Sashe 55
Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tana shirin yin magana Bamaguje ya dafa kanta nan take suka ace, sai ga su a cikin kogon dutsen Shugaba Zurufu da har wannan lokacin shi yake shugabantar Al'ummar mutanen Rumzu. Saboda matsanancin gudun da Jawahir take yi ko kallon gabanta ba ta iya yi, babban burinta bai wuce ta ganta a sashensu na Bayi ba ko don ta ceci kanta. Bayan fitowar Muhsin da sauri ya rufa mata baya, duk inda suka wuce ban da idanu babu abin da ake zura musu wasu kuwa tuni suka fara tsegungumi. Mafi yawa daga cikinsu tsammanin da suke yi Jawahir ta yi wa Muhsin babban laifin don haka yake bin ta zai hukuntata. Kafin wani lokaci tuni Bayi suka ci gaba da kacalcala maganar, masu arfin halin ciki suka rufa wa Muhsin baya don gano wal uwar dakan abin da zai faru. Da matsanancin gudu ta fa akinsu kai tsaye kan gado ta haye jikinta ban da karkarwa babu abin da yake yi, a bakin ofar akin ya tsaya yana are mata kallo nan take ya ji tausayinta ya kama shi. A hankali ya fara takawa har zuwa bakin gadon, jin motsinsa ya sa Jawahir ta ago irjinta na bugawa. Kafe ta ya yi da kallo don sura da irarta ba aramin fisgar hankalinsa suke ba, hannunsa ya kai kan fuskarta yana shirin yin magana ya ji wani irin aaauuu tamkar wutar lantarki ta ja shi. Yarfe hannu ya shiga yi yana kai wayar idonsa ya ga an yatsan da ya ta a ta ya yi ba i wuluk. "Ki yi ha uri a kan abin da mahaifiyata ta yi miki." Muhsin ya furta a sanyaye sannan ya juya ya fice daga akin. "Kamar yadda Maharaz ya sanar da kai sunana Furhussam, ina fatan za ka kasance mai adalci a gare mu bayan sauraron kowanne angaren. Wannan yaron tun a ranar da ya zo duniya rainonsa cakokam ya dawo hannuna da iyalina, idan ban manta ba kusan kimanin shekara ashirin da oriya kenan. Wata rana da doshin asuba wata yarinyar ta dire shi a kujerar da na dam awa babbar jikata ta wurin 'yata da na fi so a duniya wato Hullat. Tun lokacin da Hullat take da cikin yarinyar na yi mata al warin mallaka mata ragama da shugabancin da na ke kai, kwatsam a daidai ga ar da na tashi domin a ora jaririyar sabuwar haihuwar sai kuma na riski Kamalu a lokacin da yake jariri a kwance ko igon sutura babu ajikinsa. A a'idar masarauta da kujerar mulkin da nake kai ba kowanne jariri ne ake ora shi a kujerar ta yi daidai da shi ba sai mai tsananin rabo, sau tari wasu jariran ma ana ora su suke mutuwa ko su kamu da matsananciyar jinya. Kuma matu ar ka hau kanta ka zama jagora mai aiwatar da duk wani hukuncin da ya dace, a lokacin da haka ta faru na ji ba inciki sosai har sai da na ji tamkar na kashe Jaririn amma sai na fasa, a kan dole na na a masa kambu a kansa wanda a zahirin Baffajon da ya tsince shi ya ga zagayayyan jini da tururwa a goshinsa. 'Yata Hullat da kanta ta ba ni shawarar na aura wa Kamalu da Fartuhmu aure, saboda yadda kyakkyawar surarsa ta birge ta don haka take fatan yarta ta aure shi. Ba zan oye maka ba a siffar hallita da ira nesa ba kusa ba jinsinku na mutane sun fi mu kyau, dalilin haka yake sa muke auren matayenku da dama don ko ni ina da matan bil'adama sun kai goma. Ta farko na aure ta ne silar rashin wankan tsarkin da ba ta yi yadda ya kamata sakamakon na ta a wucewa na ji Malam Liman yana yi wa su Dattijo nasiha a kan kyautata wankan jinin al'ada da na haihuwa kai har ma da wankan najasa. Ta biyun na aure ta ne saboda yadda nake ganin tana wanka a ban aki babu addu'a sai surarta ta matu ar jan hankalina, kuma har yau ta gagara samun mijin aure kai duk wani haske da taurarinta na dasashe su ko saurayo ba ta yi. Ta ukun kuma na aure ta ne saboda kwanciya baccin dare da take yi babu addu'a kai babu ankwali ita kuma na bar ta ta yi auren amma kuma haihuwa ce na i barinta ta yi sai yawan ari da nake saka ta. Kasan dalili Abdul'aziz?" Cike za uwa Sarki Abdul'aziz ya furta. "Sai ka fa a Sarki Furhussam." *SHU'UMAR MASARAUTA* *29* *Littafin ku i ne 500 idan kina bu ata za ki biya ta wannan Account in Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.* Murmushi Basiru ya saki sakamakon gano sirrin yadda mahaifinsa ya oye littafin da yadda ake fito da shi. Sai kuma yadda shi kansa a nan gaba ba zai sha wahalar sace shi a ruwan sanyi ba, Boka Shaddas ya auko littafin ya koma kusa da Basiru ya zauna. "Ina matu aunarka Shaddas babban burina bai wuce na ga ka zama gawurtaccan bokan da har duniya ta tashi ba za a ta a mantawa da shi ba, zan mallaka maka duka arfin tsafina domin kai ka ai ne jinina da ke yawo a doron asa." "Na ji da in wannan sadaukarwar taka mahaifina Boka Bawa, tukwicin da zan yi maka bai wuce na hallaka ka ba domin amfaninka ya are a wurina. Tun ban kai shekara goma ba nake saka ido don na gano sirrin da zan kwashe duka sirrin tsafinka, amma sai yau hakan ta kasance. Ina yi maka kyakkayawan fata da kwanciya mai kyau a rayuwarka ta barzahu." Kalaman Boka Shaddas da na mahaifinsa na baya suka dawo cikin kunnuwansa tamkar a lokacin suke tattauna su, a ga ar da mahaifinsa ya mallaka masa arfin tsafinsa shi kuma ya hallaka shi. Shi kansa yana son mallaka wa Basiru halwar tsafinsa amma yana tsoron kada nan take Basirun ya hallaka shi, murmushi ya sakar wa Basiru suna ha a ido ya furta. "Ban ta a sanin haka a yake da da i ba sai yanzu da na mallake ka, kafin kai na mallaki 'ya'ya biyu amma ban ta a jin aunarsu kamar kai ba. Basiru ya sakar masa murmushi sannan ya furta. "Da sannu zan auke littafin nan na hallakaka domin na mallaki duk wata aukaka da ke ta ama da ita." Basiru ya raya a zuciyarsa amma a fili sai ya furta. "Ba na ganin amfanin karanta wannan labarin, me zai hana mu je kai tsaye da aiwatar da abin da ya kamata." Basiru ya arasa maganar yana zura wa Mahaifinsa da wa-da wan idanunsa. "Tabbas har yanzu da sauranka a halwar tsafi Basiru, babban amfaninsa ga duk wanda ya wallafa rai a kansa dole ne ya karanta labarin nan. Kada ka zama mai gaggawa a harkar tsafi da sihiri domin ba zai ta a haifar maka da a mai ido ba, kada ka nemi shahara da aukaka idan har ba ka zama gwani a harkar ba." Basiru ya sake zuba wa Boka Shaddas na mujiya yana wani nazari daban, Boka Shaddas bai sake magana ba ya bu o wurin da ya tsaya duk da shi kansa ba da in jin karatunsa yake ba, tun da ba daga farko ya fara karantawa ba amma babu yadda ya iya tun da idan ya ce zai karanta daga farko zai matu ata lokaci. Sarki Hafiz shiru ya yi yana kallona da alama tambayoyina ne suka yi yun urin daskarar da shi, ya auki lokaci a haka sannan ya furta mini. "Gaba aya ban san ta yadda aka haihu a ragaya ba amma idan kika bi ni a sannu zan warware miki zare da abawa, abu aya na sani mahaifiyarki ta sha wuya matu a kuma ta galabaita. Soyayya ta yi tasiri a rayuwarta kuma ita ce tsanin da ta kai ta ga halin da ta tsinci kanta a ciki." Ajiyar zuciya na sauke a fili cike da jinjina kai cike da damuwa, haka kawai na ji takaicin Aljanin da ya ulla soyayya da mahaifiyata. "Tun ranar da aka aura auren mahaifinki da mahaifiyarki suka fara fuskantar matsaloli ta angarori da dama, domin a labarin da kakana ya bani ya ce shi an autan Darri ne yake saka mahaifiyarki yin abubuwa da dama ba tare da ta sani ba. Kuma tsananin soyayyar da mahaifinki yake yi mata ya sa duk wani cin kashi da mahaifiyarki za ta yi masa ba ya yin fushi ko ya auki mataki. Sun shafe shekaru da dama a cikin zaman doya da manja ba tare da wata kyakkyawar ala a a tsakaninsu ba, kuma a wannan lokacin aka na a wa mahaifinki saraurar Masarautar nan bayan rasuwar Mahaifinsa. Da yin bikin na in Mahaifinki ko wata guda ba a rufa ba ya yi murabus ya dam a wa mahaifiyarki ragamar mulkin gaba aya, a wannan lokacin ne mahaifiyarki ta kafa tarihi domin ita ce mace ta farko da ta fara zama Sarauniya a masarautar nan. A wannan lokacin sai mahaifinki ya samu kan mahaifiyarki har ta an fara ba shi kulawa, dalilin haka ya sa ya sake sakankancewa a soyayyarta. Kwatsan sai aka wayi gari mahaifiyarki ta samu ciki, tun da ta samu ciki yake wahalar da ita arshe sai arinsa ta yi. Kakana ya ba ni labarin tun daga wannan lokacin sai ciki ya i zama a jikin mahaifiyarki, ashe abin da ba a sani ba a bayan fage an auran Darri ne yake arar da cikin a duk lokacin da ta same shi. Tafiya ta ci gaba da tafiya har mahaifiyarki ta sake komawa 'yar gidan jiya sakamakon ashe a oye an autan Darri ne yake kanainaye ta da da an kalamai har ya yi nasara a kanta, kwatsam babu zato sai aka wayi gari Mahaifiyarki ta yi murabus daga kan karagarta ta dam a masa. A wannan lokacin an ce ran mahaifinki ba aramin aci ya yi ba har sai da ya aurace mata na tsawon makwanni, ita kuma abin da Mahaifiyarki ba ta sani ba an autan Darri yana mata fadanci ne domin ya o wa masoyayiyarsa karagar masarautar nan ne. Kin san wace ce Masoyiyar an autan darri?" Na