← Book details Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 89

Sashe 53

Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zuwa wurin za en da Fulani Umaima za ta yi haka kawai ta ji ba ta son zuwa, don ba aramin tsanar matar ta yi ba, jin hayaniyar za ta takura mata ya sa ta sake ficewa daga akin kai tsaye ta wuce kogin tsamiya ta zauna tana wasa da ruwa. Tun tana cikin damuwa har damuwar tata ta yaye sakamakon yadda ruwan yake riki e mata yana wani irin tsiri kamar zai rufe ta sai kuma ya tafi da gudu ya sake dawowa, ta jima a bakin ruwan har sai da ta gaji don kanta sannan ta bar wurin. Har za ta koma sashensu na Bayi sai ta yanke shawarar zuwa ta gano halin da Abubakar yake ciki duk da ta san Mai gado ba za ta bar ta shiga wurinsa ba. Tamkar dirar mikiya haka Jawahir ta ci karo da shi a mararrabar ofofin da suke tsakanin sashen Fulani Umaima da Fulani babba, yadda ta ga ya yi saranda kamar mutum-mutum ne ya sa ita ma ta daskare cikin fa uwar gaba. A wannan karon bai matso kusa da ita ba sai ma murmushi ya sakar mata, mamaki ne arara ya bayyana a saman fuskarta. "Barka... da hutawa... ranka shi da e." Jawahir ta yi arfin yin maganar muryarta na rawa. "Me ya sa kike jin tsorona?" Yarima Muhsin ya wurga mata tambaya a madadin ya amsa mata. "Amm... dama... dama... ha uri zan baka..." Tun da ta fara magana ya kafe bakinta da kallo haka kawai ya ji irjinsa na bugawa, sha'awa da soyayyarta na fisgarsa. "Laifin me kika yi mini da za ki ba ni ha uri?" ila fa ya manta abin kika yi masa, indai kuwa ya manta ki rufa wa kanki asiri ki yi shiru." Zuciyarta ta raya mata. Tana shirin yin magana ta ji motsin tafiya a bayanta, wani irin turare mara da i ya bugi hancinta. Da sauri ta juya karaf idanuwanta suka sauka a kan Fulani Umaima da ke tafe fuska a ha e Bayinta biyu na biye da ita a baya. "Keee! Ke idanuwana suke gani?" Fulani Umaima ta yi maganar cikin su utar baki sakamakon rashin tsammanin ganin Jawahir. Tsoron Jawahir ya ninku a angare aya kuma haushin Fulani Umaima ya turni e ta. Tamkar ba za ta gaida Fulani ba haka Jawahir ta zuba mata manyan idanunta, idan ba gizo idanun Fulani Umaima suke yi mata ba har gani wayar idon Jawahir tana riki e mata zuwa wata siffar daban. "Barka da hutawa ranki shi da e." Kalaman Jawahir suka daki majiyar sautin Fulani Umaima. Sai da Fulani Umaima ta waiga ta sallami Bayinta sannan ya juya wurin Jawahir tana shirin yin magana Yarima Muhsin ya katse ta. "Ammi dama kin santa ne?" "Ku biyo ni ciki yanzu-yanzu." Fulani Umaima ta furta, tana gama maganar ta shiga cikin gida. Rass! Gaban Jawahir ya fa i don haka ta ji ba ta aminta da kiran da Fulani Umaima ta yi mata ba, tun da ta san babu wani abu da ya ta a ha a su ballanata ta ce ko wani kuskure ta yi mata. "Mu je ciki." Ta riski kalaman Yarima Muhsin cikin tattausan lafazi. Kamar kazar da wai ya fashe wa a ciki haka Jawahir ta shiga sashen Fulani Umaima tana tafe tana arewa sashen kallo, duk taku aya idan ta yi haka take jin bugun irjinta yana tsananta har suka shiga rumfar (Falo) Fulani Umaima. "Ammi ashe ke ma kin santa? Amma na jima ina wahalar da rayuwata." Yarima Muhsin ya yi maganar cike da shau in farinciki. "Wace ce ita?" Fulani Umaima ta tambaya shi fuska babu walwa, ta wurga wa Jawahir wani antaccan kallo cike da tsana. "Ita ce farincikin zuciyata da nake kwana nake ta shi da begenta, ita ce ta ja linzamin dokin zuciyata har nake jin babu sauran wata 'ya mace da za ta samu fada a wurina. Ita in ta musamman ce zinariya ce, tauraruwa kuma hasken zuciya. Ammi wannan ita ce yarinyar da na fa a tarkon aunarta ba tare da na sani ba..." A zabure Fulani Umaima ta mi e tsaye jikinta na karkarwa ta katse shi. "Wannan yarinyar?" Da wani irin sauri ya ji afarsa na fisgarsa zuwa sashen Sarki Abdul'aziz, amma zuciyarsa na garga in kada ya je ya aikata aikin da kan iya kai shi ga fuskantar mummunan hukunci. Amma kuma ya gagara sanin yadda zai dakatar da yanayin da yake ji don har jin sa yake tamkar yana tafiya a saman iska. A lokacin da ya arasa sashen Sarki Abdul'aziz shiru wurin, da yake da alama babu Dogarawan ofa, daga can gefen sashen lambu ya hangi masu hidimar wurin suna gyara ananun shukokin da ke wurin dangin su: Karas, ata, salak da sauransu. Bai tsaya buga ofa ko neman izini ba kai tsaye ya fa a turakar Sarki Abdul'aziz, a lokacin yana kwance da alama hutawa yake. Ganin Kamalu ya shiga akin ya sa Sarki Abdul'aziz tashi zaune da sauri cike da mamaki. "Waye yake yun urin nuna mana rashin a'a zai tako har makwancinmu muna hutawa. Bukar! Bukar!" Sarki Abdul'aziz ya kira shigaban Dogaran da ke kula da sashensa amma shiru babu amsa. Ganin Kamalu ya doshin uwar akinsa ya sa Sarki Abdul'aziz ya rufa masa baya, Kamalu na shiga akin ya ji kansa na juya masa. Ta ama da izzar mulki suka mamaye shi, cikin takun isa da asaita ya tunkari da an gidan tururuwar da ke kallon shurin cikin aki ya ora butar a saman gidan tururwar. Daga gefensa ya ji an furta. "Yau Kamalu ne har cikin zuri'ata? Lallai da alama gaggarumin al'amari zai faru, sai dai ina jimamin da wannan ziyarar ba wurina ka kawo ta ba." Da mamaki Kamalu ya kalli Dattijo Maharaz ya furta. "Dattijo Maharaz kai nake gani." Kafin Dattijo Maharaz ya ba shi amsa Sarki Abdul'aziz ya arasa bakin ofar ya furta. "Wane ne kai? Me ya kawo ka har cikin turakarmu kuma me kake yi a wurin nan?" *SHU'UMAR MASARAUTA* *28* *Littafin ku i ne 500 idan kina bu ata za ki biya ta wannan Account in Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.* Boka Shaddas na daga gefe ya zuba wa Basiru ido ganin yadda yake gudanar da al aluman tsafi, zuciyarsa ce ta yi fes farin ciki ya mamaye shi don ko a yanzu ya mutu ya san ya bar wa duniya magajinsa. A bakin wata atuwar tukunyar asa yake zaune ya ebo wasu turarrika ya zuba sannan ya ci gaba da surutai yana ambatar sunan A'ishatu, Nura, Bala da Nasiru, ta gefensa Boka Shaddas ya zaune ya yi masa jinjina da hannu. "Aikin matar jiya kake yi ne?" Sai da Basiru ya gama jero sunanyen ba en aljanun da ya tura wa anda za su yi masa aiki sannan ya furta. "Aikin jiya na riga da na zartar da shi, a yanzu haka ina gudanar da aikin Hansatu wacce ta kawo aikin 'yayan mijinta da ta ce a haukatar da biyu, aya kuma a zaunar da shi ta arshen a saka mata ba in jini. Shi kuma Uban na mallake mata shi, na tura musu aljani Zurgungu shi zai gama aiwatar da komai. Na yi masa tuwkwicin jinin jariri sabuwar haihuwa da ba en jakuna, bayan wannan ina tunanin na gama da aikina na yau." Murmushi Boka Shaddas ya yi ya dafa kafa ar Basiru, "Fiye da haka na san za ka aikata domin ina ji a jikina sai ka fi ni gawurta da shahara a harkar tsafi da sihiri. Amma ba ka tunanin Mahaifiyarka za ta shiga damuwar rashin ganinka har tsawon wa annan kwanakin ba ka le a wurinta ba?" Shiru Basiru ya yi kamar mai nazari sannan ya furta. "Zamana a wurin nan shi ya fi mini alfanu domin tun wankan tsafin da ka yi mini a duk lokacin da na kalle ta sha'awarta mamaye ni take yi, kuma na san ba za ta ba ni dama ba kuma idan na neme ta ta yi yun urin hana ni zan iya illatata ko ma na hallakata gaba aya. Babban burina aya ne ya rage mini a duniya wanda ba tun yau ba nake mafarkin samu kuma nake haramar yun urin cim masa." "Wanne irin buri ne?" Boka Shaddas ya yi saurin tambayarsa. "Masarautar Huddam! Babban burina bai wuce na mallake ta ba ta dawo ashin ikona, masarautar da ta gawurta da asaitattun aljanu ita nake so ta riki e zuwa Masarautar Matsafan da babu kamarta a fa im duniya. Burin Mahaifiyata Muhsin ya gaji Takawa, ni kuma burina ka samu nasarar kammala karanta labarin Hidaya don ka samu nasarar da za ta kai ka gaba har ni ma na mulki nahiya da yankin da nake so." urrr Boka Shaddas ya yi wa Basiru yana auna kalamansa, bai tanka masa ba ya tashi ya je bakin wani rami ya fara motsa baki. Take littafin ya fara tutsowa daga ashin asa ya fito. Da mamaki Yarima Muhsin yake bin Fulani Umaima da kallo ganin yanayin da ta yi maganar. "Ammi wai me yake faruwa..." Tun bai rufe baki ba Fulani Umaima ta auke fuskarsa da mari, tuni Jawahir ta matsa can jikin bango jiki na rawa. "Wai me yake damunki ne Ammi a kan me za ki mare ni don na gaya miki abin da yake cikin raina." Yarima Muhsin ya yi maganar a ufule tamkar zai rama marin da mahaifiyarsa ta yi masa. Fulani Umaima ta wurgawa Jawahir mugun kallo tana sake tuno tone butar da ta yi mata, wata irin zuciya ce ta ciyo ta don haka ta yi kukan kura za ta janyo Jawahir ganin haka ya sa Jawahir ta fita da gudu tana kwalla ihu cikin tashin hankali. "Me kike yi ne haka Ammi?" Muhsin ya furta cikin araji. "Wannan yarinyar annamimiya ce, ma iyyarmu ce Muhsin ka fita daga harkar yarinyar nan..." "Ki furta mini komai amma ban da kalmar rabuwa don wallahi ko Takawa bai isa ya hana ni aurenta ba, ke kin auri wanda kike so don haka babu ruwanki da rayuwata ni ma ki bar ni na yi sabgar gabana kawai, duk wata damuwa matsalarki ce." Yarima Muhsin ya arasa maganar yana
Chapter 53 · 0% Book details