Sashe 5
Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
ke zuba daga asan Fulani Babba, kunamar na fara zu ar jinin Fulani babba ta yanke jiki ta fa i jikinta na wani irin karkarwa. Fulani Umaima ta saki shu'umin murmushi, sai dai kuma ganin jariran biyu ya sa ta samu shakkun wanda za ta aiwatar da mugun udurin a kansa, na farkon da jakadiya ta yankewa cibi ta na e a zani ta auka, take zuciyarta ta aita mata wata shawara. Kiran Baiwa Maimuna ta yi ta dam a mata shi, sannan ta arasa gaban ayan jaririn da ko cibiya ba a yanke masa ba. Wutsul-wutsul yake yana kuka ta auki kunamar da ke cikin jinin ta bu e bakinsa da arfin tsiya ta matse kunamar a cikin bakinsa. Take wani irin ruwa mai yau i ha e da jini ya fara iga a bakinsa. Kamar yadda yaro yake kama mama haka jaririn ya ri a tsotsar jini da ruwa mai yau in. Ya jima yana sha sannan jaririn ya fara wani irin kakari wani farin ruwa mai ha e da jini na fita daga hanci da bakinsa. Fulani ta waiga wurin Baiwa Maimuna ta furta, "Ina bu atar ki fita ta ofar baya a sirrince, ki samu aton kogi ki jefa shi ko kuma ki samu wani aton ramin ki binne mini shi. Duk rintsi kada ki bar shi da sauran numfashi, idan ba haka ba ranki zai yi mummunan aci." Baiwa Maimuna da jikinta ya gama sanyi ta ce, "An gama ranki shi da e." Har Maimuna ta yi gaba Fulani Umaima ta katse ta, "Iya ruwa fida kai. Kowa ya biya allonsa ya wanke. Ki tabbatar ba a samu matsala ba, wallahi matu ar asiri ya tonu sai kin gayyaci mutuwarki da bakinki. Ni da kika ganni ba na waina sai da zakara don haka ki bi sannu, shawara ce na baki don kar ki bari kwa arki ta yi ruwa." Baiwa Maimuna ta russuna rungume da jaririn ta furta, "Tuba nake ragamar damisa a ja ki da nisa. Na yi tsammanin kin fahimci somu-somun hauka zubda yawu. Mai afa aya ma ya yi rawa ballantana mai biyu? Indai ni ce har gaban abadan ba zan ta a baki matsala ba." Fulani Umaima ta saki malalacin murmushi ta furta, "Na aminta da ke Maimunatu, idan kin kammala komai ki samu Jakadiya akwai kyakkyawar kyauta. Amma ina bu atar ganinki da zarar kin kammala." Cike da girmamawa Baiwa Maimuna ta ce. "Godiya nake giwar Takawa fara mai farar aniya, sikari baki yi farin banza..." "Ba mu da isasshen lokaci ki hanzarta ki fita." Fulani Umaima ta katse ta a ta aice. Daga haka Baiwa Maimuna ta fita daga sashen Fulani ta ofar baya, cikin duhu haka ta ci gaba da tafiya tana ratsa bishiyoyi da ayoyi har ta samu ta fita ta can bayan Masarauta. Ganin har lokacin jaririn bai daina kakarin da yake yi ba ya sa Jakadiya ta dubi Fulani Umaima. "Ranki shi da e me zai hana mu arasa shi tun da har yanzu bai arasa mutuwa ba?" Da ido Fulani ta kafe jaririn. "Bamaguje bai ba ni damar haka ba, ki tsaya kawai mu zura wa sarautar Allah ido. Kuma ni kaina ba na son ya mutu yanzu, na fi son na dasa wa Fulani Babba acin ran da har ta mutu ba za ta manta da shi ba." Jakadiya ta jinjina kai a daidai lokacin da jaririn ya tsagaita da wannan kakarin, a lokacin Fulani Babba ta farfa o. Ta yun ura a hankali da niyyar tashi da yake jikinta babu wari sai Jakadiya da Fulani ne suka taimaka mata. "Sannu Yaya, barkanmu da arzi i Allah dai ya kawo mana Yarima lafiya." Fulani Umaima ta furta tana sakar mata murmushi, wani irin yammm take ji a jikinta kamar tafiyar kiyashi, jiki babu wari ta sakar wa Fulani Umaima murmushi. Idonta ne ya kai kan jaririn da ke kwance ta kafe shi da idanu, wani abu take son tunawa amma kanta ya yi nauyi ta gagara tunawa. Jakadiya ta saki gu a da arfi tana aukan jaririn da ilahirin jikinsa ya ha e da gumi, ga wani irin zafi zam a kan fatar jikinsa. Gu ar da Jakadiya ta yi ce ta alamta wa Dogaran da ke kewaye da sashen saukar Fulani babba, kafin wani lokaci tuni labari ya isa wurin Mai martaba. Fulani da Jakadiya tuni suka gyara jariri da mai jego, an turare akin da turaren wuta ko ina sai buga amshi yake yi. Sai dai Fulani babba tana are wa yaron kallo ta fahimci kamar idanunsa ba daidai suke ba, ga yawu da yake an ziraro masa ta gefen bakinsa hancinsa na yoyon majina. ura masa ido ta yi tana son tuna wani abu da ya shafi lokacin da take na uda har zuwa haihuwarta, sai dai nauyin da kanta ya yi ne ya haddasa mata ciwon kai ari aya take jin kamar zai tarwatse mata. A hankali ta kalli Fulani Umaima cike da murmushi, "Na gode sosai da kulawarki anwata." Fulani Umaima ta saki murmushin ya e don saboda rufewar ido har gani take babu abin da maganin Bamaguje ya yi wa jaririn, amma saboda kissa sai ta furta. "Haba Fulani babba me ye abin godiya ina ce da kai da kaya duka mallakar wuya ne?" Fulani babba ta jinjina kai cike da jin da i ta ce. "Amma kuma yaba kyauta tukwici in ji masu iya magana." "Ai lamarin tuwona maina aka yi, ni dai bari na wuce Fulani na ji asuba ta fara aratowa." Fulani Umaima na zuwa sashenta ta fa a gado cike da tashin hankali. "Ya zame mini dole na ziyarci Bamaguje kuma a yau ba sai gobe ba sai ya hallaka mini Fulani da abin da ta haifa, idan ba haka ba zuciyata bugawa za ta yi." Ta arasa maganar tana shiga cikin uwar akinta. Tafiya mai nisa Baiwa Maimuna ta yi har sai da ta yi nisa da masarauta, ta shiga cikin wani daji mai duhun bishiyoyi. Kuka jaririn ya fara yana wutsul-wutsul, banka a zanin ta yi ta ji tausayinsa ya mamaye zuciyarta. Da yake asuba ta yi haske ya fara mamaye cikin dajin, wani an rami ta hango da ke gefen wata murgujejiyar bishiyar kuka, kallon bishiyar kukar ka ai ya isa ya tsoratar da gangar jikin mammallakiyar wayar idon. Da sauri ta arasa wurin ta tsugunna sai a lokacin ta lura da zagayyan gidan tururuwar da ke wurin, taku ta fara jiyowa a an nesa da ita da sauri ta saka shi a ciki ta bar wurin ta oye a bayan wata bishiya, amma ga mamakinta sai ta ji shiru babu kowa. Gudun kada asirinta ya tonu ya sa ta fara zabga gudu ta nufi hanyar gida, a yadda take ji ba ta jin za ta iya kashe jaririn da bai ji ba bai gani ba, don rashin imaninta bai kai nan ba. Tana cikin gudun ta ji ta yi karo da wani abu garam! Har sai da ta fa asa. Tsoro, firgici da matsanancin tashin hankali ya mamaye ta, take jikinta ya hau karkarwa sakamakon ganin bishiyar kukar da ta kwantar da jaririn a gabanta ta tsaya dass kamar yadda ta baro ta a baya. _Ummou Aslam Bint Adam_ 07062062624. *SHU'UMAR MASARAUTA*