← Book details Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 89

Sashe 76

Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sarki Sulaiman ya katse Sarki Abdul'aziz. "Allah ya ara lafiya Sarki mai matu ar karamci da mutumci." Sarki Sulaiman na shirin amsawa Sallamar Jawahir ta kara e dodon kunnuwansu. Ganin takalman Kamalu ya sake tabbatar mata da yana ciki don haka ba ta jira an amsa ba ta fa a cikin akin. Muryarata har abada ba za ta ta a zama ba uwa a wurinsa ba, ko mutuwa ya yi ya dawo ba ya tunanin sautin muryarta zai yi masa gizo ballanta ya mantata. Tun da ya ji muryar Jawahir tsigar jikinta ta yi wani irin yarr, gabansa ya yi mummunar fa uwa. Wani irin yanayi ya fara ratsa shi, da yar ya an daidaita kansa amma har lokacin wayar idonsa na kan ofar, shigar Jawahir cikin akinsa ya kusa haifar masa da dakushewar numfashi na wucin gadi, ya kafe fuskarta da kallo yana mamakin tsananin kamar da fuskarta ta yi masa da matar da har duniya ta tashi ba zai ta ta a mantawa da ita. Sai da ta zube a gaban Sarki Abdul'aziz ka fashe da kuka. "Ranka shi da ararsa na kawo maka wallahi yau ba aramin zalintata ya yi ba." Jawahir ta arasa maganar tana nuna Kamalu, kunyar duniya ta lullu e Kamalu. Ya sunkuyar da kai asa, yana jin tamkar asa ta tsage ya shige ciki. "Kamalu me ya ha a ka da anwarka Jawahir?" Sarki Abdul'aziz ya yi tambayar fuska a ha e duk da kalaman Jawahir ba aramin dariya suka ba shi ba. Jin sunan Jawahir ya sa gaban Sarki Sulaiman ya ci gaba da fa uwa, jikinsa ya yi sanyi ya sake zuba mata ido. "Jahawir!" Ya ambata da wani irin yanayi, da sauri Jawahir ta dube shi jin yadda ya furta sunan nata. *SHU'UMAR MASARAUTA* *40* *Littafin ku i ne 500 idan kina bu ata za ki biya ta wannan Account in Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.* Tamkar yadda inuwar mutum ke bibiyar kowacce hallita haka Boka Shaddas yake bibiyar Jawahir domin ya samu nasarar kai ta kogon dutsen Shugaba Zurufu, sai dai a duk lokacin da ya kusance ta wata irin fa uwar gaba da razani ne suke maye shi. Ya sha ruwan mamaki matu a da 'yar anuwar yarinyar take yun urin gagare masa, don har lokacin da ta tunkaro sashen Sarki Abdul'aziz yana biye da ita amma ya gagara sarrafa komai a kanta, dalilin da ya sa yake riki a zuwa mabambamtan hallitu don ya yi nasara a kan. La e wa ya yi a jikin wata bishiyar darbejiya, yana jiran fitowarta don ya ci alwashin a wanan karon ba zai bar ta ba. "Ina shakkun nasarar da kake hanga a kanta! Gani nake mahaifiyarta ba ta zuba ido a kanka har ka cutar da ita ba." Boka Shadda ya ji an furta a bayansa yana waigowa ya yi tozali da Dattijo Maharaz. Sai da ya tur une fuska sannan ya furta. "Me ya sa kace haka? Ko ka manta da nawa hatsabibancin ne?" "Ka manta wace ce mahaifiyarta da zamanin da ta yi? Tun wuri ina mai baka shawara ka ha ura, idan ba haka ba kuwa allura za ta tono garma." Dattijo Maharaz ya furta har zai wuce da sauri Boka Shaddas ya sha gabansa. "Soyayyar ana ce ta sa zan yi yun urin aikata haka, ko don ba anka aka ta a ba?" Murmushi Dattijo Maharaz ya yi ya ce. "Kuskuren da Mahaifiyarta ta aikata a baya kenan, Shaddas ka sani shi musulunci daban yake. Kuma a duniya wata hallita ba ta isa ba ta cutar da wata ba har sai Ubangiji ya addaro haka a cikin kundin addarorin kowanne bawa. Na ba ka shawara ne a silar zumuncin da ya ta a giftawa tsakanina da wani kakanka kafin ya rasu wani abin farincikin a hannuna ya kar i kalmar shahada. Da za ka tuba ka koma ga Allah da ya fiye maka wannan mummunar turbar da kake kai wacce ba za ta dire ka ko ina ba sai a yankin azaba da u uba." Daga haka Dattijo Maharaz ya wuce ya ba wa Boka Shaddas hanya. Wani tunani ne ya fa o wa Boka Shaddas har sai da ya saki murmushi a fili sannan ya wuce kogon tsafinsa. Fargi ta jima a wurin bishiyar kukar da suke bautawa tana kai mata kokenta ba ita ta bar wurin ba sai kusan doshin Asuba, kai tsaye Masarautar Sarki Sulaiman ta wuce a saitin windonsa ta tsaya cikin surar tantabara ta fara ka a fuka-fukanta tana kuka. Jin haka ya sa da Sauri Sarki Sulaiman ya ta shi ya fice duk da har lokaci ba a kira assalatu ba. Da hannu ya auki tantabarar ya zagaya akin hutawarsa sai da ya rufe ofar sannan Fargi ta yi girgiza ta dawo cikin ainihin surarta. "Yanayinki ka ai shi ya tabbatar mini akwai wani al'amari da yake faruwa." Shiru ta yi ta sunkuyar da kanta asa tana jin wani abu na yi mata yawo a rai, a hankali ya matsa gabanta ya riko ta tamkar wacce take jira sai kawai ta fashe da matsanancin kuka. "Gabansa ne ya ci gaba da fa uwa, bai hana ta ba sai da ta yi mai isarta yana shirin yin magana ta furta. "Ina aunarka Sadaukina! Kuma ina aunar abin cikina, ina yi mata so mai tsanani soyayyar da kowacce uwa take yi wa 'yarta. Don Allah ko bayan rayuwata ka kula mini da ita." A razane Sarki Sulaiman ya mi e tsaye ya furta. "Me kike fa a haka Fargi? Me yake faruwa da ke ne?" Murmushin arfin hali ta iro ta share hawayenta sannan ta ce. "Sai wani abu ya faru Sarkina? Babu wani abu da ya faru da ni kawai ina tsoron kada nan gaba danginka su i kar arta a matsayin 'yar cikinka!" Guntun tsaki ya saki ha e da ajiyar zuciya, sai da ya koma ya zauna sannan ya ce. "Na yi tsammanin wata maganar za ki fa a, kada ki damu Fargi. 'Ya ta za ta taso cikin kulawar mahaifi da zuri'arsa. Bayan wannan akwai wani abu?" Kai ta girgiza masa tana bin sa da kallon tausayi. Ta mi a masa wasu wuri guda uku, ta sake mi a masa wata anuwar jakar fata. Sannan ta auko wata atuwar azurfa ta ha a masa da su, da mamaki yake bin ta kallo ganin yana bu atar arin bayani ta ce. "Ka yi mini al awarin za ka aiwatar da abin zan gaya maka." "Na amince, ina jinki." "Ka shafa jinin jikinka a jikin kowanne abu da na baka, sai ka auke shi zuwa bakin kowacce irin bishiyar kuka ka ha a rami mai an zurfi ka binne. Wanne suna kake muradin a sanyawa abin da zan haifa?" Jim Sarki Sulaiman ya yi sannan ya furta. Gudun kada su fahimci yanayin da yake ciki ya sa Sarki Sulaiman ya saki murmushi ya furta, "Suna mai matu ar muhimmanci da ma'ana!" Da i ya mamaye Jawahir, ta dubi Kamalu da ke sunkuye da kai ta yi masa gwalo ha e da fa in. "Ka ji dai mai ranka shi da e ya ce suna ma ba irin naka ba." A wannan karon gabansa har ya fi na baya fa uwa, bakinta ya bi da kallo yadda take sarrafa shi tamkar yadda Fargi take magana. "Kada sake shiga harkarta Kamalu, ka bi ka hana yarinya sakat idan ba haka ba ranka zai aci." Sarki Abdul'aziz ya garga i Kamalu. "Allah ya taimake ka wanki fa kawai ta yi mini." Da sauru Sarki Abdul'aziz ya dubi Kamalu, ya sake ha e fuska ya ce. "Mun soke wannan aikin daga yau, idan kuna bu atar a yi muku wata hidimar ku nemi Bayi a saka su." Cike da ladabi Kamalu ya amsa yana jin haushin Jawahir a ransa. Sarki Abdul'aziz zai sake yin magana suka ji sallamar Galadima shi da Muhsin. Kallo aya Sarki Abdul'aziz ya yi masa ya fahimci akwai abin da ya kawo shi, ganin Sarki Sulaiman ya sa Galadima ya an ha e fuska. Sai da suka gaisa sannan Galadima ya furta. "Ranka shi da e muhimmiyar magana gare ni, kasan dai ko da ka kasance kai ne Sarki mu kuma yayyanka ne dole mu..." "Galadima a tsumaye mu muna ganawa da Mai martaba, idan muka fito za mu tattauna." Sarki Abdul'aziz ya katse shi cikin hanzari, don ya san maganar da Galadima zai kawo masa ba mai da i ba ce. "Ka ga Abdul'aziz wannan maganar ta yi daidai da lokacin yin ta, domin fa uwa ce ta zo daidai da zama. Ga ka ga Sarki Sulaimanu ga yaron nan Muhsin yanzu me ya rage? Ko ka fi son sai ya tafi idan ya auko magnar ka ce kun riga da kun gama yanke hukunci? To ba za ta sa u ba, yaron nan ya je ya same ni da magana don haka ni ne gaba da kai dole zan iya yanke hukunci a kan abin da ya kamata." Galadima ya yi maganar cikin ha ancewa don wannan botsarewar da Muhsin ya yi ba aramin da i abin ya masa ba, ko ba komai ya samu kafar da zai cusa 'yar wurinsa ga Muhsin tun da ya nuna ba ya son ha in da mahaifinsa zai yi masa. Kunyar duniya ta lullu e Sarki Abdul'aziz, ya sauke gwaron numfashi ya nuna can gefe sannan ya furta. "Bismillah muna sauraronku." Cikin gadara Galadima ya zauna, Yarima Muhsin ya ja afafuwa ya zauna yana sunkuyar da kai asa. "Sarki Sulaimanu ka san dai Abdul'aziz anina ne wurin na biyu, amma da yake bai auke ni da ima ba sai da kuka ci kuka cinye a maganar auren yaran nan ba tare da an sanar da mu komai ba..." "Galadima a tafi kai tsaye." Sarki Abdul'aziz ya katse shi rai a ace. Sai da Galadima ya yi wafa sannan ya furta, "Yarima ya same ni da maganar ba ya son auren ha in da ake shirin yi masa, don haka na ga ya dace na zo na soke wannan maganar sai kuma aka yi sara a kan ga a tun da kai ma ga ka a zaune Sarki Sulaimanu."
Chapter 76 · 0% Book details