Sashe 85
Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ya kamata a ce mun dagakatar da tsoron Shugaba daga cikin zuri'armu, Shugaba ba shi ne abin bautarmu ba don haka bai cancanci ya dinga bautar da mu yadda yake so ba." Fargi ta katse mahaifnta. "Ba yanzu ba Fargi! Ba a yanzu nake hango bijire wa Shugaba ba sai dai ko zuwa wasunmu masu zuwa a nan gaba." Cikin rauni mahaifinta ya amsa mata. "Tabbas ba a yanzu ba amma koda ba ragowar numfashi a tare da ruhina, ina fatan jinina ya zama silar wargajewar duk wani tasiri na Shugaba, da wannan mummunar al'adar da aka sa a gaba. Kuma jikina yana ba ni sauyi na gab da zuwa mahaifina, har a ciki zuciya da ruhina ina jin tamkar ni ce wacce zan zartar da wannan sauyin. Don matsayin abar bauta ka maimaita kalaman nan nawa a gaban Shugaba matsawar hakan ya faru a nan gaba." Ta arasa maganar tana mi ewa zuwa kogon tsafin Shugaba Zurufu, da kallo mahaifinta ya bi ta yana maimaita kalaman cikin tsinkewar zuciya. "A yau wa'adin kwanakin da na ibar miki suka zo arshe game da maganar da muka ta a yi da ke a baya. Fargi!" Ta ji Shugaba ya kira ta da wata irin murya, kafin ta amsa ta ji ya ci gaba da cewa. "Kada ki raina mini hankali domin ko mahaifinki a tafin hannuna yake sai yadda na sarrafa shi ba ke ba. Na hangi kusantowar abin cikin zuwa duniya, a yau ba sai wani lokaci ba za ki dam a mini tasirin tsafinki idan ba haka ba zan yaye miki laluben da kike ta amar shi ne rufin asirinki. Zan bayyanawa kowa abin da kika aikata kuma sanin kanki ne irin anyane hukuncin da ake zartarwa..." "Tura ta riga da ta kai bangi Shugaba! A baya na yi makauniyar biyayya a gare ka, sa anin yanzu da na san ciwo da 'yancin kaina. Duk wani hukunci da za ka auka a shirye nake da na fuskance shi matu ar zai kawo sauyi a rayuwar da zuri'armu take ciki, zan jure duk wata u ubu daga gare ku kuma zan san duk yadda zan yi domin na tseratar da abin da yake cikina." A razane Shugaba Zurufu ya dube ta, ya sauke wayar idonsa a kan cikin jikinta da ya rairaye ya yi asa, murmushi ya yi mata sannan ya furta. "Ko a yanzu kin nuna mini ke rainona ce Fargi, don haka ni kuma zan nuna miki ba kada kura ke da wuya ba a fe e ta shi ne aiki." Daga haka Fargi ta fice daga kogon tsafin kai tsaye ta nufi bishiyar abar bauta. Kamalu na lura da yanayin jikin Malam Umaru duk wani abin bu ata shi yake yi masa, amma lokaci sai ya lura da rikicewar jikin nasa duk da ba magana yake iya yi ba, jikinsa ya ji ya auki zafi zau cikin tashin hankali ya sa aka kira masa Waziri da wa ansu manyan hadiman fada don ya san ko ya kira 'yan uwan mahaifinsa su Galadima ba lallai su saurare shi ba. "Baba Waziru jikin Malam Umaru ya yi tsanani ya kake ganin za a yi." Kamalu ya furta cikin damuwa. "A aika yanzu a zo da Malam Sharu mai magani, In shaa Allah zai samu lafiya." Waziru ya ba da umarni. Ba a auki lokaci ba sai ga Malam Sharu mai magani ya araso rataye da jakar magungunansa na gargajiya. "Zan... sha... ruwa..." Malam Umaru ya furta murya na rawa. Tun da ya kwanta wannan ciwon sai a wannan lokacin ya samu damar yin magana, cikin hanzari Kamalu ya tallafo shi ya ba shi ruwa sai dai ka an ya samu ya sha ya ware. Sai da tarin ya lafa masa sannan ya furta. "Wani... ne... ya auke mini... Jawahir. Don Allah... Mai gado a sanar da Takawa... a nemo mini ita. Kuma a isar mini wasiyyata... wurinsa idan Jawahir ta... samu miji ya taimaka ya zama waliyinta..." Tari ne ya sake sar e shi cikin tarin ya furta. "La'ilaha'ilallah... Muhammadur Rasulilla..." Daga haka harshensa ya sar e numfashinsa ya shiga kaiwa da kawowa, kafin daga bisani ya auke gaba aya. Cikin ki ima Kamalu ya fara jijjiga shi yana kiran sunansa, ganin haka ya sa Waziri ya janye Kamalu sannan ya arasa ya rufe masa idanu. Malam Sharu mai magani da sauran mutanen da ke tsaitsaye suka fice jikinsu a sanyaye. Tamkar aramin yaro haka Kamalu ya rushe da matsanancin kuka, don idan aka cire labarin mutuwar mahaifiyarsa da wahalhalun da ta sha wannan mutuwar ita ce mutuwa ta biyu da ta dake shi a duniya. Tun tasowarsa ya taso da bawan Allah mai matu ar ha uri, karamci da sanin yakamata. A angare aya kuma Jawahir ta fa o masa da halin da za su shiga ita da Mai gado idan suka dawo suka samu labarin mutuwarsa. Gama jin kalaman aljana Zumjuttu ya harzu a Sarki Sulaiman, wani irin aci yake ji a zuciyarsa nan take jikinsa ya fara karkarwa saboda tashin hankali, a guje ya arasa ya sha i wuyan aljana Zumjuttu yana girgiza ta. "Ke annamimiya ce azzaluma maciciya, sai na kashe ki da hannuwana." Da hannu aya ta ture Sarki Sulaimanu har sai da ya kusa kai wa asa, ta saki murmushi tamkar abin da ya yi mata bai yi mata ciwo ba. "Ban san adadin irin wa annan kalaman naka da na saurara a tsakar kunnuwana ba, don haka ka adana kalamanka idan ba haka ba yanzu kai ma za ka arasa inda Fargi ta tafi. Wai ka san ma dalilin da ya sa abar bauta ba ta bi ta shafinka ba? Saboda ba ka san an haifa maka 'ya ba ballanta ka shiga duniya nemanta. Kuma na tabbata da ta san za ku sadu da juna da tuni kai ma ta hallaka ka don kar ka ba ta matsala." Zumjuttu ta furta cike da gadara. Ilahirin mutanen wurin jikinsu ba aramin sanyi ya yi ba, tsararu daga cikinsu har da masu zubar da hawaye. Mai gado ta dubi Zumjuttu cikin kuka ta ce, "Tabbas biri ya yi kama da mutum domin tun da na zo duniya ban ta a cin karo da gawar da ta tsaye mini a rai kuma ta ba ni mamaki ba tamkar ta mahaifiyar Jawahir. Don Allah don girman Allah da zatinSa ku yale yarinyar nan tun da kun hallaka mahaifiyarta..." "Mu je ki kai mu wurin abar bautarku mu gana da ita don ina son jin daga bakinta." Dattijo Maharaz ya yi maganar cikin acin rai. Cikin halin ko-in-kula ta amsa masa ta wuce gaba hannunta ri e da Jawahir da ta yi shiru sai bin mutane take da kallo, don jin abin take tamkar a mafarkinta. Gaba aya mutanen da ke gaban kogon dutsen Shugaba Zurufu ne suka rufa wa su Dattijo Maharaz baya, wasu daga cikinsu suna murnanr ganin yadda Abar bauta za ta fusata ta yi musu mummunan hukunci, yayin da wasu suke zumu in ganin yadda dambarwar za ta are. "Ku fa i ku yi sujjada a gaban Abar bauta." Zumjuttu ta furta. "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi ka ai muke bautawa babu wata hallita ko mahalukin da ya isa ya sa mu yi masa sujjada." Kamar ha in baki Sarki Abdul'aziz da Dattijo Maharaz suka furta lokaci aya. Wani irin rugugi suka ji tamkar hadari ya ha o, wasu daga cikin mutanen jin haka ya sa suka arce don gudun kada fushin Abar bauta ya fa o kansu. "Kun aikata babban zunubi don haka dole na hukunta ku, amma kafin nan me ya kawo ku wurin bautar da ake yi miki."Abar bauta ta fa a cikin isa da asaita. Dattijo Maharaz ya zayyane duk abin da suka ji daga bakin Zumjuttu, sannan ya ora da cewar. "Ki ji tsoron Allah kina hallitar Ubangiji amma kin dulmiyar da Bayin Allahn nan, me ya sa kin san gaskiya amma kika lullu e su kike dam a musu arya?" "Saboda ita ta fi kar uwa a doron asa, wai ma me ya sa kake son bayyana ainihin wace ce ni a gaban al'ummata?" Suka ji an sake furtawa daga cikin murgujejiyar bishiyar kukar gabansu. Tambayarta har ta so ba wa Dattijo Maharaz dariya, ya arasa gaban bishiyar kukar ya dafa ta sannan ya ce. " Idan babu damuwa zan sa a kira mini wa ansu muhimman bayin Allah domin a kawo arshen komai suma wa annan mutanen su fara rayuwa irin ta mutane ba ta dabbobi ba." "Kar ka kuskura ka tara mini jama'a idan ba haka ba wallahi sai ranka ya aci, fushina mai tsananj zai sauka a kanka." Dattijo Maharaz bai bi ta kanta ba, ya ambato sunan aya daga cikin 'ya'yansa sannan ya ba shi umarnin gayyato masa Babban Malami, jin haka ya sa Sarki Abdul'aziz ya ce idan babu damuwa a taho da Alaramma wato shugaban limaman garin Huddam. Sai da Dattijo Maharaz ya garga ansa Shu'aibu da ya bi ta sigar da Alaramma zai fahimce shi don kar ya tsora da shi sannan ya sallame shi, yana garga insa da kada ya ata lokaci. Waigawa ya yi wurin mutanen da suka yi tsaye carko-carko ya ce, "Shin kun ta a jin labarin wani addinin bayan wannan da kuke bautawa." Hayaniya ce ta an kaure wasu sun amsa masa wasu kuma suka nuna alubalantarsa don sun lura yana son wulan anta abar bautarsu ne a gabansu. "Da da ewa na ta a jin labarin addinin bautar wuta, bautar gumaka, bautar ruwa sai kuma wani addini wai musulunci. Amma shi a wurin masu kawo mana aikin asiri muke jin sa." Wani tsoho ya yi wa Dattijo Maharaz bayani, murmushi ya yi sannan ya furta. "Tabbas Addinin musulunci shi ne addinin gaskiya wanda kowanne bawa idan ya bi shi zai kai shi har cikin aljannah. Wannan abar bautar taku ita kanta hallitar Allah ce, jinsina ce wato jinsin Aljanu. Ko a yanzu idan na so aiwatar da abin da take yi muku nan take zan gudanar muku da shi, tana wasa da hankalanku ne amma ga wanda bai aminta da abin da nake fa a muku ba ya zuba idanu zai ku ga ikon Allah." Rufe bakin Dattijo Maharaz sai ga