← Book details Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 89

Sashe 70

Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya rayu a cikin bautacciyar rayuwa ta 'ya'yan Bayi. "Don Allah ranka shi da e idan komai ya lafa a duba rayuwar Bayi da 'ya'yansu." Kamalu ya furta a arare don har lokacin bai gama sakin jikinsa ba. "In shaa Allahu za mu yadda ka bu ata Kamaluna." Sarki Abdul'aziz ya furta. Lokacin da su Galadima suka samu labari sun matu ar razana, sai kuma mamaki ya kama su duk da kowa ya san Fulani Umaima ba mai faran-faran da mutane ba ce, amma sun ka u da jin miyagun labaran da suke fitowa dangane da ita har zuwa kan mahafiyarsu. Kuma tun da gari ya waye suke sa ran ko Sarki Abdul'aziz zai neme su amma sai suka ji shiru, babu wani aike da suka samu daga fada. Don haka suka shirya shi da Ciroma suka wuce kai tsaye zuwa fadarsa, tamkar babu hassada ko yashi a ransu haka suka shiga taya Sarki Abdul'aziz murna da jimanta masa game da abubuwa biyu da suka faru na farinciki da ba inciki. Kamar wa ansu sababbin hallitu haka wa ansu daga cikin bayi masu son ganin waf suka bi ta hanyar baya suka isa akin duhu suna le en Fulani Umaima da Jakadiya. Tsoro ne ya kama su matu a da ganin halin da Fulani Umaima take ciki, ilahirin jikinta ya yi kace-kace da jini ta fa i a gefe sai sauke numfashi take da yar. Ita kuma Jakafiya gaban rigarta a yage ga mamanta aya da ya gutsure wani irin ruwa da jini na zuba. Uwa-uba ga wani irin wari da yake tashi daga cikin akin, don haka suka dinga toshe hancinsu. Sai da manyan Dogaran wurin suka fatattake su sannan kowa ya watse, kafin zuwa yammacin ranar tuni mabambamtan labarai suka dinga zaga ciki da wajen masarautar. Kowa da abin da yake fa a, wasu su ce Sarki Abdul'aziz ne ya sa ake yi musu wannan horon na azaba, wasu kuma su ce aljanin da suka yi wa Fulani Umaima aiki ne reshe ya juye da mujiya suke dawowa gare ta. Wasu ma har ce wa suke fatalwar Fulani babba ce ta dawo take aukan fansa. Tun safiyar ranar Ru ayya ta dame shi da son ganin mahaifiyarta, kalaman da suka fara ta a zuciyarsa yake jin tausayin yaran ya kama shi. Daga arshe ma sai ya sa aka tura ta wurin Mai gado a can sashen Fulani babba domin ta ci gaba da kula da su, wunin da Kamalu ya yi tare da Takawa duk sai ya ji shi a takure don ya saba asubar fari suke fita kowa ya kama aiki gabansa amma tun da gari ya waye sai dai ya ci ya sha su yi hira da Takawa ya kwanta. "Ranka shi da e ina son ganin su Inna wuro." Kamalu ya furta yana kallon yanayin Sarki Abdul'aziz. "Mun samar maka Bayin da za su dinga taimaka maka su yi rakiya da duk wani abu da ya shafe ka. Su Inna wuro daban suke a wurinmu don haka za su yi maka rakiya zuwa wurinsu, amma daga yau ba ma son ku dinga yawan fita har sai mun sa an horar da ku abi'u da halayen 'ya'yan sarakuna." Sai da Kamalu ya russuna sannan ya furta. "Ina godiya da wannan karamcin ranka shi da e." "Mun sa an fara gina wa su Inna wuro akuna a bayan akunan mahaifiyarka, muna so nan da an wani lokaci mu ke e su daga sahen Bayi." Sarki Abdul'aziz ya furta wa Kamalu. Farinciki ne ya mamaye shi ya sake zubewa asa ya yi masa godiya, har sarki Abdul'aziz zai sa a kira bayin da za su fara yi masa hidima Kamalu ya ce. "Amma ranka shi da e idan babu damuwa zan iya za ar bayin da za su yi mini hidima?" Gya a masa kai Takawa ya yi Kamalu ya yi godiya sannan ya fa i sunan abokansa biyu da tun tasowarsu suke tare, kuma a ganinsa wannan ce hanyar da zai bi domin ya sau a musu daga aikin bautar da suke yi suma su huta, tun da shi ma Allah ya 'yanta shi. Kamar wa anda suka ga ba uwar hallita haka Bayi suka dinga bin Kamalu da kallo, duk hanyar da ya bi sai dai Bayi su dinga zubewa a asa suna gaishe shi. Shi abin har mamaki yake ba shi, ko da ya shiga akin Inna wuro suna ganinsa suka rungume shi cikin farinciki. Inna wuro ta shiga tatta a shi tana are wa kayan jikinsa kallo. "Kamaluna kai ne haka ka fito ka yi kyau?" Baffajo ya fa a, yana ta a rantsattsiyar rigar jikin Kamalu. "Baffa wallahi na yi kewarku." Kamar ha in baki duka suka amsa masa. "Muma mun yi kewarku Kamalu." Jawahir ce ta shiga akin hannunta auke da waryar furar da Mai gado ta turo ta don ta kawo wa Inna wuro. Turus ta yi tana bin Kamalu da kallo, shi in ma kallo yake bin ta da shi. Karamcin jiya da ta yi wa mahaifinsa ya sa ya fara ganin girma da imarta. Ta e baki ta yi kamar ba ta gan shi ba, ta mi a wa Inna wuro furar sannan ta ce. "Inna wuro ga fura Inna ta ce na kawo miki kuma wai ku biyu ka ai za ku sha." Jawahir ta yi maganar tana satar kallon Kamalu don da ta san yana akin ba za ta yi wahalar dakan fura har ta dama ta kawo kuma ya sha ba. "Inna zan sha fura." Kamalu ya fa a saboda jin abin da Jawahir ta fa "Malam kar ka sake wallahi ka sha don ban daka fura don wani ato ya sha ba..." Daga bayanta Mai gado ta katse ta. "Dama rashin hankalin da kika zo yi kenan ko Jawahir? Kin manta matsayin Kamalu yanzu?" Jin haka ya sa Kamalu ya an sake tsare gida, Jawahir ta ata rai ba incikinta bai wuce a gaban Kamalu Mai gado ta dinga ce mata tana rashin hankali ba. "Wallahi ni kam bai isa ba a wurina, ni kullin a kamalu nake kallonsa tun ba a ta a sauyawa tuwo suna." Jawahir ta arasa maganar tana ficewa daga akin. Baki sake Mai gado ta bi ta da kallo, sannan ta rufa mata baya don kullin lamarin Jawahir ara gaba yake yi sai ta tashi tsaye a kanta. Wani murmushin eta Kamalu ya saki don, ya fahimci hanyar da zai bi ya cusgunawa Jawahir don ya lura rainin da ke tsakaninsu ara yawa yake yi. "Ban zaunar da ke domin ki yi mini kuka ba, tambayar ki nake cikin waye a jikin?" Mahaifiyar Fargi ta sake jefa mata tambayar. "Na aikata babban zunubin da ya kasance babban hukunci ne ga duk wanda ya aikata makamancinsa a yankin nan, Inna aure na yi na sirri ba tare da kun sani da. Ki dubi girman tsafi kada ki fallasa wannan sirrin da na sanar da ke, wallahi ban san yadda aka yi na zunduma cikin kogin soyayyarsa ba. Dalilin haka ya sa muka yi aure a oye, kuma ni kaina rannan bincike ya bayyana mini cikin da ke tare da ni." Ilahirin jikin mahaifiyarta rawa yake, ganin haka ya sa zuciyar Fargi ta sake karyewa. "Kuma shi bai kasance jinin zuri'ata ba, hasali ma Sarki ne a wata masarauta da ke nesa da yankin nan, sai dai masarautar ba oyayya ba ce. Don girman tsafi da dogaron da muka yi akansa ki binne wannan sirrin, ke uwa ce za ki fahimci abin da nake fa a. Ina nan zan ci gaba da binciko yadda zan yi da cikin jikina amma ba zan ta a lalata shi ko na salwantar da shi ba." "Me ya sa kika aikata haka Fargi bayan kin san zunubi ne yin soyayya da an wata zuri'ar, amma har ta kai ki ga aure?" "Saboda ina son a dakatar da wannan mummunar abi'ar da ke shiga ha in zu ata, an kashe 'yan mata da dama sanadin haka. Samari da dama sun kashe kawunansu saboda rasa masoyansu da ba sa cikin zuri'ar nan, shin ko kin san Lado, Tine, Wargu, zinne da Damiggu duk sun kashe kansu ne saboda sun san kashe su za a yi matu ar tsafi ya san suna soyayya da wa ansu da ba sa cikin zuri'armu? Ta yaya za mu samu ci gaba har zuri'armu ta bun asa a doron asa, na za i hakan ne ko zan rasa raina a nan gaba ban damu ba matu ar zai karya wannan al adarin da zuri'armu take kai tun iyaye da kakanni. Amma don matsayin da kika ba wa tsafi da sihiri kada ki tona asirina har sai bayan na sauke cikin da nake tare da shi." Ajiyr zuciya mahaifiyarta ta sauke sannan ta furta. "Ba na son na rasa ki Fargi, don haka zan taya ki rufe asirin halin da kike ciki. Amma ina tsoron abin da kaje ya zo a nan gaba." A ranar kwana uku ciff da aika takardun da Sarki Abdul'aziz ya sa aka yi, Mai martaba da mahaifiyar Fulani babba suka yi wa Masarautar Huddam tsinke, ba a gama tarbarsu ba sai ga su Mahaifiyar Fulani Umaima sun araso. Lokaci aya gidan ya hautsine da baki, Bayi suka shiga hidima da manyan ba i aka sauke su a babban akin saukar akin Sarki Abdul'aziz, babu jimawa Sakina da Khadija suma suka arasa cikin masarautar. Wasu na ji suna mamakin Ru ayya 'yar Fulani Umaima ba ta mutu ba, kun manta bayan ta haifi Basiru ta sake samun ciki ta haifi 'ya mace aka saka mata Ru ayya. Ita waccan Ru ayyan ai ita take bin Yarima Muhsin wannan kuma ita ce take bin Basiru. *SHU'UMAR MASARAUTA* *37* *Littafin ku i ne 500 idan kina bu ata za ki biya ta wannan Account in Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.* Boka Shaddas ya jima yana kai-kawo a cikin halwar tsafinsa yana bincike game da yadda zai auko Basiru amma ko ushin samun mafita bai gani ba. "Tabbas Shugaba Zurufu ya kasance ta adari kuma hatsabibi amma zan ji da shi, sai na yi masa kwantan aunan da zan shamace shi
Chapter 70 · 0% Book details