← Book details Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 89

Sashe 62

Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da an aljan ban san ta ina zai fara ba, ka dube ni komai ya are ya tsumbure." Rai a ha e Shugaba Zurufu ya ce. "Na rantse da gawurtar tsafin da ke cikin dajin nan da muka gada tun iyaye da kakanni idan kika sake magana sai na shafe ki Jakadiya. Ki fice ki ba mu wuri don yanzu haka Buguzu yana can yana amsar horo daga wurin Kabdu." Jakadiya ba ta sake furta koda kalma aya ba, sai kuka da ta saje rushewa da shi ta fice daga cikin tsibirin don rabonta da shar ar kuka kamar wannan tun mutuwar marigayin mijinta. Tun da Dattijo Maharaz ya fara magana Fulani Umaima ta yi wata irin zabura, cikinta ya yi wata irin mur a wani irin zazzafan gumi ya fara keto mata. "Me... kake fa a... ne? Wai ma... waye.. kai?" Fulani Umaima ta yi maganar cikin in'i'na. "Ranka shi da e me wannan tsohon yake fa a ne? An ya ba mahaukaci ba ne..." Tun Muhsin bai gama magana ba Sarki Abdul'aziz ya sauke masa yatsu biyar a fuska. "Idan kuka nemi ku kawo mana rashin a'a ranku zai yi mummunan aci." Ilahirin mutanen da ke wurin jikinsu sanyi ya yi, hatta Abubakar ganin haka sai da ya sa shi ya fashe da kuka yana janye jikinsa daga Sarki Abdul'aziz don gani yake tamkar shi ma zai hukunta shi. A jikin Kamalu ya kwanta, ya saka hannuwa biyu ya ri e shi yana cusa kansa a jikinsa. "Wannan da kuka gani ba iya kaka na auke shi ba, na auke shi jini da tsokar jikina. Ina matu ar girmama shi har ban san yadda zan fasalta girma da matsayinsa ba. Ba kai ba ko mahaifiyarka ba ta isa ta furta magana marar da i a kansa ba." A wannan karon tuni Fulani Umaima ta yi fu ai-fur ai, ban da goge gumi babu abin take yi. "Dattijo Maharaz kalamanka na shirin kawo ru ani a cikin iyalina, ban fahimci abin da kake nufi ba." "A allah na yi zamani da mahaifin kakanka Abdul'aziz, a zubi da tsarina ka san ni ba yaro bane. Ina da zuri'a ina da 'ya'ya da tarin jikoki, idan na furta wa anan kalaman don na kawo ru ani ko tashin hankali a tsakaninka da iyalanka shin wacce riba zan ci? Ka na tunanin zan furta maka arya ne Sarki Abdul'aziz?" Kunya ce ta lullu e Sarki Abdul'aziz da jin kalaman Dartijo Maharaz, ba tun yau ba ya kan ji ana cewa wasu daga cikin jinsin Aljanu sun iya sharara arya musamman idan suka fahimci mutum yana anfani da abin da suke fa a. Amma a wannan fannin zai iya bugar irji a ko ina ya tsame Dattijo Maharaz daga cikin wa anda ake wa kallon ma aryata. "Ba haka nake nufi ba Dattijo Maharaz, ina fatan za ka yi mini kyakkayawar fahimta farin jakada. Duk magidancin da ya tsinci irin wa annan kalaman a kan iyalansa dole zai samu shakku da shiga ru ani Dattijo Maharaz." Murmushi Dattijo Maharaz ya saki sannan ya furta. "Na fahimci kalamanka Sarki Abdul'aziz amma ka san bahaushe yakan ce dole gya a ta yi mai idan ta i ta sha matsa, ka matsa matarka iya bakin arinka na tabbata za ta fito da duk bayanan da kake bu ata. Idan kuma hagu ta i sai a koma dama amma kuma kafin wannan wa a a bakin mai ita ai tafi da in sauraro." Sarki Abdul'azizi juyar da kansa ya yi yana kallon Fulani Umaima da ita ka ai take ta zabga uban gumi. "Ya aka yi yaron nan ya zama ana alhalin ban san da haihuwarsa ba? Wace ce mahaifiyarsa? Kuma ya aka yi ban san da ciki da haihuwarsa ba? Ba yau nake tare da Dattijo Maharaz ba na tabbata ko wanina ba zai yi wa arya ba ballantana ni da zuri'ata." Sarki Abdul'aziz ya yi maganar yana tsare Umaima da idanu. "Ba ni da aya daga cikin amsoshin tambayoyin da kake tuhuma ta a kai. Me ya sa haka Ranka shi da e? Me ya sa sai ni za a tuhuma da irin wannan maganganun alhalin ba ni ka ai ce iyalinka ba?" Fulani Umaima ta yi maganar cikin nuna dakiya da warin gwiwa. "Umaima!" Sarki Abdul'aziz ta ambata da wata irin muryar da ba su ta a jin ya yi magana da ita ba saboda tsananin acin rai. "Wane ne yaron nan?" "Ban san shi ba" "Idan ba ki san shi ba ai kin san Boka Bamaguje ko?" Dattijo Maharaz ya wurga mata tambaya. A razane Fulani Umaima ta dubi Dattijo Maharaz a fili cikinta ya ba da sautin uuuu! Har sai da Yarima Muhsin da Sailuba suka bi ta da kallo. Boka Shaddas sai da ya jima da fita sannan Basiru ya mi e zuciyarsa al ya fara takawa har ya isa bakin ramin da mahaifinsa yake oye littafin, sai da ya gudanar da duk wani abin da mahaifinsa yake yi na tsaface-tsaface kafin ya auko littafin sannan littafin ya fara tutsowa daga asa. Sai da ya gama fitowa ya saka hannu ya auka ya yace da wata mahaukaciyar dariya, ya jima yana yin mai isarsa sannan ya auki wata farar takarda ya ajiye ta a asa ya sa sandar tsafinsa ya bugi farar takardar nan take takardar ta riki e zuwa surar littafin da ya auke daga cikin wurin. Rungume littafin ya yi a irjinsa babu jimawa ya ji wani abu aaau tamkar ya harbi zuciyarsa, da sauri ya ago littafin yana are wa bangon littafin kallo sai ya sake mayar da shi irjinsa ya rungume da hannunsa aya. Har ya je ofar fita daga kogon dutsen sai ya hangi wani kurtun giya, ya auko shi ya aga kansa ya aka sannan ya fice kai tsaye ya nufi cikin Masarautar Huddam. Jakadiya tun da ta koma akinta ta shiga sa a da warwarar makomar rayuwarta, a ganinta wannan karon tonen kaza da ke iya kaita ta tono wu ar yanka kanta ce ya fa o kanta. Da farko ta karaya sosai, amma da wani tsagin zuciyar tata ya hararo mata irin cin zarafin da za ta yi wa Fulani Umaima kuma Sailubanta ta warke sai wata irin warin gwiwa ya ratsa ta. Mi ewa ta yi ta auki garin maganin da Shugaba Zurufu ya bata, ta juye shi a cikin warya ta tu e kayanta sai da ta kullo ofar akinta sannan ta fara fa in wa ansu sunaye tana yi tana watsa ruwan ajikinta sannan ta yi turaren sihirin da ya bata. Tana gamawa kuma fargabarta ta koma kan hanyar da ta samu damar ganin Basiru, don ita sai a lokacin ma ta ga wawtarta saboda a ebe ta haure sama da kwana biyar ba ta saka shi a cikin idanunta ba. "Ki je sashensa mana!" Tsagin zuciyarta ya ba ta amsa. "Wata ila ma idan kika samu damar kai masa Basiru yau ya fasa ha a ki da an autan aljanin da zai turmushe ki." Zuciyarta ta sake raya mata. A gurguje ta saka kayanta ko garin maganin jikinta bai gama bushewa ba ta fice daga akinta, kai tsaye ta wuce sashen Fulani Umaima sakamakon soronsu aya sai dai angaren su Yarima Muhsin daban na Fulani Umaima daban. Tun daga bakin ofa Jakadiya ta fara jin wa ansu irin surutan Basiru har sai da tsora ta, le awa ta yi ta windo ta hango shi yana birgima duk ya ata jikinsa da aman giyar da ya sha, a gefe aya kuma littafin da ya auko yana ri e a hannunsa na hagu. Da sauri Jakadiya ta fa akin jikinta har rawa yake ta tsugunna a gabansa, "Barka da hutawa Saraki!" Jakadiya ta furta don ta ga irin yanayin amsar da zai ba ta. "Ki... tafi ni na... gama da sh... na... auke masa... littafin... tsafi ya... ba ni... dama..." A fili Jakadiya ta saki murmushi ta ri o hannunsa da arfin gaske sannan furta. "Zuruful-Bukusu Barduku kass." Sai da ta furta haka sau uku sannan suka ace daga wurin, suka bu i ido a cikin kogon dutsen Shugaba zurufu. Da matsanancin mamaki Shugaba Zurufu yake bin Jakadiya da kallo, mi ewa ya yi jiki na makyarkyata ya arasa gaban Basiru sannan ya auke littafin da ke hannunsa. A lokacin da zai auke littafin har sai da Basiru ya ago da sauri, Shugaba Zurufu ya hura masa sihirtacciyar iska, take Basiru ya fa i gefe guda jikinsa ya yi wani irin laushi yana numfashi ka an-ka an. "Kin cika jajirtacciya Jakadiya, don haka ya zame mini dole na biya miki bu atarki." Al'amuran da ke faruwa ba aramin dagula wa Kamalu kwanya suka yi ba, tun tasowar shi sam ba shi da son hatsaniya ko tashin hankali don haka ya mi e tsaye ya furta, "Dattijo Maharaz ni dai zan je wurin Baffajo, ka gafarce Ranka shi da e idan har na yi kuskure a kalamaina." Kamalu ya arasa maganar yana russuna wa Sarki Abdul'aziz. Tausayin Kamalu ya kama Dattijo Maharaz, idanunsa suka ciko da walla sannan ya furta. "Tun da kake ba ka ta a jin uminsa ba, ba ka ta a jin gatan da kowanne mai uba yake ji ba musamman da ka kasance asalin mai gata gaba da baya. Don Allah Abdul'aziz ka rungume yaron nan ko ya ji abin da sauran 'ya'ya suke ji." Tun ba rufe baki ba Sarki Abdul'aziz ya ri o hannunsa, Kamalu sororo ya yi yana jinjina taushin hannun Takawa sa anin na shi da ya saba da wahala da yake tamkar katako saboda tauri. Mamakinsa ya ninku da ya sake jin Takawa ya rungume shi tsam a jikinsa. "Wai yau nine a tare da Mai martaba ko idanuwana da gangar jikina ne suke yaudarata? Ya Allah idan mafarki nake yi kada ka farkar da ni yanzu domin na ji irin ni'imar da masu mulki suke ji a rayuwarsu." Kamalu ya yi maganar a hankali, a tsammaninsa a cikin zuciyarsa ya yi ta. "Ba mafarki kake yi ba Kamalu, idan kuma kana tantama yanzu ne za ka tabbbatar da haka." Dattaji Maharaz ya furta yana nuna bangon akin Sarki Abdul'aziz. "Ya kai Dattijo Maharaz shin me ye dalilinka na yi mini kutse a
Chapter 62 · 0% Book details