Sashe 80
Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kan atan Jawahir, domin na ji daga bakin Dogarawan ofa babu wanda ya ga fitarta." Kamalu ya yi magnar yana duban yanayin Sarki Abdul'aziz. "Mun yi wannan tunanin amma sai muke ganin mai zai hana mu bari zuwa wayewar gari, kada mu shiga ha insa idan yana da wani uzurin." Ba haka Kamalu ya so ba amma sai bai nuna komai ba, ya yi wa mahaifinsa godiya sannan ya fita. Kai tsaye sashensa ya nufa yana shirin bu ofar shiga akinsa ya ji sallamar Dattijo Maharaz, har a fili Kamalu sai da ya sauke ajiyar zuciya ya fa a fara'arsa. Sai da ya amsa masa sannan ya bu e masa akin suka shiga ciki, Kamalu ya bu e baki zai yi masa bayani Dattijo Maharaz ya dakatar da ni. "Mahaifinka dattijon warai ne da sanin ya kamata, don haka ban ba unce shi a wannan lokacin ba kamar yadda ya yi mini uzuri. Duk abin da yake faruwa na san komai Kamalu, kuma ka daina zargin an uwanka Muhsin don ba shi da hannu a atan Jawahir. Sai dai akwai babban hatsari a wannan tafiyar domin karawa ce tsakanin zuri'a biyu, kuma dole wannan tafiya za a yi ta ne da Sarki Sulaimanu." "Sarki Sulaimanu fa? Ko dai kana nufin Mahaifina Dattijo Maharaz?" Boka Shaddas shi da Basiru na isa kogon tsafinsa Basiru ya kafe ahi da idanu har sa gaban Boka Shaddas ya fa i. "Ba ni hatsabibiyar aska!" Basiru ya furta yana sake kafe mahaifinsa da kallo. "Ya aka yi ka san da ita? Kuma me za ka yi da ita..." Tun bai rufe baki ba Basiru ya auke fuskar Boka Shaddas da hatsabibin mari nan take wayar idonsa na hagu ya fa o, wata irin azaba ta ratsa shi cikin ki ima ya kwarara ihu cike da azaba. Babu shiri Boka Shaddas ya turbutsa hannu a cikin ashin asa ya zaro wata anwar aska, jikinsa na rawa ya mi a wa Muhsin don bai manta ba da ita ya hallaka mahaifinsa har lahira. Muhsin yana kar a bai ko waiwaye shi ba kai tsaye ya nufi Masarautar Huddam. *SHU'UMAR MASARAUTA* *42* *Littafin ku i ne 500 idan kina bu ata za ki biya ta wannan Account in Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.* Tun daga ranar da Fargi ta ziyarci bishiyar da suke bautawa ta fara horar da abin da yake cikinta tare da ba shi duk wata kariya, musamman da ya zaman ta bincika halwar tsafinta ta; ta san mace za ta haifa. A wani lokacin ta kan zauna jigum ta dinga tunanin makomar rayuwar abin da za ta haifa, fargabarta aya kada bayan ta mutu Shugaba ya cutar da abin cikinta, sai zuciyarta ta shawarce ta da ta dam a ta a hannun mahaifinta ko ta taso cikin kulawar mahaifinta don tana da tabbacin ko bayan ba ta raye zai kula da ita. A angare aya kuma wata zuciyar tata ta i ba ta ha in kan amincewa da haka. Wannan yanayin da ta tsiro da shi na killace kanta da tsafin da take yi wa cikinta, bai sa ta janye jiki daga wurin Shugaba ba don gudun kada ya zargi shirinta, kuma kusan kullin sai ya tunt e ta don ya ji shawarar da ta yanke amma kullin bagarar da shi take tana nuna masa har lokacin nazari take yi, shi kuma babban burinsa bai wuce ta dam a masa arfin tsafinta ba. Sannu a hankali Mahaifinta da manyan yayyanta suka fahimci yanayin damuwar da take ciki, watarana har sai da mahaifinta ya zaunar da ita ya tambaye ta dalilin da ya sa take ke e kanta kullin a bukkar da take gudanar da al'amuran tsafinta. Don ta kawar masa da shakku da damuwa sai ta nuna masa wasu manyan ayyuka take gudanarwa, a lokacin da mahaifiyarta ta ji haka ta tausaya mata matu a duk ita ma ba ta san abin da Fargi take aiwatarwa ba, amma haka kawai jikinta yake ba ta akwai dalilinta na yin haka don haka watarana ta ta a samunta a bukkar. A lokacin da mahaifiyarta ta shiga a zaune ta same ta gaban sihirtacciyar wutar da ke gabanta, da sauran tarkacen kayan tsafinta. Wani farin haya i ne yake tashi sai ya je kan allon farin arfen da take tsafi da shi sannan ya dawo ya shige cikinta, duk wani abu da take gudanarwa tana yin sa ne a kan abin da yake cikin jikinta. Shiru Mahaifiyarta ta yi tana kallonta sai da ta ga ta kammala sannan ta furta. "Ko ba za ki sanar da kowa ba ni mahaifiya ce, ki sanar da ni dalilin aiwatar da wannan sabon aikin da kike yi ba dare ba rana. Ko kina tsoron kada na yaye miki labulen sirrinki ne?" Cike da gajiya Fargi ta mi afarta ta fara yi mata tsami ta an jingina da bango. "Ko da ba za ta gaje ni game da al'amarun tsafi da sihirina ba, ina katange ta daga kaidin Shugaba da duk wani mai sharri. Na san waye Shugaba da zuri'armu, sanin kanki ne matu ar wannan cikin ya bayyana a gare su ba za su ta yale mu ni da abin cikina ba. Ko na haife ta kin san su da bibiya ba za su bar ta, akwai wani sirri da nake son sanar da ke dangane da yarinyar nan." Fargi ta yi shiru tana bin cikin jikinta da kallo, mahaifiyarta ta sauke ajiyar zuciya ta ce. "Ina sauraronki." "Yarinyar nan ta kasance maha i ce na kowanne matsafi ko gawurtaccan mai sihiri zai so ya mallake ta, babu wani boka da ba zai so ta zame masa tsanin da zai hau da zai kai shi ga tudun shahara da gawurta ba." "Ban ta a jin irin haka ba, wanne dalili ne zai sa ta zama haka shin kina nufin ba za ta samu sukunin rayuwa ba kenan?" Mahaifiyarta ta wurga mata tambaya. "Saboda taurarin abar bauta sun sauka a kanta, sara na yi a kan gaba a lokacin da na kai kokena gare ta. Ta zubar mata da jinin shanu marasa adadi, akwai muhimman sa onni a kanta, zan labarta miki ka an daga ciki idan dare ya tsala." Cikin gamsuwa da maganarta mahaifiyarta ta amsa mata, sannan suka ci gaba da hira. Dattijo Maharaz ya girgiza wa Kamalu kai sannan ya ce. "Sunan Mahaifinka Sarki Abdul'aziz, shi kuma Sarki Sulaimanu ai daban yake." "Amma me ye ala ar Sarki Sulaimanu da atan Jawahir? Ko dai akwai wani mummuna ala'amari da ya gudanar a kanta. Na rantse da girman Allah, matu ar aka same shi da hannu a atanta sarautar da yake ta ama da ita ba ta isa ta ba shi kariyar hukuncin da za a yi masa ba. Sai dai duk wani ruguntsumi da zai faru ya faru..." Murmushin Dattijo Maharaz ya katse Kamalu cikin mamaki Kamalu ya bi shi da kallo. "Ina ma za ka bari abin da yake asan zuciyarka ya bayyana a fili, ina ma ba wannan ha in Sarki Sulaimanu ya zartar ba, da kuwa tabbas ha in mabambamta zuri'ar nan sun yi daidai. Kwatankwacin yadda ake ora warya a gurbint." Kamalu sam bai fahimci maganar Dattijo Maharaz ba, yana shirin yin magana ya katse shi. "Sarki Sulaiman na tare da wata alfarma ko sirri wanda zai zame muku tamkar fitila da za ta haska muku hanya a cikin duhun dare. Yanzu abin da nake so da kai dai, idan Allah ya kaimu gobe zan samu mahaifinka mu yi magana da shi, kasan ba a shiga dawa haka nan dole sai an yi masa shiri." Jinjina kai Kamalu ya yi ya ji kusan kaso mai yawa na damuwar da yake ciki ta ragu, har Dattijo Maharaz ya mi e zai tafi Kamalu ya katse shi. "Jikina a sanyaye yake a kan wannan lamarin, ina tsoron kada abin da ya faru da ni ita ma ya kasance a kanta, wallahi ba za ta iya jura ba. Ni na san Jawahir farin sani, cika bakinta da tsiwarta a iya fatar baki ce. Don Allah ka yi wani abu farin jakada idan har za a cutar da ita." Kamalu ya arasa maganar cikin damuwa. "Ba a iya fatar baki wa annan kalaman naka suke fitowa ba, da alama suna fitowa daga cikin zuciyarka ne. Kusan abin da ya faru da kai ne ya faru da ita, sai dai suna da matu ar bambamci domin ita gida ta koma, ta koma tsatsonta ne sa anin kai da babu dangin iya ballantana na baba." A zabure Kamalu ya dafe irji ya ce. "Kana nufin ita ma 'yar cikin jinsinku ce?" Dariya sosai Dattijo Maharaz ya yi sai ya yi mai isarsa ya ce. "Idan hakan ne akwai wata damuwa ne?" "Allah ya sani na aminta da kai Dattijo Maharaz ban ta a rayawa a raina za ka fa a mini ba daidai, kuma wannan oyayyan sirri ne da babu wanda ya ta a jin sa daga gare." Sai da Kamalu ya tattaro jarumta murya a dashe ya ci gaba da cewa. "Tun da na bu i ido na fara jin wani irin yanayi a game da ita, zuciyata ta jima tana azabtuwa a aunarta sai dai a kullin rashin jituwarmu ta sa ban ta a gangancin bayyana mata sirrin da ke kwance a cikin raina ba. Dattijo Maharaz na jima da dulmiya kogin auna da soyayyar Jawahir, kogin da ya shallake rijiya gaba dubu a tsananin zurfi da nisa, kuma na yi tsalle babu adadi domin na fito daga ciki har yau ban samu nasara ba. Ko Kalaman Muhsin a kan soyayyarta ba su gigita ni tamkar yadda wannan furucin naka ya imauta duniyata ba, yanzu shi kenan aure ya haramta tsakanin da Jawahir Dattijo Maharaz?" Tausayin Kamalu ya kama shi, ya dafa kafa arsa sannan ya ce. "Ita bil'adam ce kamar kai Kamalu, kalamaina sun yi tsauri da ka fahimci abin da nake nufi kai tsaye. Ka bari za mu tattauna idan Allah ya kaimu." A sanyaye Kamalu ya amsa masa sannan suka yi sallama ya fice. Bayan fitar Boka Shaddas Shugaba ya sake kallon wurin da Jawahir ke tsaye tana hawaye ya ce, "Bu e mini