← Book details Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 89

Sashe 54

Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ficewa daga akin ya rufa wa Jawahir baya. "Da ace ka san matsayinsa da ba ka tsaya kana tambayarsa dalilin zuwansa wurin nan ba Sarki Abdul'aziz." Dattijo Maharaz ya yi maganar yana jingina da bango. A razane Sarki Abdul'aziz ya dubi wurin da yake jin muryar da ko a mafarki ya ji ta sai ya tantance ta. "Wane ne kai? Me ya sa kake son yaudarata da muryar Dattijon da nake matu ar ganin girmansa da mutumtawa?" Murmushi Dattijo Maharaz ya sakar masa sannan ya furta. "Ba yaudara ba ce Sarki Abdul'aziz! Kuma ba gizo wayar idanunka take yi maka ba, kana tare da Dattijo Maharaz, Dattijon da yake matu ar farinciki da ganin irin girmamawar da zuri'ar aminsa suke masa." A take Sarki Abdul'aziz ya saki baki da hanci cikin tsananin mamaki domin wannan shi ne karo na farko da ya ta a sanya wayar idonsa a surar Dattijo Maharaz a zahiri duk da ya fito masa a cikin surar mutane, sakamakon tun yana arami sai dai ya ji muryarsa a bakin shurin da ya bu e ido da ganinsa a turakar mahaifinsa. "Ya aka yi aka haihu a ragaya Dattijo Maharaz? Me ya sa ba ka ta a bayyana mini kanka ba sai yanzu?" Kafin Dattijo Maharaz ya ba wa Sarki Abdul'aziz amsa suka ji wani irin as a daidai wurin da Kamalu ya ajiye butar, wata irin katantanwa ta fara yi sannan wani farin haya i ya fara fita daga cikin gidan tururuwar. Nan take Kamalu ya fara fita daga hayyacinsa, a hankali ya fara takawa don ya arasa kan gidan tururwar, da sauri Dattijo Maharaz ya sha gaban Kamalu hankali a tashe yana fa "Kada ka yi mini haka Furhussam! Kada ka aiwatar da abin da zai zo daga baya ana da-na-sani." Dattijo Maharaz ya furta a an razane. "Ka matsa daga gabana Maharaz, kada ka yi gangancin dawo da borno dawaki. Abin da ya faru ya riga da ya wuce don haka kowa ya yi harkar gabansa." Furhussam da yake magana ta jikin Kamalu ya furta yayin da Dattijo Maharaz ya sha gabansa. "A yarjejeniya da muka ta a yi babu aukar aya hallita aya daga cikin zuri'ar Masarautar nan." Fa uwa asa Kamalau ya yi, nan take wani gajeren mutum ba i wuluk mai fafa ar fuska, kansa auke da wata hular arfe ruwan zaiba ya ce. "Maharaz ba na tunanin akwai wani mahaluki da ya isa ya sa na gagara zartar da hukuncin da na yi niyya, ba tun yanzu ba ya rayu cikin kulawa da ikonmu. Don me zai sa bayan ya gama aiwatar da abin da muka jima muna buri ba zan auke shi ba?" Gaban Sarki Abdul'aziz ya shiga bugawa. Ya dubi angaren Dattijo Maharaz a an rikice, "Me yake faruwa Dattijo Maharaz? Ina jin tsoron kada wani sabon al'amari ya faru da al'ummar cikin masarautata." "Wannan tsohuwar da iyar gaba ce Sarki Abdul'aziz, wannan yaron kuma da kake gani makusancinka ne kuma makusancin wannan karagar da kake kai ne. Ban yi niyyar furta wannan maganar ba amma tun da na lura Furhussam bai ri e al warin da muka auka ba zan fayyace maka komai amma sai yaron nan ya dawo hayyacinsa don na yi masa al awarin hakan." Dattjio Maharaz ya arasa maganar yana matsawa gaban Kamalu da ke kwance jikinsa na wata irin karkarwa. "Idan haka ne ba mu ka ai muka karya al awari ba amma tun da haka ne yau ko sama da asa za ta ha e sai na atar da yaron nan daga cikin masarautar nan." Da sauri Dattijo Maharaz ya ago ya dube shi, yana shirin magana Sarki Abdul'aziz ya furta. "Dattijo Maharaz ka fi kowa sanin ni ba ma'abocin son hayaniya da tashin hankali ba ne, don Allah ka lamunce masa ya auki yaron na tun da shi ma yana daga cikin jinsinku na aljanu." Murmushi Dattijo Maharaz ya yi sannan ya kalli Sarki Abdul'aziz da ke cikin matsananciyar damuwa. "Allah sarki Abdul'aziz! Tabbas na yarda rashin sani ya fi dare duhu, duk wannan cizawa da ake yi da ni saboda kai nake yin ta." Da mamaki Sarki Abdul'aziz ya ce. "Saboda ni kuma Dattijo Maharaz?" Dattijo Maharaz ya gya a masa kai cike da arfin gwiwa. "Wannan da kake gani sunansa Sarki Furhussam, ya kasance Sarki kuma Shugaban ba en aljanun doron asa. Tun a dubban shekarun da suka gabata mun yi zaman ma otaka da su ga gida ga gida amma bisa yanayin abi'a da mu'amalarmu da ta sha bambam sai ya zamana mun fara zaman doya da manja. Ka san mene ne muhimmiyar gabar da ta gifta a tsakaninmu?" Dattijo Maharaz ya wurga wa Sarki Abdul'aziz tambaya. Girgiza masa kai ya yi sannan ya ci gaba da cewa. "Yara ne suka shiga tsakaninmu, ba iya ku ka ai ba hatta jinsinmu fa an yara ya kan yi tasiri har zuwa kan iyayensu idan ba a kai zuciya nesa ba. A dubban shekarun da suka gabata Shugaba Furhussam yana da wata hatsabibiyar yarinya marar jin magana da rashin ganin giraman manya mai suna Hullat, ba zan oye maka ba; ba iya nan ta tsaya ba har 'yan sace-sace da haddasa fa a tsakanin ma'auratan jinsinku take yi. A lokacin shi kuma ana na uku wato Umaru ya tasa sai ya zamana shi mai zafin zuciya ne ba ya aukan raini. Ana cikin haka sai fa a ya ha a su har ta kai Umar ya yi mata jina-jina, a lokacin da afata na taka har zuwa wurin Furhussam a kan musamu maslaha na ba shi ha uri a sasanta yaran, amma fir sai ya i saurarata. In ta aice maka dai sai ma ya auki gaba da ni ko magana na yi masa ba ya tanka mini, sannu a hankali sai na watsar da lamarinsa da iyalansa. Ashe wannan abin da ya shiga tsakanin Hullat da Umar ita tuni ta fa aunarsa har ta ta a samunsa ta sanar da shi, shi kuma ya yi mata korar kare. Tun daga ranar duk yarinyar da Umar zai gani ya ce yana so ba ta sake kwana a duniyar nan Hullat take hallaka ta, sai da ta kai ta kawo ko ganin Umaru 'yan matan cikin jinsinmu suka yi ba sa tsayawa. Lokaci aya ya zama tamkar mujiya ko kiran sunansa ba a son yi, daga arshe da na yi bincike ma zurfi sai na gano da sa hannun Hullat a ciki. A ranar da na sanar da Umaru a ranar kuma kusan sai da samari goma suka kwanta dama a cikin zuri'ar Furhussam, a ciki kuwa har da yayan Hullat wanda shi ne babban an Sarki Furhussam in. Wannan rashin ne ya harzu a Furhussam ya shiga taya 'yarsa kisan zuri'ata, ganin haka ya sa matasan cikinmu suka mara wa Umar an wurina baya aka yi ta auki ba da Abu kamar wasa aramar magana sai ta zama babba, tun ina aukan fa an a matsayin na wasa har abu sai da ya kai mu ga gagarumin ya i. Bayan da urar ya in ta lafa kowannenmu sai da ya rasa wani tsagi daga angarensa, sai Malam Habu limamin cikinmu da shi da Shugaban da ke koyar da su Furhussam na su addinin na bautar ruwa suka ha u aka tsayar da matsaya cikin maslaha. Shugabanninmu ne suka tsayar da matsayar kowannenmu kada ya kuskura ya shiga sabgar waninmu, ko azabartar da waninmu ko kuma aukan waninmu ba tare da ha insa ba. Sakamakon mu muna daga cikin jinsin fararen aljanun doron asa, shi kuma Furhussam yana daga cikin jinsin ba en aljanun doron asa. Daga arshe ma sai suka yi aura daga cikin mu sai dai lokaci-lokaci sukan dawo mahallansu su kwana biyu su ara gaba." Ajiyar zuciya Sarki Abdul'azi ya sauke, Dattijo Maharaz ya ci gaba da cewa. "Dubi can Abdul'aziz." Da sauri Takawa ya kalli wurin da Dattijo maharaz yake nuna masa. "Wannan tafkeken gidan tururuwar da kake gani shi ne ainihin muhallinsu, shi ya sa sai a kusa shekara ba ka ga giftawar turuwa ta fito ko waya aya ba. Idan ban manta ba ka ta a yi mini orafi a lokacin da turuwa ta addabe ku na ce maka wannan ba hurumina ba ne. Wannan shurin da kake gani shi ne angarena da zuri'ata da muke rayuwa cikin aminci, sai kuma idan mun yi sha'awa ko iyalanmu mata idan za su yi aiki suka fita cikin jinsinku ba tare da ku kuna ganinsu ba. Fulani Umaima ta yun ura da sauri da niyyar auko ahonta don ziyartar Bamaguje, ta ji wani irin auuuu a asanta tamkar zai zazzago, da sauri ta koma ta zauna tana runtse ido cikin azaba. Jin abin na sake tunku o mata ya sa ta kai hannu da sauri nan take ta ci karo da wani mulmulallan abu ya tokare ta tamkar kan a ne zai fito. A galabaice ta fara yarfe gumi ta le a don ganin ba on yanayin masifar da rufto cikin rayuwarta babu tsammani, tashin hankalinta ya nunku sakamakon cin karo da ta yi da wata mulmulalliyar ba ar tsoka ta tokare ta, sannu a hankali wasu ba en tsutsotsi suka fara fa owa aya bayan aya. Da rarrafe da jan gwiwa ta fara ja har ta arasa da yar ta iya auko ahon ta busa don arasawa wurin Bamaguje ko ya magance mata damuwa da al'amuranta. "Fa uwa ta yi daidai da zama Umaima! Yanzu nake shirin auko ki sai kuma aka yi katari gaki kin kawo kanki!" Kuka ta fashe masa da shi, a wannan karon duk wata al'ada da take yi ta ziyartarsa ba ta tsaya ta aiwatar ba saboda azaba. "Ka taimaka mini Bamaguje ka dubi halin da nake ciki." "Ki saurara mini Umaima don yanzu haka a kan hanya nake, dama na yi niyyar auko ki ne domin na kai ki dajin Bururu wurin Tsoho kuma Shugaba Zurufu. Shi zai yi mini iso wurin gawurtattun Ba en al'aljanu domin na samu nasarar dawo da littafina da ke hannun Shaddas, shara i ne ya gindaya mini a kan tilas ne sai na zo da ke domin ke ce mahaifiyar Basiru akwai tambayoyin da zai gudnar miki." Take cikin Fulani Umaima ya uru ruwa,
Chapter 54 · 0% Book details