← Book details Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 89

Sashe 82

Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yi matu ar mamakin jin tafiyar Takawa a rana tsaka. Tuni aka aikawa da Mai gado game da tafiyar, Kamalu tamkar zai zubar da walla a lokacin da za su tafi. Sarki Sulaimanu yana cikin turakarsa bayan ya koma daga dubo jikin mahaifiyarsa aka sanar da shi zuwan Sarki Abdul'aziz daga Masarautar Huddam tawagarsa, duk da bai san da zuwansu ba amma nan take ya sa aka shirya musu tarba ta musamman. Ba su auki lokaci mai tsayi ba Sarki Abdul'aziz ya furta. "Sarki Sulaimanu mun zo ne domin ka yi mana wata alfarma." Sarki Sulaimanu fuska auke da mamaki ya furta. "Alfarma kuma Sarki Abdul'aziz? Wacce iri?" Dattijo Maharaz da ke gefe ya yi shiru yana jin tattaunawarsu. "Zuri'ar Rumzu! Zuwa gare su muke son ka yi mana iso..." A zabure Sarki Sulaimanu ya mi e tsaye jiki na karkarwa. "Ya aka yi ka san da su? Wannan binannan sirri ne da iya mutum biyu ne ka ai suka da shi. Ya aka yi kasan ala ata da..." "Ni na sanar da shi haka Sarki Sulaimanu. Kuma mun zo ne domin neman goyon bayanka zuwa cikin wa annan mutanen domin akwai abu mai matu ar muhimmamci da za mu aiwatar." Dattijo Maharaz ya katse Sarki Sulaiman. "Ko da babu kowa na fargi a wurin zan je wannan garin ballanta mahaifi da mahaufiyarta suna raye." Sarki Sulaiman ya furta sannan ya sa aka yi musu shiri suka nufi garinsu Fargi. Mai gado tun daga Masarautar Huddam kanta ya kulle, sakamakon babu wani kyakkywan bayani da aka yi mata, ba don Takawa ne a gabanta ba da ta tambayi dalilin gayyato ta da zuwa wannan garin, amma ta san ko karen hauka ne ya cije ta ba ta isa ta wurga masa tambaya ba. Abu aya ne ya tsaye mata a rai jin sunan Fargi don idan ba ta manta ba ta ta a jin Jawahir ta ce ita ce take yi mata i irarin mahaifiyarta ce. *Littafin ku i ne 500 idan kina bu ata za ki biya ta wannan Account in Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.* Ganin ofar akin nasu a bu e hanhai ya sa Jakadiya ta fara jan jiki a hankali ta zo ba ofar wurin da niyyar ta fita idan ya so ko guduwa sai ta yi tun da dare ya fara yi ba lallai wani ya ganta ba. "Idan kin tafi ina za ki je? Waye zai kar e ki a wannan yanayin da kike ciki? Ki rufa wa kanki asiri ki koma, zamanki a wannan wurin shi ne suturarki." "Ki gudu kawai, yanzu zama za ki yi azaba ta kashe ki?" Tagwayen shawarwarin suka fara shawagi a zuciyarta. "Kamar ba ki san a cikin gidan da kike ba? Kin manta ke Jakadiya ce labarinki ya gama kara e ciki da wajen masarautar nan a kan abin da kika aikata? Ki rufa wa kanki asiri kawai ki koma ciki." Zuciyarta ta sake ba ta shawara. Babu yadda ta iya a hankali ta sake jan jiki ta koma cikin akin, har lokacin Fulani Umaima na wurin da Muhsin ya bar ta tana zubar da hawayen nadama. "Ban san haka duniya take yi wa mutum atishawar kaji ba sai da layinta ya zagayo kaina. Kaicon rayuwar da ba ta da amfani, ni Umaima na cuci kaina." Fulani Umaima ta yi maganar cikin galabaita da tsantsar nadana. Abin duniya ya ha e wa Sailuba goma da ashirin sakamakon yadda mutane suke yamatarta da wula antata dangane da laifin mahaifiyarta, ko guri ta je tana zama kowa yake darewa sai dai a barta ita ka ai. Lokaci aya ta fige ta rame ta lalace Uwa-uba cutar kwarkwatar da ke damunta, don ta samu ruwan da ke fita daga ansata ya yi sau i sosai. Sai a wannan lokacin da ta bambamce tsakanin tsaba da tsakuwa take dana-sanin wula ancin da ta dinga yi wa Bayi a baya, sai ga shi Bayin da take hantara take kyara a wannan lokacin sun fita ima da mutumci a idanun manyan masarautar da sauran mutanen cikin gidan gaba aya. Idan ta yun ura don ta je ta gano halin da mahaifiyarta take ciki fargaba sai ta mamaye ta, sau aya ta ta a zuwa ta gano ta ranar ko baccin kirki ba ta iya yi ba saboda damuwa. A wannan ranar ne ta yanke shawarar sake zuwa ta gano halin da Jakadiya take ciki, ta tafi da wani guntun busasshen anzo a leda ta tafi mata da shi don ta san abinci sau aya suke ci a wuni guda. Duk irin dakiyar da ta gayyato wa kanta sai da warin wurin ya addabe ta, don haka ta sa hannu ta toshe hancinta tana jin wani irin amai yana taso mata. Kwamacalar fitsari da tsutsotsin da ke cikin akin ya sa Sailuba ba ta iya shiga akin ba, sai daga bakin ofa ta iya wurga wa mahaifiyarta ledar arzon da ko daka shi ba ta yi ba. Kamar kaji haka suka fara kokawa a kan ledar sabida yunwar da ke addabarsu, suna cikin haka ledar ta yage suka ci gaba da ibar na asa suna cinyewa. Wani irin kuka ne ya zo wa Sailuba ta juye za ta bar wurin ta hangi wasu aratan Dogarai sun nufo wurin da ofa a hannunsu, basu kula ta ba suka fara kiciniyar mayar da ofar wurin ganin haka ta sa ta wuce sashensu Bayi zuciyarta a dagule. Gya a kansa Mahaifin Fargi ya yi ya ce mata. "Amma Fargi me ya sa kika yi nisa da mu? Me ya sa kika guje mu? Mun jima muna bulayin nemanki amma ko mai kamarki ba mu ta a gani ba sai a yau da na yi tozali da yarinyar nan." "Akwai rikitattun labarai da zan bayar game da Fargi, amma sai na kai Jawahir binne littafin labarin Hidaya sannan ta auko sihirtacciyar takobin da ta Hidayan ta binne. Da sauri Jawahir ta fara ja da ba ya ta ce. "Don Allah ki kaini wurin Inna na san tana can cikin damuwa." Jawahir ta furta kamar za ta yi kuma. "Innarki ta taho yankin nan kada ki damu Jawahir." Shiru Jawahir ta yi ba ta amsa ba. Tana nan tsaye mutane suka ci gaba da tuttu owa ana shigowa cikin kogon dutsen, kallonsu ta fara yi aya bayan aya tana sakin murmushi sannan ta ri e hannun Jawahir sosai ta furta musu. "Ku dakace mu zuwa wani an lokaci ka an." Daga haka suka ace daga wurin ba su tsaya a ko ina ba sai a cikin wata farar sahara, bakin wani koren kogi suka arasa ruwan cikinsa garai-garai kana iya kallo duk abin da yake ciki. Sannu a hankali Fargi ta fara jan Jawahir har cikin ruwan, wani irin sanyi ta ji yana ratsa ilahirin jikinta. A tsamaaninta kogin mai zurfi ne sai dai har suka je tsakiyarsa a yadda yake haka suke tafiya. "A shakaru masu yawa da suka wuce ainihin gurin nan ba teku ba ne, ko lokacin da Hidaya ta binne takobinin babu ruwa a gurin nan. Saka hanunki a nan ki auko takobin nan." Fargi ta yi maganar tana nuna wa Jawahir wani zabgegen farin takobi da ke tsaye cak a cikin gidansa yana walwali da aukan ido. Babu musu Jawahir ta saka hannunta za ta auka am ta ji takobin ya fara fisgarta can asan ruwa, a tsorace ta fara kwarara ihun sai bayan wani lokaci ta ji komai ya lafa sannam ta ri o takobin hannun nata. "Ungo mayar da littafin nan ciki, jiya na ku utar da shi daga hannun Shugaba don na san zai iya atar da shi ko ya one shi domin kowa ya rasa." Kamar mutum mutumi haka Jawahir ta tsaya duk abin da ake saka ta haka take aiwatar da shi, saboda kallo aya za ka yi mata ka fahimci a tsorace take. A hankali ta arasa daidai wurin da ta ciro takobin ta zura littafin, da kansa ta ga yana gangarawa ya shige yana gama shiga ta ji wani abu ya aure mata kai tamkar wacce aka kafa wa hula a kanta har sai da ta kai hannu ta shafa saman goshinta. Luuu ta ji a kanta wata irin juwa na yun urin aukanta, tana shirin zubewa asa da sauri Fargi ta ri o ta tana sakin murmushin. Ru o hannunta ta sake yi suka fito daga wannan ruwan sannan ta ja hannunta zuwa bakin wata murgujejejiyar bishiyar kukar da ke ma ota da kogin, jingina ta ta yi a jikinta ta fara motsa bakinta, ta jima a haka sannan ta dafa kafa arta nan take suka ace daga wurin. A inda suka bar mutane da Mahaifin Fargi a nan suka koma suka same su tsautsaye carko-carko, Shugaba har kawo lokacin yana tsaye ba inciki ya mamaye zuciyarsa. Jagora ta yi musu zuwa wajen dutsen sakamakon cunkoson mutanen da suka aru a cikin kogon dutse, da hannunta aya ta fara jan Shugaba a asa duk irin ihun da yake yi ba ta kalle shi ba. Kamalu yana cikin Masarautar Huddam yana kula da Malam Umaru amma zuciyars da ruhinsa na wurin Jawahir da halin da take ciki, duk wani abu da Malam Umaru yake bu ata shi yake yi masa daga arshe ma gaba aya Bayin da ya kira masu taimaka masa ya sallame su. Har cikin dare Kamalu yana jin shige da ficen da Muhsin yake yi da alamar akwai abin da yake son tambaya amma ganin Kamalu ya sa ya ha iye abin da yake ransa. Sarki Sulaimanu sai da ya sa aka ha a musu guzuri da kayan abin da ba a rasa ba sannan Bayi da Sojojin cikin Masarautar suka rufa musu baya, tafiya suka yi mai nisa sannan suka shiga cikin garin Bururu. Kafin su shiga ta cikin ofar sai da Sarki Sulaimanu ya isa bakin wata bishiyar kuka da ke gefen ofar ya dafa ta da hannunsa na hagu sannan ya furta. "Sulaimanu ba shi ka ai ba ne tare yake da mabambamtan fuskoki." Sai da ya tsinki ganyen bishiyar kukar ya dam a musu kowannensu ya ri e a hannun hagunsu sannan suka shiga cikin garin, tun daga
Chapter 82 · 0% Book details