← Book details Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 89

Sashe 27

Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

nan kuma kuke tafiyar da ita a yadda ta zo muku wannan ma ku auke ta a haka. Ko da wasa har iyalanka kada ka sanar da su wannan mushen San ba daga gare mu ba ne, domin fa ar taka na iya jefa duk mutanen cikin masarautar nan a cikin halaka. Ba ka sani ba ko akwai wanda yake burin mallakarta a cikin masarautar nan, to kuwa muddin ya allo maka ruwa babu makawa sai kun gwammace ki a da karatu." Gwaron numfashi Sarki Abdul'aziz ya sauke sannan ya furta, "Na yi maka al awari ya kai wannan Dattijo mai cikakken karamci." Murmushi Dattijo Maharaz ya yii ya furta. "Na san ba za ka ta a bijire mini ba don haka nake sake godiya da irin girmamawar da kake yi mini. Ina mai yi maka albishir da wani alheri na nan tafe cikin iyalinka, duhu zai yaye sannan haske zai mamaye ka da ahalinka wala'alla ma ya tsamo ka daga wata irin sar iya. Sai dai kuma akwai acin rai, acin ran da ka iya kai ka ga yin nadama a lokacin da nadamar ba za ta yi maka amfani ba." Gaban Sarki Abdul'aziz ya yanke ya fa i, cikin rashin kuzari ya ce. "Wanne irin haske ne wannan da ke iya tsunduma ni cikin nadama...?" "Ba haske ne zai kai ka ga nadama ba, sai dai ulli da mur a-mur ar da ke kanka ce za ta yi tasirin ko kuma silar tafiyarka kan turbar nadama. A arshe ina mai yi maka fatan alheri mai orewa kai da iyalanka, na barka lafiya Sarkin sarakuna." Ko ka an ba haka Takawa ya so ba, ya so a ce ya samu damar sake tattaunawa da Dattijo Maharazu amma babu yadda ya iya haka ya taso daga gaban shurin ya koma kam gadonsa, ya ji ma shi ka ai yana maimaita kalaman da Dattijo Maharaz ya furta masa. Ganin babu wata mafita ya sa ya shiga ban aki ya gabatar da al'awala don gabatar da sallar Isha'i. Bai san dalili ba amma haka kawai wani lokacin yake jin ba ya sha'awar yin salloli a kan lokacinsu, sai ya kai zuciyarsa nesa yake gabatar da su. "Kamar yadda muka al arwarta muku mun tattauna da Dattijo Maharazu har ya kara yi mana fashin ba i." Sarki Abdul'aziz ya yi maganar bayan ya tara fadawa da sauran masu sarautun cikin masarauta. Cike da girmamawa suke jinjin kai sannan ya ci gaba. "Gaba ayanku ba ba i ba ne dangane da wa ansu al'amura da ke faruwa a gidan nan kamar shan nono ranar juma'a, rafin tsamiya, busar sarewar shuri da sauran abubuwan da aka saba gani yau da kullin." Sai da ya an tsahirta ya ci gaba da jawabi. "A don haka su ma wa annan mushen Saniyar na daga mazauna cikin masarautar nan, kuma a tabbatar an garga i talakawa a kan koda wasa kada wani ya yi gangancin aiwatar da wani udiri game da shanun, abu aya aka lamunce a duk ranar da aka yi tozali da su a tabbatar an kawar da su zuwa babban juji kamar yadda ake yi a baya." Surutu ne ya fara tashi sama-sama kowa ya fara tofa albarkacin bakinsa bayan doguwar tattauna Mai martaba ya shiga gida sannan kowa ya kama gabansa. A kullin lamarim larurar Fulani Babba ara ta'azzara take, abin da yake sake aga mata hankali bai wuce yadda fitsarin da take yi ya ci gaba da bibiyarta har ta kai tana yinsa ido biyu, daga baya sai abin ya zame mata tamkar mai yoyon fitsari ba ta aukan wani lokaci mai tsawo sai zanin jikinta ya ji e sharkaf. Da ta ayyana za ta nemi magani game da ciwon ko ta sanar da Sarki Abdul'aziz sai ta ji kanta ya yi nauyi lokaci aya ta manta halin da take ciki, hatta ibada sau tari idan ta yun ura da niyyar gabatar da sallah sai ta fara wasu-wasin sallar Azahar ce za ta yi ko La'asar. Wani lokacin har sai tambayi Bayinta ko su Khadija idan suna kusa da ita, a angare aya kuma duk ranar da muradin mijinta ya bijiro mata na son ewa da shi to ranar haka za ta kwana tana mafarkin Takawa ya zo zai kusance ta ta arfin tsiya kuma duk yun urinta na in amince masa haka zai yi amfani da ita ta arfin tsiya sannan ya ago yana she a mata wata iriyar dariya. Duk ranar da ta yi wanna mafarkin idan ta wayi gari wuni za ta yi wani irin ruwa mai oyi yana ta fita daga jikinta. Abin oye kusan ya fito fili domin kusan duk Bayin masarautar sun fahimci Fulani Babba ba ta da kwana a wurin Mai martaba, sai dai jifa-jifa ya kan neme ta da rana ta je turakarsa su an ta a hira shi ma ba wata hirar kirki suke yi ba. Kusan abin sai ya ha e mata goma da ashirin ga ciwon Abubakar da kullin gaba yake yi ga ita ma nata, domin a wannan lokacin Abubakar bai ciki bambamce tsabar abinci ba da asar da yake rayuwa a cikinta, kowanne ya samu dan arawa cikinsa yake yi. Ya zama tamkar mujiya hatta bayin da ke yi masa hidima a tsorace suna yi masa su kammala, don sau babu adadi yana kama Bayi idan sun shiga bashi abinci ko gyra shi ya ri a cizgar gashin kansu yana cinyewa. Dalilin haka ya sa Dogarawa ke aure shi kafin a shiga akin, hatta su kansu sai sun yi da mugun gaske. A 'yan kwanakin wa ansu irin mafarkai take yi na Abubakar wai yana zaune sai kuma ta ga wani mai tsananin kama da shi ya zo yana jan hannunsa a kan ya mi e su tafi. A mafarkin da ta yi na arshe kafin ya kama hannun Abubakar sai ya isa gare ta ya furta mata. "Me ya sa bakya sona kika bari na yi nisa da ke, ni ma anki ne don Allah ki dawo da ni gare ki." Hawayen idanunta ta share ta furta. "Ta yaya uwa za ta i abin cikinta ina matu aunarka..." Kalamanta suka katse a lokacin da ta ga ya ri o hannu Abubakar ya mi e tsaye tun yana tangal-tangal har ya take afafuwansa, cike da murna ta fara bin su tana wala musu kira amma kafin ta isa sun ace wa ganinta." Firgigit ta farka tana sauke ajiyar zuciya, ta yi mamakin nannauyan baccin da ya yi awon gaba da ita da tsakar rana. Sau tari ta kan yi mafarkin ta haifi tagwayen jariri duka maza, amma da ta tashi aukansu sai ta nemi aya ta rasa. "Barka da tashi uwar gijiyata." Mai gado ta furta da ke gefe zaune a gabanta. "Mai gado na jima ina bacci ko?" "Ranki shi da e ai hutu ne kika samu uwar gijiyata." Fulani babba ta matu ar aminta da Mai gado saboda yanayin ri on amana da rashin kwaramniyarta. Sai da Fulani Babba ta tashi zaune sannan ta tattara hankalinta wuri aya ta furta. "Mai gado wata tambaya gare ni." "Ina sauraronki ranki shi da "Don Allah mace na iya haihuwa ba tare da tana cikin hayyacinta ba har ta manta da abin da ta haifa?" Tafiya suke cikin ba in dajin da ke cike da ban tsoro, firgici da tashin hankali. Kukan tsuntsayen da ke dajin ya isa ya hautsina kwanyar mai tafiya a cikinsa. Bakin wani kogo suka shiga suna tafe suna fa "Mu masu bin umarninka ne sau da afa." Jakadiya ce a gaba sai Fulani Umaima da ke biye da ita har suka arasa bakin wata atuwar rijiya da wani Boka ke zaune a saman ruwanta, a madadin ruwa a cikin rijiyar wuta ce ke ci ganga-ganga. Tsirara yake babu sutura a jikinsa, duk da dare ne amma kogon dutsen a haske yake tarwai kamar rana da wani sihirtaccen haskensa. "Barka da aiki Boka Shaddas, ka yi naka ka yi na kowa duk wanda ya ja da kai ya halaka." Faffa ar fuska gare shi kamar faranti mai auke da aton hancin, jajayen idanu da jan le e. Wata irin dariya ya saki mai kama da kukan jaki." Ku dakata a nan me neman biyan bu atar ita za ta araso." atuwar muryarsa ta e cikin kogon dutsen, jiki na rawa Fulani Umaima ta fara takawa da sauri har ta isa gare shi. "Daga yau za ki daina sallah da wanka tsarki har tsawon shekara guda, ki tabbata duk abin da muka umarce ki za ki aiwatar mana kuma ki sa a ranki bau atarki tamkar ta biya ne." Fulani Umaima ta furta. "Duka na amince, matu ar bu atata za ta biya ko me kake so zan aiwatar da shi." A karo na biyu ya sake sakin dariya mara da in saurare. "Ba ma bu atar tukwicin komai sai na jinin mahaifiyarki, mahaifinki da an cikinki. Sannan kuma dole ne mu lashi zumar jikinki ta hanyar kusanctarki. Matu ar kika aiwatar da wannan ina mai yi miki rantsuwa da sirrin tsafi da sihirina a duniyar nan babu abin da za ki nema a wurin mu ya gagare ki." SHU'UMAR MASARAUTA *MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE* *SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?* *TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN URAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHE I KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI* *SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI
Chapter 27 · 0% Book details