Sashe 39
Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ko a fuska ba ta musa ba. A ranar da Fulani Asabe za ta koma a ranar suka wuce tare da Fulani Umaima. Fulani Umaima tun tasowarta fitsararriyace ga rashin tsoro duk wani abu da za ka yi mata baraza da shi ba zai tsorata ta ba. Uwa-uba kafiya, taurin kai ta taurin zuciya. Tana da matu ar wayo sosai don lokaci aya ba za ka ta a gane ainihin halayya da abi'unta ba, tun ba ta kai haka ba ta iya makirci, kissa da kisisina saboda ko a cikin Masarautarsu Mahaifiyarta ba ta jin ko ar a game da ita, kuma duk cikin 'ya'yanta ta fi ji da ita. A ranar da ta fara tozali da Sarki Abdul'aziz a ranar kwana ta yi tana ayyana abubuwa da dama a cikin zuciyarta, a yadda zuciyarta ta yi nisan kiwo a kansa ba ta jin za ta iya rabuwa da shi kamar yadda Fulani Asabe ta ce za su yi auren jeka na yi ka. Sannu a hankali sai ta fara shige wa Fulani babba tana yi mata hidimar an aikace-aikace da taya ta hira, da farko daga Mai babban aki har Fulani babba babu wanda ya saki jiki da ita, sai daga baya da suka ga yanayin kyawawan abi'un d Umaima ta nuna musu sai suka sako jiki da ita. Makwan Umaima takwas Fulani Asabe ta ba ta wani farin kwalli ta ce ta saka shi kuma ta tabbatar da sun ha a ido ita da Sarki Abdul'aziz, da i ya lullu e Umaima har murnarta ta bayyana a fili. "Ba na son sakarci fa, kada ki auka auren jinda i da kwanciyar hankali za ki yi." Da kamar Fulani Umaima ta musa amma sai ta alo murmushi ta furta. "Ba ina yin murmushin saboda wata manufa ba Inna, ina sakin murmushin murna da jin da in ganin mulki da sarautar gidan nan sun kusa dawowa tafin hannunmu ne." Fulani Asabe ta saki murmushin farinciki. "Shi ya sa nake aunarki uwar akina." Shiru Fulani Umaima ta yi tana bin Fulani Asabe da kallon ba ki da hankali, don haka ta sake kwantar da kanta har lokacin da Allah ya ha a fuskarta da Sarki Abdul'aziz. A ranar da ya yi tozali da ita a ranar ne ya yi tattaki har zuwa wurin Mahaifinsa da maganarta. Bai hana shi ba don ganin shi ne shugaba kuma wakilin Masarauta, don haka cikar kamalarsa za ta aru ne idan ya tara iyali sama da aya. A lokacin da Mai babban aki ta samu wannan labarin ranta ba aramin aci ya yi ba, don haka kawai ta ji Umaima ba ta kwanta mata ba, take ta nuna wa Sarki Usman rashin amincewarta amma sai bai ba ta goyon bayan ba. Duk wannan abin da yake faruwa Fulani babba ba ta san wainar da ake toyawa ba, sai dai ta lura da sauye-sauye tsakaninta da Maigidanta. Ya bijiro mata da sababbin halayen da ba ta san da su ba kamar; kyara, hantara, yawan fa a, saurin fushi da aurace mata, amma gudun tashin hankali a tsakaninsu sai ta ri a takatsantsan. Amma kuma ta yi mamaki matu a da ta ga Umaima ta janye afarta daga shiga sashenta har sai da watarana ta ta a aika bayinta su gano mata ko lafiya kwana biyu ba ta zo mata ba. Duk da sa on da Fulani babba ta tura wa Umaima bai sa ta taka ta je ba domin a ganinta ai bu atar maje hajji sallah, bu atarta ta riga da ta biya babu sauran wahalar da kai. Lokacin da Mai gado ta ji sa on kiran Fulani babba da halin da take ciki ba aramin ka uwa ta yi ba, zani daban riga daban ko ankwali ba ta aura ba ta ora mayafinta a kanta ta fice. "Ko dai abin da yarinyar nan ta fa a gaskiya ne?" Mai gado ta ayyana a zuciyarta. Kamar za ta tashi sama hake take zabga sauri tana shirin gifta ofar Fulani Umaima ta ji an furta. "Keee!" Cak Mai gado ta tsaya cikin saranda ta waiga. "Allah ya taimaki ranki shi da "Ina za ki je?" Fulani Umaima ta tambaya don son jin halin da Fulani babba take ciki. "Tuba nake ranki shi da e, Fulani ce ta aika na zo da gaggawa ba ta jin da i." Wani sanyi ya ratsa zuciyarta amma sai ta fuske. "Idan kin gama da sashenta ina son ganinki." Rass! Gaban mai gado ya fa i don ko ka an ba ta san wata ala a da za ta shiga tsakaninta da Fulani Umaima musamman da ya zama duk cikin Bayi Fulani babba ta fi aminta da ita. "An gama ranki shi da e, ki huta lafiya." Mai gado ta furta a sanyaye sannan ta wuce bayan Fulani Umaima ta sallame ta. "A gafarce ni uwar akina idan na yi jinkirin zuwa." Mai gado ta yi magana tana arasawa jikin gadon Fulani babba zuciya a tsinke. A madadin Fulani Babba ta iya tanka mata sai kawai ta fashe da matsanancin kuka, hankali a tashe Mai gado ta matsa gabanta idanunta suka ciko da walla. "Uwar akina akwai abin da yake damunki ne?" Sai da Fulani babba ta yi kuka mai isarta sannan ta sanar da Mai gado duk abin da yake faruwa, ban da hawaye Mai gado babu abin da take yi, da yar ta iya aga Fulani babba ta jingina da bango ta sauya mata kayan jikinta ta aura mata alwala tana yi tana zubar da wallah. "Ranki shi da e mai zai hana a aika da takarda asar Rumm a sanar da Yadikko halin da kike ciki?" Fulani babba ta kalli Mai gado tana son ta girgiza kanta amma ta kasa. "Mai gado... mahaifiyata girma ya kamata, ga Yaya Halima da ke gabanta tana fama da lalurar hauka. Idan na sanar da ita hankalinta zai ara tashi." Mai gado ta share wallar idonta tana shirin yin magana Fulani babba ta ci gaba da cewa. "Ban sanki ba, ban san daga inda kika fito ba Mai gado, amma duk cikin masarautar nan da ke ka ai na aminta." Kuka ya ci arfin Yaya babba, Mai gado ta share mata hawaye duk da ita ma kukan ya gagara tsagaitawa daga wayar idonta. "A halin da nake ciki jikina yana ba ni ajali ya kusanto ni, tawa ta zo arshe. Don Allah ko bayan rayuwata ki kula mini da Abubakar, na san wannan wahalallan al awari ne na dam a miki domin ba ki da ikon kanki wata ila ma a hana ki shiga al'amuran shi. Amma idan har kin samu dama ki kula mini da shi, na bar shi a hannun Allah da hannunki Mai gado." "Ranki shi da e cuta ba mutuwa ba ce, ki daina fa in haka In shaa Allah za ki samu lafiya." Murmushin ya e Fulani ta saki. "Na yi jinya kala-kala Mai gado, na gamu da cutuka mabambam amma wannan ciwon da na wayi gari da shi daban yake da sauran." Lokaci aya wani irin tari ya turnu e Fulani babba, ta fara kwara wani irin ba in aman jini mai wani irin wari. A ru e mai gado ta kira Baiwa Zainaba suka fara gyra Fulani babba, a lokacin tuni zuciyar Mai gado ta gama karyewa. Sai bayan wani lokaci Fulani babba ta dawo hayyacinta, Zainaba da Mai gado sai share walla suke don duk wanda ya ga halin da take ciki sai ya tausaya mata. "Ranki shi da e na aika Zainaba wurin Takawa ba ta same shi ba." A wannan karon muryarta ta sake yin asa sosai. "A sanar da Jakadiya idan ya dawo ta sanar da shi halin da muke ciki." Da sauri Baiwa Zainaba ta fita ta samu Jakadiya ta sanar da ita halin da Fulani take ciki. Kamar wacce aka yi wa kyautar Aljanna haka farinciki ya lullu e zuciyar Fulani Umaima, ta koma cikin sashenta cikin murna tamkar ta zuba ruwa a asa ta sha. Uwar akinta ta fa a ta tsinci kanta da auko akwatin da ta adana littafin labarin Hidaya, sai da ta auko aurarriyar fatar da Bamaguje ya bata ta juya a hannunta tana sakin dariyar eta sannan ta mayar ta auko littafin. Sai da ta jingina da bango ta bu e shafin da ta tsaya sannan ta ci gaba da karantawa. Ban san me ya ba wa Sarki Hafiz dariya a cikin tambayata ba don haka na kafe shi da idanu ina kallo, sai da ya an saita nutsuwarsa ya dube ni yana fa in. " A tsammanina ko ka an bakya daga cikin wani jinsi bayan na bil'adama. A labarin da Kakana ya ba ni wanda shi kansa ya ce kusan labari ne na kunne ya girmi kaka, mahaifiyarki ta kasance 'ya daga wurin sarkin wanzamin garin nan wato Bala wanzam. Su biyu ne 'ya'yansa daga mahaifiyarki sai an uwansa Shamsu, tun tasowar Mahaifiyarki mace ce mai sanyin hali da kyakkyawar mu'amala. Shi kuma mahaifinki ya fito daga zuri'ar Bargi wa ansu mutane ne da ke rayuwa a ga ar tekunan da ke kewaye da su, wa annan al'umma al'amuransu na da matu ar ban mamaki sakamakon ba sa rayuwa a ko ina sai ga ar teku, kuma duk hunturu ba sa barin wurin. Kuma an yi zargin mahaifinki jika ne ga sarkin ruwan yankin Dahwan, a yadda Kakana ya ba ni labari watarana wani masunci ne ya zo da 'yarsa ga ar yankin da zuri'ar Mahaifinki suke zaune, sun yi mu'amala da arzi i da shi yana shiru ruwa da zummar ya yi su, sai kwalakwalensa ya kife da shi. Duk iya ruwa da warewarsu da kogi ba su iya samo mutumin ba, dalilin haka ya sa mahaifin kakanki ya auki yarinyar da ya bari ya ci gaba da rainonta har ta zama budurwa Kakanki ya aure ta. "Idan na fahimta kenan babu wanda ya asan asalin Kakata kenan?" Na katse Sarki Hafiz daga bayanin da yake yi mini sai dai ko ka an kwanyata ta gagara jera kalmominsa a ma'aunin da suka dace. "Mutane da dama sun yi harsashe sai dai har kawo wannan lokacin babu amsa wara kuma mai tushen da za a kafa hujja da ita." Ajiyar zuciya na