← Book details Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 89

Sashe 49

Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da zai hallakar da ita a ruwan sanyi amma hakan bai samu ba. A lokacin da Fargi ta kai shekara goma sha uku ta fara zama budurwa, kyawun sura da na halitta suka bayyanar mata. Ba a ce ba can sosai ba, sai dai doguwa ce tana da tsayi ba ta da kauri sosai. A wannan lokacin cika da asaitar tsafinta ta tunbatsa don haka samarin cikin zuri'arsu suke shakkar tunkararta da niyyar ulla soyayya, sakamakon tsoron kada ta fusata har ta auki mummunan hukunci a kansu. A na cikin wannan yanayin kwatsam Boka an tani ya kawo an sarkin asar Bahdi wurin Shugaba a kan ayi masa aikin da za a hallaka yayansa idan ya so ya gaji karagar mahaifinsa. Shugaba Zurufu duk yadda ya so ya buga aikin Sulaiman sai lamarin ya gagare shi sakamakon shi ma Yariman da aka kawo mahaifiyarsa a tsaye take tsayin daka wurin tsubacce-tsubacce, a wani binciken da ya yi ma ya gano shi da kansa ya yi wa mahaifiyar Yariman aikin da Mahaifinsa zai yi murabus ya dam a masa. Ganin babu nasara ya sa Shugaba ya sallami Sulaiman ba tare da yin nasara ba, a sanyaye ya fito daga kogon dutsen ya hange ta a tsaye a jikin dokinsa tana aiwatar da an tsafe-tsafenta da fuskar dokinsa. Idan ta shafa fuskarsa sai ta koma zuwa da saniya, agwagwa, zaki, kura da duk sauran kayan namun dajin da take bu ata. "Idan aka bar shi da fuskar damisa yau ina na kama?" Sulaiman ya yi maganar cikin zolaya. Waigowa ta yi ta sakar masa murmushi. "Sadaukin namiji ba a san shi da jin tsoro ba. Kai da kake burin zama Sarkin Bahdi dole ka janyo bargon jarumta ka lullu awa kanka." Kallon mamaki ya bi ta da shi, ta an matsa daf da shi. "Za ka samu sarautar Masarautar Bahdi indai da yawan numfashi amma kuma sai dai ba ta sigar da kake bu ata ba." A karo na biyu ya sake zuba mata idanu da matsanancin mamaki. Kasancewar duk wasu masukantan Fulani babba sun hallara, gari na an washewa aka fito da gawar Fulani Babba, dubannan mutanen manya da yara ne suka sallaci gawarta sannan aka wuce da ita gidanta na gaskiya. Sarakuna daga asashe da dama ne suka ziyarci Sarki Abdul'aziz domin yi masa ta'aziyyar rashin uwar gidansa, kuma uwar 'ya'yansa. Ilahirin mutane gidan kowanne ka dube shi cikin alhini da jimamin mutuwar Fulani babba yake, Abubakar da ke akinsa sai bin mutane yake da kallo ba tare da ya san abin da yake faruwa ba. Abu aya yake yi kuka idan ya ji yunwa ta dame shi, kuma da ya ga ba in fuskar ba bai saba gani ba sun shiga akinsa sai ya fara bige-bige yana son cakumo mutum. Mahaifiyar Fulani babba ban da kuka babu abin da take musamman da ta kalli Abubuwar, Su Khadija kowacce ta zo da 'ya'yanta amma kallo aya za ka yi musu ka fahimci suna cikin matsananciyar damuwa. Mahaifiyar Fulani Umaima da 'yan uwanta ba su iso ba sai bayan da aka kai gawar Fulani Umaima, kallo aya mahaifiyarta ta yi mata ta fahimci akwai wata a asa game da mutuwar Fulani babba. "Ba ni labari yadda aka haihu a ragaya don ganin fuskarki ka ai ya tabbatar mini akwai wata a asa." Mahaifiyarta ta furta bayan sun shige uwar aki da Fulani Umaima. "Aikin Bamaguje ne, kin san ko shugaban she anu haka ya gan shi ya yale." Umaima ta furta. "Ni shaida ce don yanzu haka jiya mahaifinku ya tsayar da ranar da zai yi murabus ya dan a wa an'uwanki Muhammad." Murmushi Fulani Umaima ta saki sannan ta furta. "Amma fa ina da gagarumar matsalar yanzu dai tun da a cikin kacaniyar mutuwar nan ake zan ziyarci Bamaguje." "Wannan karon ba ke ka ai za ki ziyarce shi ba domin ni kaina akwai abin da ya fara ci mini tuwo a warya." Hawaye ne bibbiyu yake zuba a idanun Mai gado da ke gaban gadon da Jawahir take kwance, jikinta ta auki zafi zauuu sai sauke numfashi take sama-sama. Da alama bacci take amma kallo aya idan ka yi mata za ka fahimci a galabaice take, gaban Mai gado na fa uwa ta kai hannu a hankali ta yaye rigar Jawahir. Dam! irjinta ya buga da arfi har sai da ta sa hannu biyu ta dafe irjinta, tambarin cikin Jawahir ne ya fito jawur tamkar garwashin wuta. "Kin sa a umarnina Jawahir! Ina hango abubuwan da ke ba za ki ta a hango su ba, amma duk da haka hannunka ba zai ta a rubewa ka yanke ka yar ba. Ba ni hannunki Jawahir." Mahaifiyarta ta furta tana mi a wa Jawahir hannu. A an tsorace Jawahir ta fara takawa har zuwa gabanta, gabanta na fa uwa ta mi a mata hannunta na hagu. Da arfi mahaifiyarta ta fisgi hannunta sannan ta fara tafiya da ita har ta isa bakin bishiyar da Fulani Umaima ta binne butar da Bamaguje ya bata. "Ki ha o butar nan ji ki je ki ebi ruwan rafin tsamiya, ki je sashen Umaima ki zuba asirin jikin Takawa zai wargaje gaba aya. Sannan ki auki butar ki dam awa Kamalu ita ragowar aikin zuri'ar da ke tare da shi za su nusar da shi abin da zai yi a gaba. Kuna da matu ar tasiri dangane da junanku sai da arashin ruhi ne ke tsaurara tsattsamar ala a a tsakaninku." Mahaifiyarta ta arasa ta dam i wuyan Jawahir da arfin gaske har sai da ta fara wani irin kakari idanunta suka firfito waje numfashinta na yun urin aukewa sannan ta sake ta; ta ci gaba da cewa. "Na yi rantsuwa da girman shahara da fifikon tsafin da na fi gaba aya zuri'ata matu ar kika kuskurewa umarnina sai na hallaka ki da tafukan hannuwa, domin ba zan iya jurar a salwantar da rayuwarki ba tare da cikar muradina da na mahaifinki ba." Wani irin kakari Mai gado ta ji Jawahir tana yi numfashin na arin aukewa, tana shirin tashinta Jawahir ta tashi firgigit a galabaice tana sauke ajiyar zuciya idanunta sun firfito. Hannu biyu Jawahir ta sa a wuyanta ta ri e har lokacin ba ta daina sauke numfashi ba. "Sannu Jawahir jikin ne?" A hankali Jawahir ta girgiza mata kai, "Inna shi kenan Fulani ta mutu?" Jawahir ta yi wa Mai gado tambayar don ta kawar da hankalinta, sai da Mai gado ta share hawaye sannan ta furta. "Jawahir har abada ba zan daina kukan rashin Fulani ba." Jawahir ta mi e a hankali ta auki mayafinta ta ora a kafa "Ina kuma za ki jawahir ke da zazza i bai gama sauka daga jikinki ba." "Inna yanzu nan zan dawo." Jawahir ta yi maganar tana ficewa daga akin. Tana tafe gabanta na fa uwa sai raba ido take cikin matsanancin tashin hankali, kallo aya za ka yi mata ka fahimci ba ta cikin nutsuwarta a haka har ta arasa sashen Sarki Abdul'aziz da ke cike da 'yan gaisuwa. Ta bayan sashen sha atawarsa ta zagaya a lokacin babu kowa take tsoro ya sake mamaye ta, daga can bakin wata bishiya ta hangi asanta na fitar da haya "Ga wurin can, ki yi gaggawar tonewa kada ki ata lokaci." Ta ji muryar matar da ta yi mafarki da ita ra au a cikin kunnuwanta, da sauri ta arasa ta fara tonowa ba ta auki lokaci mai tsayi ba ta tone butar nan take ta ji wani irin yammmm tsigar jikinta na tashi. Kai tsaye rafin tsamiya ta nufa ta ebi ruwan ciki tana mi ewa ta ga wurin yana juya mata, runtse idonta ta yi ta ji kamar ana tafiya da ita a saman iska. Tana bu e idonta ga mamaki ta hange ta a soron sashen Fulani Umaima, a cikin mayafinta ta oye butar irjinta na bugawa matsanancin tsoro ya mamaye ta. Tana nan tsaye lokaci aya ta ji butar arfen ta fara aukan zafi, tamkar ana neman a kwaci butar haka ta fara ji. Tana son aga afarta don ta shiga tsakar gidan Fulani Umaima amma yadda ake fusgarta na neman gargararta. Sai da ta yi da gaske sannan ta iya shiga cikin sashen, ta fara zubawa. Duk wurin da ta zuba ruwan butar sai dai wani ba in haya i ya tashi, tana gama zubawa da sauri ta fice daga sashen gabanta na tsananin bugawa. Murmushi auke a saman fuskokinsu suka arasa cikin kogon dutsen Bamaguje, daga can saman dutsen suka hango shi a tsaye ri e da sandar tsafinsa saboda tsufa ya ran wafa sosai jikinsa sai karkarwa yake. Fulani Umaima ta dubi mahaifiyarta tana sakin murmushin don rabon da su kawo wa Bamaguje ziyara a tare a alla an doshi kusan shekara Talatin, Mahaifiyarta ta fara yin gaba ita kuma tana biye da ita. "Tsafi ya ja linzamin dokin shugaba har zuwa arshen rayuwa, ina gwanin wani ga nawa? Ina mai aryata tsafi ya zo ya ga tushen wurin da ake gudanar da gundarin tsafi. Ka da e ka yi arko da shekaru irin na dabina Bamagujena, ina ananan Bokaye da 'yan tsubbu ga shugabanku. Wa ya isa ya ja da kai yanzu a ga arshen rayuwarsa! Na gaishe ka madogarata mai yaye mini damuwa da share mini hawaye." Mahafiyar Fulani Umaima ta arasa kirarin tana zubewa a gabansa. Fuskarsa a murtuke babu ko igon fara'a ya ago ya kafe Fulani Umaima da kallo. Tana shirin yi mata magana ya saka hannu ya auke ta da matsanancin mari, a yadda yake idan ka ga Bamaguje sai ka rantse idan ya mari mutum ba zai yi wani tasiri ko zafi a jiki ba. Azabar marin ta sa Fulani Umaima ta kusa zubewa, kafin ta kai asa ya sake auke ta da wani marin. Hankali a matu ar tashe Umaima da mahaifiyarta suka kafe Bamaguje da kallo, musamman Umaima da ta san laifin da ta aikata dangane da salwantar da littafin hannunta. Da sandar hannunsa ya nuna Umaima nan take ta tafi shuuuuu har ta dangana da bangon dutsen kogon, ya sake nuna ta da sandar hannunsa rai a ace nan take ta ame am kamar dutse. A razane Mahaifiyarta ta arasa gabansa cikin kuka ta dafa afafuwansa, bai tanka
Chapter 49 · 0% Book details