin da nake gudanar da aikina a cikin halwar tsafina?" Bamaguje ya yi maganar cike da damuwa. "Ina neman afuwarka Boka Bamaguje bisa shiga ha inka a daidai ga ar da ba ka tsammace ni ba. Shin ko ka san wannan baiwar Alahr da bawan Allahn nan?" Dattijo Maharaz ya nuna Fulani Umaima da Kamalu. "Wacce irin magana kake yi mini Maharaz? Tambayar wannan a wurina tamkar cin fuska ne da cin zarafina domin Umaima jinina ce 'yata ce ta cikina halak-malak ni ne mahaifinta. Shi kuma wannan yaron ban san shi ba, sai dai zan iya shiga halwar tsafina na bincika tauraronsa..." arya kake Bamaguje! Wallahi arya kake ni ba 'yarka ba ce. Wallahi sharri zai yi mini ranka shi da e ni ban san shi ba ban ma ta a ganinsa ba." Murmushin Dattako Dattijo Maharaz ya saki. Lokaci aya fuskar Bamaguje ta murtuke rai a ace ya nuna Fulani Umaima ya furta. "A yau ba sai gobe ba na rantse da girman tsafina da sihirin da nake ta ama da shi sai na nuna miki ke in 'yata ce babu wani mahaluki da zai sake yi mini iko da ke." *SHU'UMAR MASARAUTA* *33* *Littafin ku i ne 500 idan kina bu ata za ki biya ta wannan Account in Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.* Jin kalaman Shugaba Zurufu ya sa kan Jakadiya ya sake girma, ta sunyar da kai asa tana sakin murmushin farinciki. A angare aya kuma tana addu'ar Allah ya tsallakar da ita daga mu'amalar da aka ce an autan aljan zai yi da ita. Kamar Shugaba Zurufu ya shiga ranta ya furta mata. "Ban ta a tsammanin samun biyan bu atar nan tawa a cikin ruwan sanyi ba, don haka Jakadiya mun auke miki mu'amala da an auta Buguzu. Sannan a daren yau ba sai gobe ba zan fatsama gudanar da aikinki a cikin halwar tsafina." Jakadiya ta sake sunkuyar da kai sannan ta fara zuba masa godiya, wata jar tsoka ya auko ya mi a mata wacce take igar da wani ba in jini mai wari. "Ki je ashin gidan tururuwa ki binne ta a ciki, bayan kwana biyu ki saurari abin da zai biyo baya." Cikin matsanancin Farinciki Jakadiya ta mi a hannu za ta kar a da sauri Shugaba Zurufu ya matsar da hannunsa sai da ya jefa tsokar naman a ciki wata 'yar jakar fatar ya sake mi a mata. "Kin so ki yi ganganci Jakadiya, da a ce kin ta a wannan tsokar da duk abin da na yi niyyar ulla wa Umaima kanki zai fa a." A razane Jakadiya ta ja baya, Shugaba Zurufu ya saki murmushi sannan ya Sallame ta. Har ta juya za ta tafi ta dawo da sauri idanunta a kan Basiru ta furta. "Ya kai Shugaba Zurufu shin a ta yaya zan iya mayar da Basiru cikin masarautar Huddam? Ina tsoron kada asirina ya tonu." "Wannan ba aikinki ba ne Jakadiya! Ki bar mini komai a hannuna ni zan aiwatar da komai." Tsoro ne ya mamaye Jakadiya don sai a yanzu wani tunani ya fa o mata. "Shugaba ina fatan ba za ka hallaka shi ba, domin ina tsoron kada wani abu ya faru da shi ni ma na shiga uku." Jakadiya ta yi maganar a firgice. "Babu abin da zai faru da shi Jakadiya, kuma kada wannan ya dame ki domin zan aika wani aljanin ya riki e zuwa surarsa ta yadda wani ba zai fahimci ba shi ba ne." Sai a lokacin Jakadiya ta sauke ajiyar zuciya sannan ta fice daga kogon dutsen tana jin zuciyart fes tamkar bu atarta ta gama biya gaba aya. Bayan fitar Jakadiya runtse idanu Shugaba Zurufu ya yi ya fara karanta wa ansu alasuman tsafi, ya an jima yana yi nan take kogon dutsen na shi ya rufe ruf sannan ya zaro littafin yana jin wani shau i da farinciki ya lullu e shi. Saboda yanayin tsufa hannunsa sai karkarwa yake ya saka hannu ya bu o littafin nan take ya ga a daidai wurin da Boka Shaddas ya tsaya da karatu. Ya saki malalacin murmushi sannan ya furta. "Tabbas ka rage mini aiki da yawa Boka Shaddas." A wannan karon ba Kamalu ba hatta sauran mutanen da ke cikin akin tsananin mamaki ne ya kamasu, Sarki Abdul'aziz ne ya yi arfin halin kallon Boka Bamaguje don mafi yawan su ba aramin tsoro ya ba su ba. A zaune yake jikinsa babu kaya sai ugunsa da ke aure da wata fatar damunsa, jikinsa a lulku e da gashi kansa zagaye da furfura har zuwa fuskarsa da ta yi buzu-buzu babu kyawun gani. "Dattijo Maharaz, tarin tunanninka sun yi wa kwanyata jerin gwanon da na gagara kunce koda ulli aya ne, kuma lura da hakan bai sa ka fasa rikito mini da wa ansu ullin da suke sake dulmiya kwanta cikin taikun tunani ba. Wane ne wannan bokan da nake jin yana ala anta kansa da iyalina?" Dattijo Maharaz ya sake nuna Umaima sannan ya ci gaba. "A yadda na ji Bamaguje ya furta shi mahaifinta ne, ka ga arin bayani muna saurare daga wurinsu Sarki Abdul'aziz. Amma kafin mu kai ga wannan shin Boka Bamaguje ko ka gane wannan yaron?" Bamaguje ya ura wa Abubakar idanu sannan ya saki wata irin dariya har sai da sauran mutanen suka an tsorata. "Da a ce Umaima ta nuna ima da mutumcina a idanun tarin wa annan mutanen ciki har da Sarki Abdul'aziz, ina ganin da babu abin da zai hana ban lulli a mata bargon rufin aziri na wanke ta ba. Amma tun da ta kwaye mini baya ta nemi cin zarafina, babu abin da zai hana ni banka e mata laluben sirrinta kuma daga arshe ko ta i ko ta so na auke ta zuwa kogon tsafina ta dawwama a wurina." Da ace su Sarki Abdul'aziz na ganin yadda zuciyar Fulani Umaima take bugawa da babu abin da zai hana ba su yi tsammanin tarwatsewarta a wannan lokacin ba. "Wannan yaron tun yana cikin mahaifiyarsa ba ba ona ba ne domin daga shi har mahaifiyarsa, na yi rikitattun ayyuka da dama a kansu. Sannan tsafi ya ba ni nasara don a wancan lokacin zan iya yin komai domin farincikin 'yata Umaima, sa anin yanzu. A ta aice dai ni ne na yi asirin da ya kasance shagiri-girbau wato marar hankali." Lokaci aya akin ya auki salati ciki har da Yarima Muhsin da Sailuba. Wani irin tu in ba inciki ne ya turnu e zuciyar Sarki Abdul'aziz, a sanyaye ya juya ya ura wa Fulani Umaima idanu da ta ji e sharkaf da gumi idanunta sauka yi tsilli-tsilli kamar shege a rabon gado. "Kada ka aminta da abin da ya fa a ranka shi da e wallahi sharri yake yi mini! Bakinsu aya da Dattijo Maharaz so suke su ha a mu da kai. Wallahi-tallahi ban san duk abin da yake fa a ba." "Umaima shi fa shure-shure ba ya ta a hana mutuwa! Da tun farko kin mutumta ni ba zan kwaye miki baya ba, kuma wannan ba shi ne karo na farko da kike dagula mini lissafi ba. Don haka Maharaz idan ka gama da ni zan sa a auko mini Umaima mu ara gaba." "Amma dai ku tsinannu ne Allah ya tsine muku albarka. Allah ya isa tsaninmu da ku..." Kalaman Sarki Abdul'aziz suka katse sakamakon matsanancin kukan da ya ci arfinsa. Jikin Kamalu ba aramin sanyi ya yi ba, Ru ayya da ke gefe ta arasa wurin Takawa ita ma ta saka kuka. Shiru akin ya yi sai sautin kukan da ke tashin yayin da Fulani Umaima ke gefe tsuru kamar an ji era a buta. "Sarki Abdul'aziz na jima da jin kalmar tsinuwa a kaina, a bakin mahaifiyata na fara jin ta a farkon fara koyon tsafina lokacin da zan haike mata. Ka ga kuwa fa arka ba za ta a ni da asa ba, tambaya aya na yi shin an gama da ni na auke 'yata na yi gaba ko da saura?" Dattijo Maharaz ya jinjina kai don dama ya san dole ranar za ta zo, ranar da Sarki Abdul'aziz zai ji miyagun labaran da za su nemi tarwatsa kwanyarsa. Ya dubi Bamaguje ya furta. "Ba mu gama da ku ba Bamaguje, shin a tunaninka anyan aikin nan da kuka aikata zai tashi a banza ne?" Cikin halin ko in kula Bagauje ya aga kafa sa sannan ya furta. "Zan ci gaba da gudanar da aikina duk abin da ake ciki ina sauraronku, ke kuma Umaima ki saurare ni." "Wallahi kin yi asara duniya da lahira Umaima, yanzu ke ashe dama 'yar boka ce har kike shuka iskancinki son ranki a gidan nan?" Sailuba ta yi maganar tana wurga wa Fulani Umaima harara. Dafa kafa ar Sarki Abdul'aziz Dattijo Maharaz ya yi ya girgiza masa kai sannan ya ce. "A iya sanina kai ba mai raunin zuciya ba ne Abdul'aziz, kai jajirtaccan namiji ne me ya sa yanzu za ka aro abi'ar raunanan sarakuna ka yafa wa kanka?" "Na tuno Fatima ne Dattijo Maharaz! Na tuna irin wahala da alubalen da ta fuskata a wurina sanadin yaron nan. Na tuna irin awainiya da fa in-tashin da ta yi a kan ganin ya samu lafiya, da tarin burukan da ta ci a kansa. Me ya sa kake tsammanin ba zan koka a kan wannan ba? Fatima ta fuskanci alibalen da har abada ba zan ta a manta shi ba Dattijo Maharaz." Jinjina kai Dattijo Maharaz ya yi sannan ya furta. "Duk da na aminta da kalamanka, kuka bai cancanta a gare ka ba, don a yanzu haka kana gaban wanda yake bu atar lallashinka shi gaba aya ma bai santa ba, bai ta a ganinta ba hasali ko umin da kowanne jariri yake ji na mahaifiya bai sani ba. Ya kake tsammanin shi zai ji a zuciyarsa?" "Wane ne shi? Ban fahimce ka ba Dattijo Maharaz." Daga bangon akinsa Bamaguje ya furta. "Yaron da ke gefenka! Ina nufin Kamalu abokin tagwaitagar Abubakar. Shi ma anka ne, a iyasi da lissafi shi ne babban anka a maza domin shi ne Fulani babba ta fara haihuwa kafin Abubakar, ina nufin tagwaye ne Hasan
Chapter 63 · 0% Book details