Sashe 89
Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read
ya ce a nan aka aura aurensu suka yi bincike sannan suka aminta da ita, ya zayyana musu irin kisan zalincin da aka yi wa Fargi da halin da Jawahir ta yi yun urin shiga duka a sanadinsa. Nan take Mai babban aki ta gane kuskurensu na in barinsa ya auri za insa, suka rungumi Jawahir cikin soyayya da kulawa sai dai daga angaren matansa iri- iri suka nuna kishinsu a fili, sai Sarki Sulaimanu da Mai babban aki suka tsawatar musu sannan suka sauko kuke kulawa da ita. Bayan da suka kwana biyu suka huta ne kuma aka fara shiga da Jawahir cikin dangi 'yan uwa da abokan arzi i, Jawahir har mamaki take yi ganin irin gatan da take samu, a angare aya kuma idan mutuwar Malam Umaru ta fa o mata sai ta shiga aki ta ci kuka ta more. "Wai ni ma 'Yar Sarki?" Ta wurga wa kanta tambaya tana sakin murmushi, kallon al aryar da take ciki take tana jinjina irin wahalhalun da bayi suke sha don jin ta take tamkar a cikin aljanna. "Ranka shi da e! Don Allah wata alfarma gar ni." Sarki Sulaimanu ya zuba wa Jawahir ido cikin tsananin soyayya, don jin Jawahir yake ta fi dukkan 'ya'yansa samun fada a zuciyarsa. "Muna sauraronku tafi a kai tsaye Jawahiruna." "Don Allah a dinga kula da rayuwar Bayi da halin da suke ciki, ranka shi da e a dinga duba cima da wurin makwancinsu. Na taso cikin angin bauta da Bayi, na san wahala da rashin 'yanci da ke cikin rayuwar Bayi da 'ya'yansu idan da hali a dinga kyautata musu ko da ba za su kai matsayin iyalin Sarki ba. " Jawahir ta sauke numfashi ta ci gaba. "Ba iya Masarautar Huddam ba, a wannan gidan ma na ga irin rayuwar da na fuskanta a baya. Don Allah a tausaya musu domin suma 'ya'ya ne kamar mu." Murmushi Sarki Sulaimanu ya yi jin yadda take zayyana zance tamkar mahaifiyarta. "Tabbas barewa ba za ta yi gudu anta ya yi rarrafe ba. Fargi ba za ta ta a gogewa daga zuciyarmu ba har sai mun daina numfashi, In shaa Allahu za mu kyautata wa Bayi kamar yadda kuka bu ata, za kuma mu wae musu rana guda a mako domin sha ata." "Godiya nake ranka shi da e." Jawahir ta furta cikin girmamawa. Bayan Wani Lokaci Kamar yadda Sarki Sulaimanu ya al awarta bayan da su Jawahir suka samu kwanaki masu yawa, suka shirya da kayan alfarma tare da tsarabar sha tara ta arzi i suka nufo Masarautar Huddam ha e da maganar auren su Kamalu. Jawahir na zuwa Sashen Mai gado ta nufa da gudu ta rungume ta sai da ta suka an sha kukansu na rashin Malam Umaru, suka sake jajantawa kansu sannan ta shiga ba ta labarin duk abin da ya faru. Bayin cikin masarautar manya da yara suka shiga tururuwar zuwa ganin Jawahir, nan ta fara ganin kulawa da soyayyar da suke nuna mata. Wasu daga cikinsu har mamakin yadda suke haba-haba da ita take. akin Abubakar ta shiga ta same shi a zaune, yana ganinta ya sakar mata murnushi alamun ya gane ta, a hankali ya yun ura ya fara tafiya yana an layi kamar zai fa i har ya arasa wurin Jawahir. Da i ne ya kamata ganin jikin Abubakar ya ara kyau don Sarki Abdul'aziz ya dage da nema masa magani sosai, gwaranci ya shiga yi mata tana biye masa suna ciki haka Ru ayya ta shiga suka ci gaba da hira. Kafin su Sarki Abdul'aziz su zauna tsayar da maganar aurensu Kamalu sai da ya aika aka kira Kamalu, Muhsin da Jawahir. "Ba tun yau ba Jawahiruna na ce ba zan yi miki auren dole ba, don haka na sa a kira ki don na ji ta bakinki shin kina son Muhsin." Dire kalaman Sarki Abdul'aziz suka yi daidai da bugun irjin Kamalu. A razane ya ago yana kallonta ta sunkuyar da kai asa idanunta suka ciko da walla ba tare da ta amsa ba. "Duk yadda kuka yanke daidai ne ranki shi da e." Ta arasa maganar hawaye na zuba. "Jawahir a yi magana muna sauraronki ke za ki zauna da shi ba mu ba." Cewar Sarki Abdul'aziz don ya ji da in yadda Sarki Sulaimanu ya yi masa kara. "A gafarce ni ranka shi da e amma Jawahir ba ta son Muhsin." Kamalu ya furta kai tsaye. Daga Sarki Sulaimanu har Sarki Abdul'aziz idanu suka zuba masa, ya sunkuyar da kai asa ya furta. "Na san Jawahir farin sani ba tun yanzu ba wallahi ba ta son Muhsin..." arya kake munafuki." Muhsin ya katse shi a harzu e. Murmushi irin na manya Sarki Abdul'aziz ya yi ya ce. "Tsakanin Kamalu da Muhsin wa kike so?" Da sauri Jawahir ta ago ta dubi Kamalu, ta yi saurin goge hawayenta ta saki murmushi ta sunkuyar da kai asa. "Kamalu kike so?" Ya sake wurga mata tambaya, da sauri ta gya a kai sannan ta fice daga akin tana dariya. "Za mu aura miki wanda kika so Jawahiruna saboda haka ku tashi ku ba mu wuri." "Dama ni na jima ina ganin bambamci ai, ni na san ba aunata ake yi ba idan ba haka ba ai har mahaifiyata da tuni an fito da ita. Kuma wallahi babu wanda ya iya ya hana ni aurenta." Muhsin ya yi magnanar yana fita daga akin. "Matu ar muna numfashi za mu aura wa Jawahir za in ranta, duka 'ya'yana ne amma kowa na san nutsuwa da abu'unsa. Amma muna neman alfarmar a aga mana bikin nan zuwa makwanni biyar masu zuwa, sakamkon muna jiran Mai gado saura kwana hu u ta fita daga Takaba. In shaa Allahu akwai aikin alkairin da za mu zartar a kanta." Sarki Abdul'aziz ya furta yana murmushi. "Ranka shi da e da alama kai ma sharce amarcin kake shirin yi, shi ke nan babu damuwa Allah Ya nuna mana." Gaba aya suka saka dariya. Takaicin da ya kama Muhsin kai tsaye sashen angaren akin duhu ya nufa, yana tafe yana hawaye ko gabansa ba ya gani duk wurin da ya wuce kallonsa Bayi suke yi. Tsayuwarsa a wurin ofar ya ga yadda Mahaifiyarsa ta sake lalacewa, on kanta ya yi wa ansu mula-mulan uraje, da alama duk sun uri ruwa. Basiru ya hanga tsaye a gabanta da wata kaifaffiyar askar, duk yadda Fulani Umaima take yi masa ro o da magiya bai saurare ta ba. Askar ya mi a da niyyar ya yanki kunenta Bamaguje ya dira a gabansa, daga fuskarsa har jikinsa a daddauje yake, sai taintsiyar hannun Bamaguje da take a guntule. Kafin Basiru ya yi wani yun uri Bamaguje ya auke ta suka ace, Fulani Umaima ta shiga walla arara tana fa in ya sauke amma ko ta kanta Bamaguje bai bi ba, ganin haka ya harzu a Basiru ya kwarara ara shi ma ya rufa masa baya, ya ace nan take. imauce Muhsin ya yi cikin gida ya sanar da mahaifinsa halin da ake ciki, Sarki Abdul'aziz shi da Sarki Sulaimanu ne suka je wurin tun a nesa suka dakata saboda wari, ya saka Dogarai suka duba akin sai dai babu Fulani Umaima babu dalilinta, sai Jakadiya da take galabaice cikin dagwalon azanta. Takawa ya bayar da umarnin a fito da Jakadiya a sallame ta daga Masarautar Huddam. Komawarta sashen Mai gado ta ji jikinta ya auki umi, daga tsakiyar cikinta ta ji ya fara aukan zafi. Tana aga rigarta ta ga tambarin bishiyar abar bauta ya sake bayyana, ta bu e baki za ta yi magana kenan ta neme shi ta rasa. "Ko dai idanuwana ne suka niyyar yadarata?" Jawahir ta wurga wa kanta tambaya. "Da zarar kin sake ganin wannan tambarin na cikinki, ki tashi ki aura alwala ki fara karatun al ur'ani, kuma ki sanar da Maharaz ya sanar da ni." Jawahir ta tuno kalam Babban Malami na baya a cikin kunnuwanta. Ajiyar zuciya Nimrah ta sauke bayan ta rufe aton littafin da take karanta wa awayenta su Intisar, wanda a bayansa aka rubuta SHU'UMAR MASARAUTA da babban ba i. Ta kalli su Nihal da ke gabanta ta furta. "Kun san dalilin da ya sa na fara rubutu har na zama marubuciya da ma asudin rubuta lattafin nan?" "Amma dai ba kina nufin labarin ya are ba?" Nawwarah ta tambaya tana kwa e fuska. "Sai kun ba ni amsar tambayata." Nimrah furta tana rungume aton littafin a irjinta. Cikin ha in baki suka furta mata. "A'a Sister Nimrah sai kin fa a." don sun damu su ji daga gare ta. "Ranar da Umma ta ba ni labarin Mahaifiyarta! Saboda labarin cike yake da almara, zalinci ban tausayi da ta a zuciya." Nihal ta yi sauri fa in, "Wai kina nufin Jadda dai kakarku ita ce Jawahir in da kika karanta mana labarinta?" Dariya Nimra ta yi ta ce, "Kina mamaki ne?" Lokaci aya suka gya a mata kai. warai kuwa ita ce, don kafin na fara rubutun labarin nan sai da na je na sake jin komai tiryan-tiryan daga bakinta sannan na rubuta shi." "Lallai ashe Jadda ta ga duniya. Amma don Allah da gaske labarin a nan ya are?" Intisar ta tambaya kamar za ta yi kuka. Mi a mata littafin Nimra ta yi ta ce, "Ga shi nan ki duba idan arya nake miki." Marairaice murya Intisar ta yi ta ce. "Amma bayan tafiyar Fulani Umaima ina Bamaguje ya kai ta? Ya suka arke da Basiru? Kuma wai a ciki wa Jadda take aura Muhsin Ko Kamalu? Ni fa duk tarzomar da aka yi ban ji kin ce Sarki Abdul'aziz ya saki Fulani Umaima ba, kuma wane ne ya gaji Sarki Abdul'aziz? Wai ya aka yi aka kwana a ragaya?" Nimra ta aka mata duka a cinya ha e da mi ewa tsaye ta ce. "Sannu 'yar Jarida sai ki bari na yi sallar magariba na dawo, kin san dai kullin hu ubar Mai martaba kenan a dinga sallah a farkon lokacinta." Nimrah ta arasa maganar tana ficewa daga akin, Intisar da Nihal har rige-rigen aukar littafin suke yi. Nihal ta sake duba bangon littafin a fili ta furta. "SHU'UMAR MASARAUTA. Labari mai almara da tsaya wa a rai." TAMMAT BI HAMULILLAH Ina
matu ar godiya ga Allah S.W.A da ya ba ni ikon kammala wannan littafi na SHU'UMAR MASARAUTA. Gadiya mai tarin yawa a gare ku masoya wa anda suka sa ku insu suka sayi littafina wannam ma soyayya ce, ina mai jinjina muku bisa yadda kuka auki kwanaki kuna bibiyar littafin nan Allah ya bar auna. Na ce ba 'Ni maYar adam ce wato tara dai nake ban cika goma ba, na tabbata kun ga kurakuran da ba a rasa ba a yafe ni, kuskuren ciki Allah ya yafe mana darasin da ke cikin labarin Allah ya ba mu ikon auka. *DON ALLAH DON GIRMAN ALLAH DA ZATINSA, DON SOYAYYAR DA KUKE WA ANNABI MUHAMMAD S.A.W KADA KU HA A MINI DOCUMENT ZAN HA A DA KAINA, DON ALLAH BA DON NI BA."* Ummou Aslam Bint Adam F H J H J Calibri Calibr SimSun Times New Roman Times New Roman Light Light DengXian Cambria Math Cambria Math !%),.:;>?]} $([{ _GoBack SummaryInformation DocumentSummaryInformation WpsCustomData TECNO KF7j TECNO LD7 WPS Office 2da4ca90c267461eb7149dff6a581959
matu ar godiya ga Allah S.W.A da ya ba ni ikon kammala wannan littafi na SHU'UMAR MASARAUTA. Gadiya mai tarin yawa a gare ku masoya wa anda suka sa ku insu suka sayi littafina wannam ma soyayya ce, ina mai jinjina muku bisa yadda kuka auki kwanaki kuna bibiyar littafin nan Allah ya bar auna. Na ce ba 'Ni maYar adam ce wato tara dai nake ban cika goma ba, na tabbata kun ga kurakuran da ba a rasa ba a yafe ni, kuskuren ciki Allah ya yafe mana darasin da ke cikin labarin Allah ya ba mu ikon auka. *DON ALLAH DON GIRMAN ALLAH DA ZATINSA, DON SOYAYYAR DA KUKE WA ANNABI MUHAMMAD S.A.W KADA KU HA A MINI DOCUMENT ZAN HA A DA KAINA, DON ALLAH BA DON NI BA."* Ummou Aslam Bint Adam F H J H J Calibri Calibr SimSun Times New Roman Times New Roman Light Light DengXian Cambria Math Cambria Math !%),.:;>?]} $([{ _GoBack SummaryInformation DocumentSummaryInformation WpsCustomData TECNO KF7j TECNO LD7 WPS Office 2da4ca90c267461eb7149dff6a581959