Sashe 11
Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga aukan tsattsauran mataki don haka a kiyaye. SHAFI NA SHIDA Ajiyar zuciya Fulani Umaima ta sauke ta zauna a gefen gado, wani irin gumi ya fara tsattsafo mata. "Binciken da nake kan yi dangane da abin da kike auke da shi a cikin cikinki, na shafe tsawon kwanaki ina bincike har yau na gagara sanin mene ne a ciki. Kullin duhu nake mai auke da rashin alkairi, duhu ne mai auke da tururi da ke one duk wani makusancinsa. Ba ke ka ai ba ni kaina ina da burin sanin me za ki haifa domin amfanar gobena. Ina bu atar Magaji a halwar tsafina Umaima." A razane ta ago tana kallonsa, "Ban gane kalamanka ba Bamaguje, me ye ala ar abin da yake cikina da gadon halwar tsafinka?" Bamaguje ya saki murmushi. "Wannan sirrintaccan sirri ne tsakanina da mahaifiyarki, ba ala ar abin cikinki ya kamata ki tamabaya ba. Amma mu jirayi lokacin kin san ko ba da e ko ba jima akwai lokacin da ya za ta akin anwa." Sallamar Baiwa Salame ta katse Fulani Umaima daga duniyar taunanin abin da suka tattauna da Boka Bamaguje. Ba ta amsa mata ba don haka Baiwar ta koma, Fulani Umaima ta mi e ta ci gaba da kaiwa da kawowa damuwa cunkushe a zuciyarta. Kamar wacce aka tsokara haka ta mi e ta arasa ta auko akwatin sirrinta, ta auko littafin da Bamaguje ya bata. Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta bu e shafin da ta tsaya da karatu. Na jima a tsugunne gaban Uwar Bayi ina tsammanin kalamanta har sai da na fara yanke auna da samun abin da nake bu ata, ba zato na ji muryarta a tsakiyar kaina. "Hidaya labarinki cike yake da almara, al'ajabi da ban mamaki. A tsammanina ni ce mace ta farko da na fara tozali da ke a cikin masarautar nan, ban sani ba ke 'yar cikinta ce ko akasin haka. Abu aya na sani watarana na tafi isar da sa on Fulani Hauwa na gan ki tsaye a jikin bishiyar kukar da ke bayan akunan Bayi kina rusa kuka, gudun kada na yi latti a aiken da aka yi mini ya sa sai da na kai na dawo har lokacin ba ki daina kuka ba. Da yake a ranar an shigo da sababbin Bayi sai na yi tsammanin 'yar aya daga cikinsu ce yawo ya kawo ta nan take kuka ta gaza gane hanya wurin mahaifiyarta. Sai na ri e miki hannu muka wuce sashen Bayi na araci cigiya babu wanda yace 'yarsa ce, to da yake a cikin Bayin da aka kawo akwai wasu mata biyu da suka rasu sai na yi tsammanin mahaifiyarki na aya daga cikinsu. Amma daga baya sai na ga 'yan uwansu suna cewa sam ba tare da su aka kawo ki ba, wannan dalilin ya sa kika ci gaba da zama a sashen Bayi ba tare da iyaye ba." Kalama Uwar Bayi suka zo arshe a daidai lokacin da ni kuma bakin omar idaniyata ta alle, sai da na yi kukana mai isata na dube ta. "Haka zan are rayuwata ba tare da sanin makomata ba." Uwar Bayi ta wara hannuwa. "Abin da na sani ka ai na sanar da ke, idan Allah ya sa akwai rabo sai ki gansu ko a nan gaba ne." Yau ita ce rana ta farko da na ji dadda an kalamai daga bakin wani daga cikin Bayin da nake mu'amala da su, don haka na iri murmushin da bai kai zuci ba na furta. "Shi kenan ina godiya Uwar Bayi da wannan bayanin naki." Babu wanda ya sake tanka mini haka na tashi jiki a sanyaye kamar kazar da aka jefa da wu a na koma mazaunina na farko na zauna ina jin zuciyata babu da i. Ina jin su suka ci gaba da hirarsu sai dai ko ka an ba na fuskantar koda kalma aya, zuciyata ta yi nisan kiwo a fannin tunani da na gagara janyo ta balle ta gane in da hirarsu ta dosa. Wani farin tsoho mai auke da farin gemu na gani yana tunkaro ni, tsananin kammanin da muke yi da shi ya sa na tsaya cak ina kallonsa. Tun da na zo duniya ban ta a ganin mai kamceceniya da ni ba, ban yi tsammanin ya kusance ni ba don haka na ji hannuwansa a cikin nawa. "Kada ki damu da sai kin san wace ce ke, kina da kowa kuma wannan masarautarki ce gadonki ce halak malak, sai dai ina mai ta'ajibin sanar da ke har duniya ta tashi ba za ki ga mahaifiyarki ba. Ni ne mahaifinki! Ni ne mahafinki!! Ni ne mahaifinki!!!" Firgigit na farka daga mafarkin da nake yi, na juya ina kallon yadda mutane ke baccinsu hankali kwance. Mamaki ya kama ni, cikin damuwa na furta. "Ya aka yi ka zama mahaifina? Kuma me ya sa kuka guje ni." Kamar alamara na ji an furta mini. "Ba mu guje ki ba, mun kawo ki karagarki ne don ki kar i abarki." Waige-waige na fara yi don ganin mai tanka mini a cikin tsohon daren nan, har na yun ura zan tashi sai na ji tsoro ya mamaye ni, ba shiri na koma na zauna bacci ya aurace mini. A lokacin da bacci ya fara fisga ta na ji Uwar bayi tana tashinmu cikin hargowa da masifa kamar yadda ta saba duk asubar fari. A haka na ci gaba da gudanar da rayuwa cikin rashin da i, rashin 'yanci da angin bauta. Mu Bayi ba mu da wani gata ba musan ci mai kyau da sha mai kyau ba, ana cikin haka watarana sa o ya iso gare mu ana san Uwar bayi ta sake za en Bayi ta kai sashen Fulani Hauwa kulu, haka kawai na ji gabana yana tsananin fa uwa. Aka saka mu muka yi layi cikin tsautsayi addara ta yarfo mini hannunta, Uwar Bayi ta za a har da ni a cikin mutane ukun da Fulani Hauwa take bu atar ari.Tun da nake rayuwa a cikin Masarautar ban ta a shiga sashen Fulani ba, hasali ma ban ta a tozali da ita ba, sakamakon rashin imanin da nake jin ana fa a game da ita. Wannan ta sa nake takatsantsan a kan abin da zai sa na kai kaina sashenta. Tun da muka dumfari hanyar sashen Fulani nake jin jikina yana yi mini wani irin zafi, hayaniya na fara ji sama-sama a kaina ga wani ki an tambura da nake ji yana tashi a tsakiyar kunnuwana. Sai dai yadda na lura ni ka ai nake jin wa annan ba in al'amuran da ke yi wa duniyana dirar mikiya. Take gumi ya fara keto mini sakamakon yadda nake jin zafin na ratsani kamar wacca aka tsire a tukubar tsire. A babban ofar rumfar (Falo) Fulani Hauwa na coge, sakamakon yadda nake jin ana fisgata. Hayaniyar da nake ji ta fara riki a zuwa muryar da nake jin tamkar na ta a sanin mamallakiyar muryar. "Barka da zuwa Sarauniya." Na ji an furta. Waige na fara yi amma ban ga kowa ba, na ri a jin busar sarewa a tsakar kaina ba tare da na ga masu yi mini ba. Ina nan tsaye na ji Uwar Bayi na fa "Ku yi hanzari kada ku fusata Fulani kuke tafe la ai-la ai kamar marasa laka a jiki." Da sauri na ci gaba da tafiya har muka arasa babban rufar Fulani da ta ayatu da kayan alatu kala-kala. Kaina na ji ya yi girma wata irin asaita, isa da tsantsar izzar mulki na ratsa ni, da yar nake taku cikin asaita. Uwar Bayi da sauran Bayin da muka taho tare suka tsaya cak a bakin wata mashinfi a wacce bayi suke tsayawa idan sun shiga wurin Fulani Hauwa kulu. Ban kalle su ba na zarce kan asaitacciyar karagar da ke cikin falon, na zauna ina kallon su Uwar Bayi ai. Da zamana na ji wani abu au! Yana zagaye on kaina. Uwar Bayi kusan mutuwar tsaye ta yi ganin anyan aikin da na aikata, bakinta na rawa ta furta mini. "Hidaya...hankalinki aya kuwa? Kin san a fadar wacce kike?" "Ya kamata ki gyara linzamin harshenki, idan ba haka ba sai na sa an datse shi nan take. Wannan fadata ce..." Ashar in da Fulani Hauwa kulu ta saki ya katse kalamaina, na dube ta cikin tsadaddiyar shigarta ina are mata kallo. "Uban waye ya halatta wa wannan antaciyyar zama a karagata?" Cikin isa da asaita na ora afa aya kan aya, kamar ba zan amsa ba na ago ina kallonta a wula ance. "Wannan karagar iyaye da kakannina ce don haka ki gyara kalamanki." Na lura da razani a saman fuskarta, an yatsanta na rawa ta nuna ni. "Ta tabbata ke ce Hidaya ko?" Na jingina da jikin kujerar na furta. "Ba tsammani ba ne ni ce Gimbiya Hidaya." Wata gwauruwar ajiyar zuciya na ji ta sauke. "Tabbas da alama tarihi zai kuma maimaita kansa. "Tarihi tuni ya sake maimaita kansa tun da gani na wanzu a gabanki." Fulani Umaima ta rufe littafin tana jin kanta na sarawa don a kullin labarin Hidaya ara hargitsa kwanyarta yake. Ta wurga shi cikin akwatinta tana sakin tsaki a fili don ba ta jin za ta sake ci gaba da karanta wannan rikitaccan labarin. Komawar su Yaya Halima Masarautarsu da kwana aya labari ya dawo wa Fulani Babba na sabuwar lalurar da ta afka wa Yaya Halima na kurumcewa da makanta, hankalin Fulani Babba ba aramim tashi ya yi ba. Da yake jego take yi babu damar ta tafi dubiya haka ta zauna ta ci kukanta a cikin aki, ta sake ayyanawa zuciyarta ko da wasa ba za ta sanarwa da mahaifiyarta halin da take ciki ba don kar damuwa ta yi mata yawa. BAYAN SHEKARA GOMA Tafe suke a cikin wani ba asurgumin daji mai matu ar hatsarin gaske, su kansu sukan yi takatsantsan wurin shiga irin wa annan dajijjikan sakamakon miyagun hallitu da iskokin da ke cikinsa. "Mai gado wai ni kam kin taho mini da ba ar bakata?" Umaru ya fa