← Book details Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 89

Sashe 67

Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta fara zirarar da wallah murya a sanyaye ta furta. "Tabbas na yarda rana dubu ta arawo ce rana aya ce tak ta me kaya, tun kafin ka aure ni nake cin duniyata da tsinken tsire har kafin lokacin da duniya ta yi mini atishawar kaji, duk abin da ya faru ni ce sila. Da hannuna da gabban jiki tare da taimakon wannan tsinannan mutumin da yake i irarin mahaifina ne shi. Na zalinci Fulani na zalince ka ranka shi da e." "Ki gama tsinewa Bamaguje ni kuma na tabbatar miki da naki hukunci don na yi rantsuwa na ara, sai na shayar da ke ruwan azabar da ko mutuwa kika yi aka ambaci sunana sai kin farfa o." Bai Maimuna ta yi maganar cikin wata irin murya mara da in sauraro. *SHU'UMAR MASARAUTA* *35* *Littafin ku i ne 500 idan kina bu ata za ki biya ta wannan Account in Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.* Boka Shaddas na acewa daga kogon dutsensa bai sauka a ko ina ba sai a bakin dutsen Shugaba Zurufu, ya jima a tsaye yana arewa dutsen kallo sannan ya shiga ciki a lokacin duhu ya mamaye ko ina, shiru cikin kogon dutsen ya yi babu motsin komai sai sautin tafiyar da Boka Shaddas yake yi. Sai da ya je tsakiyar filin haske ya gauraye cikin dutse. Cak Boka Shaddas ya tsaya ya har e hannuwansa a irjinsa, bai yi tsammani ba sai gani ya yi Shugaba Zurufu ya burtso ta ashin asa a gabansa har sai da ya an tsorata. Baya ya ja suka fura wurgawa junansu kallo kowa da manufarsa a zuciya, Shugaba Zurufu ya katse shirin da cewa. "Barka da zuwa Boka Shaddas!" Bai amsa ba kuma bai yi alamun zai amsa ba, don haka Shugaba Zurufu ya ci gaba da cewa. "Dama na san ko ba da e ko ba jima za ka kawo kanka..." "Ina ana yake?" Boka Shaddas ya katse shi rai a ace. Sai da Shugaba Zurufu ya koma can kan wani farin dutse ya zauna sannan ya furta. "Yanzu haka yana tare da kai, sai dai ba za ka ta a tozali da shi ba har sai ka cika sharu an da zan gindaya maka." "Idan kuma na ha ura da shi fa." Boka Shaddas ya yi maganar yana zuba wa Shugaba manyan idanunsa. Sai da Shugaba ya auki wani garin magani ya watsa a cikin wutar da ke ci a saman cinyarsa sannna ya wara hannuwa alamun rashin damuwa ya ce. "Idan ka ha ura da shi ba ni da damuwa, amma ka sani ha ura da Basiru tamkar ka ha ura da kundun tsafinka ne gaba aya. Idan ba ka yarda ba ka koma can kogon dutsenka, ka binciki rijiyar tsafinka za ta ba ka tabbacin abin da nake nufi." Ajiyar zuciya Boka Shaddas ya sauke gabansa na fa uwa, duk yadda ya so nuna dakiya don kada Shugaba ya fahimci rauninsa abin ya gagara. "Mene ne sharu an naka?" Boka Shadda ya wurga masa tambaya. Shugaba na jin haka ya mi e ya auki sandar tsafinsa ya fara tafiya yana zagaye kogon dutsen da ita, sai da ya kammala sannan ya sake komawa mazauninsa na farko ya furta. "Shara ina guda aya ne, don haka a yanzu sai da na toshe duk wata arakar da mahaifiyarta za ta ba ni matsala, a baya ta yi yun urin binne mana tushenta amma bincikena ya haske mini ita. Sai dai Fargi ta kasance hatsabibiya kuma mai tsananin wayo, ta nesantamu da 'yarta don haka wani daga cikin zuri'armu bai isa ya sarrafata yadda ya dace ba. Dalili kenan da zan tura ta ka kawo mini JAWAHIR, yanzu haka tana can cikin Masarautar Huddam. Idan ka aikata mini haka na yi rantsuwa da girman tsafi da sihirina sai na dawo maka da anka kuma na ninka maka arfin iko da tsafinka." A madadin kalaman Shugaba su faranta ran Boka Shaddas sai ya sake tur une fuska, "Me ya sa sai ni? Me ya sa duk yawan bokayan da ke fa asar nan ba za ka zartar da wannan hukuncin a kansu ba sai ni?" "Saboda sara aka yi a kan ga a kuma fa uwa ta yi daidai da zama." Shugaba ya katse Boka Shaddas, shiru ya yi har lokacin yana bin Shugaba da kallo. "A daidai ga ar da nake yunwar bu atarta a wannan lokacin Jakadiyar Masarautar Huddam da ka ta a kawowa ta kawo mini kanta a kan wata bu ata da take ci mata tuwo a warya, ganin haka ya sa na jefi tsuntsu biyu da dutse aya. Wato na bata umarnin kawo mini Basiru domin na san kai jajirtacce ne za ka aiwatar mini da abin da nake bu ata, yanzu haka tun kafin ka dawo daga taron da aka gayyace ka na gama magana da Shugaba, ka aiwatar mini da abin da nake bu atar ni kuma na warware maka zare da abawa." Guntun tsaki Boka Shaddas ya saki sannan ya furta. "Zan koma kogon tsafina domin na nazarci abin da ya kamata, duk hukuncin da na yanke za ka ji daga gare ni." Daga haka Boka Shaddas ya fice daga kogon dutsen ba tare da ya ji abin da Shugaba zai fa a ba. Kai tsaye halawar tsafinsa ya koma yana jin zuciyarsa na tu acin rai, a angare aya yana ayyana irin mummunan hukuncin da zai yanke wa Jakadiya. Jin kalaman Baiwa Maimuna ya s ake ka a hantar cikin Fulani Umaima, ta sharce walla tana sunkuyar da kai asa don haka kawai take jin kunyar mutanen akin. "Yanzu Ammi kina nufin duk abin nan da ake fa a kin aikata? Wacce irin zuciya gare ki Ammi? Me ya sa za ki biye wa son ranki ki aikata wannan rashin imanin?" Yarima Muhsin ya yi maganar cikin matsanancin acin rai. "Saboda a lokacin shai an ya buga mini gangarsa don haka zuciya ta ingizani har na taka rawa son raina, rawar da ta shammaci afafuwana zuwa fa awa tekun nadama da da-na sani." Fulani Umaima ta tsahirta saboda yadda ta ji numfashinta na shirin aukewa sakamakon wannan tsokar da ta tokaro ta, sai da zugin ya lafa mata sannan ta ci gaba zayyana duk abin da faru a rayuwarta tun farkon zuwanta cikin Masarautar taba budurwa, har zuwa aurenta da Takawa da rayuwar da suka gudanar ita da Fulani Babba. Ilahirin mutanen wurin jikinsu ba aramin sanyi ya yi ba, ban da hawayen tausayin Fulani Babba babu abin da suke yi. Sailuba ta kalli Jakadiya tana jin wani irin aci a ranta, kunyar Sarki Abdul'aziz ta lullu e ta don ba ta san da wanne idon za ta kalle shi da laifin mahaifiyarta ba. "Wannan mata amma ke dai kin cika azzaluma marar imani." Inna wuro ta furta wa Fulani Umaima tana share wallar idonta. Kamalu ya waiga ya sake kallon halin da an uwansa yake ciki, ya tuna irin gwagwarmayar da aka fa i mahaifiyarsa ta sha sai kawai ya fashe da kuka yana ora kansa a kan cinyar Inna Wuro. A sanyaye Jawahir ta zauna tana jin tsanar Fulani Umaima na mamaye ta, ta waiga wurin Kamalu tana bin sa da kallon tausayi. "Ashe dama Inna Wuro ba ita ta haifi Kamalu ba? Kenan a yanzu batsayinmu aya ba shi ba ya tashi daga matsayin Bawa?" Jawahir ta fara watsa wa zuciyarta tambaya. Jakadiya sai da ta share wallar idonta tana shirin neman yafiyar Sarki Abdul'aziz ba ta yi aune ba zuruf ta ji hannun Buguzu a saman rigarta, da sauri ta ago za ta yi masa magana ya katse ta ha e da wurga mata wala- walan idanunsa. "Kada ki dakatar da ni don na lura abin ba na are ba ne, ni fa ba haka muka yi da Shugaba Zurufu ba. Ya mallaka mini ke har abada kuma tun a farkon dare nake son arje amarci amma sai cikas ake kawo mini." Buguzu yana gama maganar ya sake zura hannunsa, kafin Jakadiya ta yi wani yun uri tuni ta ji hannunsa ya mur e mata mamanta tamkar zai tsinke mata su, dalilin haka ya sa Jakadiya da Buguzu da ke auke da siffar Basiru suka fara kiciniya. "Dakata Buguzu! Kada ka nuna mana rashin a'a. Duk uzurunka ba ka kai wa annan bayin Allahn ba, don haka wannan rashin girmamawa ne." Dattijo Maharaz ya yi maganar rai a ace. Ba don ya so ba Buguzu ya saki Jakadiya, ganin haka ya sa ta yi tsalle daga wurin da koma can gefen Fulani Umaima. Ta sunkuyar da kai asa cike da nadama, "Ka fafarce ni Ranka shi da e, wallahi sharrin shai a..." "Ku adana tubanku Jakadiya ba ma bu ata." Sarki Abdul'aziz ya katse Jakadiya murya a kausashe. Ya ago ya dubi Fulani Umaima yana jin wani irin aci a ransa, da sauri ta sunkuyar da kai asa gabanta na fa uwa. "Yanzu wanne irin hukunci kike so na yi miki Umaima?" Shiru ya ratsa akin kowa da abin da yake ayyanawa a ransa. "Don Allah ka yafe mini..." "Hukunci na tambaye ki." Takawa ya sake katse ta. "Duk wani hukunci da za ka aiwatar mini duk azaba da ra insa zan iya auka, amma don Allah don girman Allah kada ka tsame ni daga ashin inuwarka. Kada ka yanke jajirtacciyar ala ar da ke tsakaninmu ta auratayya, ba zan iya jure rashinka ba. Allah ya sani kishi da aunarka sune tsanin da suka kai ni ga duk wani mummunan aikin da na aikata ranka shi da..." "Yanzu idan na ce zan ci gaba da zama da ke za ki amince Umaima? An ya kin tuna irin miyagun ayyukan da kika aikata mini? Idan Fulani kishiyarki ce shi wannan yaron ba jinina ba ne?" Shiru Fulani Umaima ta yi ban da hawaye babu abin da yake zarya a saman fuskarta. Sarki Abdul'aziz ya juya wurin Bamaguje sannan ya furta. "Bamaguje kake ko? Ka zo da wa ansu kalamai da suka rikita mini kwanya amma a wannan ga ar ba zan yanke hukunci ba, don haka za a sake saka mana lokaci domin wannan maganar dole za ta je wurin Mai martaba wato mahaifin
Chapter 67 · 0% Book details