← Book details Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 89

Sashe 59

Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tunanin halin da yake ciki, wani lokacin har zubar da walla take yi. Wannan ne karo na farko da Jawahir ta ji ba za ta sake biyewa umarnin matar da ke zuwar mata a mafarki ba koda za ta hallaka. Hatta Mai gado sai da ta fahimci halin damuwar da Jawahir take ciki don haka ta tsare ta da tambaya. "Jawahir wani abu yana damunki ne? Ko mafarki kika sake yi da matar nan?" "Inna ina tunanin halin da Kamalu yake ciki ne! Ko ya mutu ko yana raye Allah ne masani." Jawahir ta arasa maganar kamar za ta yi kuka. "Addu'a ita za mu ci gaba da yi, idan muna nuna karayarmu a fili za mu sake raunata zuciyar Inna wuro don haka kika ga a kullin nake sake arfafar gwiwarta." Lokacin da Muhsin ya gama shan furar wurin Jakadiya tana fita bacci ya yi awon gaba da shi, ya jima yana bacci har bayan sallar Isha'i. Bayan ya tashi ya an ji damuwarsa ta ragu don haka ya wuce ya auro alwala ya gabatar da sallolin da suke kansa, zamansa babu jimawa fuskar Jawahir ta ci gaba da dawo masa a hankali murmushi ya su uce masa. Fulani Umaima sai da ta yi wanka ta sake gyara jikinta ta tura aton tsumma asanta domin ya dinga tare ruwan da ke fita daga jikinta, ta rame sosai fuskarta ta yi fayau tamkar wacce ta jima tana jinya. Kai tsaye sashe Muhsin ta nufa a wannan karon ko Baiwa aya ba ta bari ta yi mata rakiya ba, a lokacin da ta je yana zaune zugum cikin damuwa. Da sallama ta shiga sai dai ciki-ciki ya amsa mata ya auke kansa gefe, a kusa da shi ta zauna ta aro murmushin ya e ta furta. "Na zo bikon Sarkin gobe." "Hmmm!' Kawai Muhsin ya ce. "A baya na yi maka mummunar Fahimta ne Yarima, a tsammanina Yarima mai jiran gado tamkarka bai dace da auren Baiwa ba. Amma a yanzu da na fahimci irin soyayyar da kake yi mata na amince ari bisa ari Sarkin gobe, da kaina zan wuce har gaban Takawa domin na yi maka iso a kan neman aurenta." Sai a lokacin Yarima Muhsin ya saki fuskarsa, ya ru o hannun mahaifiyarsa cikin farinciki. "Na ji da warai da kika fahimce ni Ammi! A daren nan kuwa zan yi gaggawar dakatar da Jakadiya tun da kin sauko..." A razane Fulani Umaima ta katse shi. "Wacce Jakadiya? Me za ka dakatar da ita?" *SHU'UMAR MASARAUTA* *31* *Littafin ku i ne 500 idan kina bu ata za ki biya ta wannan Account in Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.* Sarki Sulaiman tare da ma arrabansa cikin farinciki suka koma masarautarsu, tun bai shiga cikin sashensa ba kai tsaye wata ofa ya shiga wacce aka sassa a da zallar farin arfe, sai walwali take tana aukan idanu. Kusan ya zame masa al'ada duk fita idan zai yi ko bayan ya dawo daga wani wuri sai ya shiga cikin wannan ofar. Babban aki ne da aka awata shi da kayan alatun more rayuwa, a tsakiyar akin an sassa a wata atuwar tantamara wacce aka yi mata adon fentin fari da ba i sai wa ansu duwatsu da aka manna mata a jiki. Sai da ya arasa ya sumbace ta sannan ya fito ya fice kai tsaye ya wuce sashensa, da saukarsa babu jimawa aka ha a masa ruwan wanka ya shiga ya gaggasa jikinsa sannan ya zura 'yar shararsa ta shan iska ya bayar da umarni Jakadiya ta kira masa matansa gaba aya kowacce tare da iyalanta. Sun yi matu ar mamakin jin kiran da yake yi musu don haka kowacce zuciyarta cike da wasu-wasin dalilin tarasu ta arasa. Sarki Sulaimanu Matansa Uku da 'ya'ya goma cif, yana da 'ya'ya maza hu u sai 'ya'ya mata guda shida. Uwar gidansa Fulani Habiba tana da 'ya'ya Hu u, uku mata sai namiji aya. Kuma babbar 'yar Sarki Sulaiman mace ce mai suna Raihanatu. Matarsa ta biyu Fulani Sa'adiyya tan da'yaya mata biyu sai 'ya'ya maza biyu, ita kuma Fulani Zabba'atu tana da 'ya'ya biyu duka mata. "Assalamu alaimum. Muna bu atar gaba ayanku ku ba mu hankalanku domin mu sanar da ku abin da yake tafe da mu na alkhari." Sai da ya zayyane musu duk yadda suka yi da Sarki Abdul'aziz sannan ya ci gaba da ce wa, "A yanzu haka ni da Mai martaba mun zartar da lokacin aurensu Raihanatu nan da makwanni hu u masu zuwa cikin yardar Allah. Ina fatan ke Raihanatu ba za ki watsa mini asa a ido ba." Cikin ladabi Raihanatu ta gya a masa kai, farinciki fal zuciyar mahaifiyarta ya oyuwa don babu wanda ba zai so ya ha a zuria'a da masarautar Huddam ba. Sai da suka an ta a hira a tsakaninsa da iyalansa sannan ya sallame su kowacce ta wuce sashenta. Ba inciki ne ya mamaye zuciyar Fulani Sa'adiyya don a ganinta Yarima Muhsin da 'yarta Hansatu ya fi dacewa. Dattiji Maharaz sai da ya duba lungu da sa on cikin dajin amma ko mai kama da jinsin halittar an adam bai gani ba, a galabaice ya zauna a bakin wata bishiya sannan ya fa a duniyar tunani. "Da wacce shaida zan koma na sanar wa Sarki Abdul'aziz? Shi kenan rayuwar Kamalu za ta koma hannun Furhussan da zuri'arsa?" Dattijo Maharaz ya furta a fili. "Sam ba zai ta a yuwa ba." Ya yi maganar yana mi ewa tsaye rai a ace. "Na ji da i har a kullin warin gwiwarka ne yake rinjayar rauninka, kai mai farar zuciya da jin ai ne don haka zan taimaka maka da baiwar da Allah ya hore mini." Dattijo Maharaz ya ji an furta daga bayansa, yana waigawa ya ci karo da Malam Liman. A fili ya bayyana fara'arsa ya arasa wurinsa yana niyyar russunawa ya ago shi. "Kada ka damu Maharaz, babu isasshen lokacin da za mu auka. Zan taimaka maka a wato yaron nan domin shi in ba jininmu ba ne kuma ba jinsin mu ba matu ar aka bar shi a cikinsu an cutar da shi da iyayensa, kuma a kowanne lokaci suna iya sauya masa addini gaba aya." Jinjina kai Dattijo Maharaz ya yi sannan ya shiga zabga wa Malam liman godiya bisa karamcin da yake nuna masa da soyayyar addinin musulunci. "Furhussam ya yi amfani da sirrin tsafi da sihiri, mu kuma sai mu karya shi da addu'o'in kariya daga ayoyin Allah. Ka dafa wannan dutsen da bismillah bayan ka yi alwala kuma ka ambata da ya ini a zuciyarka Ubangiji Shi zai iya aiwatar da komai kuma da taimakonSa za mu samu mu ku uto da wannan yaron." Sun fara tafiya mai nisa Fargi ta dakatar da shi tana share hawayenta sannan ta furta. "Idan zuri'arka sun amince na aure ka na san halin zuri'ata har gaban abada ba za su lamunce na aure ka ba Sulaiman, hasali ma a yanzu matu ar suka ji ala ar da ke tsakaninmu gaba aya hallaka mu za su yi. Ha uri shi ya kamace mu gwarzona, ina ganin dama can tsafina bai bincika mini daidai ba." "Ba zan iya ba Fargi! Ba zan iya rabuwa da ke ba, idan kin lamunce zan kai ki a aura mana aure a oye idan ya so na dawo da ke cikin danginki kafin mu nemarwa kanmu mafita." Shiru Fargi ta yi tana nazartar kalamansa ganin kamar ba za ta amince ba ya sa ya shiga lallashinta da gaya mata da an kalamai har dai Sulaiman ya yi nasara a kanta. Alkyabbar jikinsa ya cire ya rufa mata ya ora ta a kan dokinsa sai da suka yi tafiya mai nisa sannan suka fito cikin gari, tsoro ne arara ya mamaye Fargi sakamakon wannan ne karo na farko da ta ta a tsomo afafuwanta cikin gari ta baro dajin da suke rayuwa. "Ki nutsu Sarauniyata babu abin da zai kama ki, idan kina nuna firgici mutane za su dasa zarginsu a kaina." Sulaiman ya furta mata cikin sigar lallashi bayan ya gama na e fuskarsa domin kada a gane shi. Can bayan garinsu ya wuce da ita ya bu e wani aramin guda mai aki biyu ya saka ta a ciki sannan ya ce mata yana zuwa. Da fitarsa kai tsaye gidan Waziri ya wuce aminin mahaifinsa, takanas ya auko shi sai da ya kawo shi cikin gidan sannan ya zayyane masa duk abin da yake tafe da shi. Zuciyar Waziri al ya amince da bu atar Sarki Sulaiman don a ganinsa nan gaba wannan auren da zai yi ba aramin na asu da damuwa zai kawo masa a harkar mulki ba tun da babu wanda ya san da auren, idan ya so nan gaba ko hayayyafa ta yi yana iya murje idanunsa ya ce bai san zance ba tun da har Mahaifinsa ya iya tsallake 'yarsa Shafa'atu ya aura wa Sulaiman wasu. A wancan lokacin Sulaiman har sai da ya yi wa Fargi tayin addinin musulunci amma fir ta nuna masa ba ta aminta da shi ba, ko da za ta shiga addinin sai zuwa bayan wani lokaci. Sulaiman bai takura mata ba don haka shi da Waziri suka fice daga gidan, a can wani aramin auye Waziri na da wani amini sunansa Kalidu tare da Sulaiman suka tafi garin Waziri ya zayyane masa komai. Malam Khalidu ya amince zai zo a matsayin waliyyin Fargi shi kuma Waziri ya zo a matsayin waliyyin Sulaiman, suka tara mutane a ofar gida aka aura auren Sulaiman da Fargi kamar yadda addinin musulunci ya hukunta. Da an mamaki a fuskar Muhsin yake kallon mahaifiyarsa ganin yadda ta razana lokaci guda. "Ita ta ce mini za ta wuce mini gaba wurin Takawa a kan maganar auren yarinyar." Ajiyar zuciya Fulani Umaima ta sauke a fili tana juya kalamansa a cikin zuciyarta. "Ruwa fa baya ta a tsami banza ni na san akwai manufar Jakadiya a wannan maganar! To ko ta gano neman yarinyar nake yi ruwa a jallo? Da sannu zan fahimci inda ta dosa, don na yi rantsuwa da arfin ikon Bamaguje Jakadiya ba za ta ta a kwaye mini baya ba." Fulani Umaima ta
Chapter 59 · 0% Book details