Sashe 33
Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
mu yi bori da sanyin jiki mu ga samu mu ga rashi." Ri o hanunsa ya yi cikin jin da i. "Na matu ar jin da in wannan maganar taka, dama an ce aikin mai shawara ba ya aci sai da kuma ba shi da sirri." Galadima ya bushe da dariya, "To ai dama abokin kuka ba a oye masa mutuwa ka ga sai mu ci mu lashe ba tare da wani ya sani ba." Ciroma ya ba shi amsa sannan ya yi masa sallama. Yana fita Zulai matar Galadima ta shiga akin da sauri ta yi asa da murya, "Mai gida an ya kana ganin ka yi farar dabara kuwa? Kar fa Ciroma ya..." "Haba Zulai kamar ba ki san mijinki ba?" Galadima ya katse ta. "Ai duk inda mai aro za shi da sanin mai kaya ne. Kina tsammanin a banza zan ce Ciroma ya yi wa Mai martaba magana game da auren ha in da yake son yi tsakanin ansa da Sakina? Tsuntsu biyu na ke son jifa da dutse aya don na san waye Abdul'aziz ba na jin zai bayar da 'yarsa ga mashayi, kin ga a lokacin kowa ya san da bu atar Ciroma idan Takawa ya hana auren a daidai ga ar ni kuma it zan kashe shi, kin ga zargi zai hau kan Ciroma bayan an tura shi gidan yari kafin a na a Yarima sai na san yadda zan ullo a ha a aurensa da yarinyar nan. Bayan wannan me ya rage Zulaihatuna?" Galadima ya arasa maganar yana kallon Zulai. "Ayyiriyiriyiriiii! Shi ya sa ko ka an ba na kaicon za ar ka da na yi a matsayin mijin aure, ka biya ni ko ba sisi billahillazi da an ga sabuwar sarauta a asar nan." "To tun da mu Marigayi ya i mu da sarautar ba sai mu dasa 'ya'yanmu a kai ba, matar sarki idan ta iya jan birki ai ita ce Sarkin mai jan ragamar masarautar." Gaba aya suka kwashe da dariya. Tun bayan rabuwar Kamalu da dattijo Maharaz bai sake ganinsa ba kuma ko ka an ba damu ba saboda a kullin suka ha u da tsohon bai wuce ya ri a gaya masa maganganun da bai cika gane makamarsu ba, sannu a hankali ya saba da aikin wahalar da Bayi mazan suke yi sune saran itace, yin gine-ginen har fasa dutse ba a bar shi a baya ba. Lokaci aya hasken fatarsa ya disashen ya yi duhu sosai don kusan kullin idan Inna wuro ta gan shi sai tausayinsa ya kamata. Watarana suna zaune bayan Kamalu ya dawo daga fasa dutsen da aka saka su hannuwansa duka sun farfashe, ya zauna yana cin abinci ya dubi Inna wuro idanu cike da walla. "Inna wuro yanzu shi kenan rayuwar Bayi a haka za ta are? Ba mu da 'yanci ba mu da gata ba mu da lokacin kanmu ballanta mu amfani kanmu da kanmu? Inna wuro na gaji ki zo mu bi dare kawai mu gudu ina ganin sai mun fi samun kyakkayawar rayuwa." walla ta zubo idanunta jin hannunsa yadda ya bushe ya yi tauri kamar katako a saman hannunta, duk wahalar da suke sha nasu nafila ne a kan mazan cikin masarautar. "Kamalu haka Allah ya addara mana, shi ne gatanmu yana kallon duk halin da muke ciki. Idan muka ce za mu gudu ina za mu je?" Kamalu ya cusa sandararran tuwon dawar bakinsa yana turawa da yar yana share hawaye, a hankali Inna wuro ta ri a lallashinsa har ya watsar da maganar guduwa daga cikin gidan. Inna wuro ita da Mai gado ta su ta fi zuwa aya duk cikin sashen Bayin, sai dai kuma 'ya'yansu ko ka an ba sa jituwa duk da sun kasance ba sa'annin juna ba. Ko ka an Kamalu ba ya ta a zama wurin da Jawahir take zaune, haka kawai ya ji ya tsani yarinyar musamman idan ya kalli wayar idonta da yake ganin wata murgujejiyar bishiyar kuka a ciki. Ita kuma Jawahir duk lokacin da Kamalu ke zaune a wurin da take wani irin zafi ne yake ratsa ta, sannu a hankali kuma sai ta ri a ganin tururuwa na fita daga jikinsa duk wacce ta arasa jikinta sai dai ta ji tana gasa mata cizon da ke arin aye fatarta. Dalilin da ya sa Kamalu na zama ita kuma za ta ri a zunduma ihun neman agaji. Yana gama cin abinci ya mi e ya zagaya ta can bayan rumfar bayi ya ci gaba da tafiya har ya isa bakin bishiyar tsamiyar da ke kallon bayan akunan Bayin. Tun bai kai ga zama ba ya ji muryar dattijo Maharazu. "Assalamu alaikuma!" Bai san ya yi rashinsa na kwana biyu ba sai a yanzu da ya ji muryarsa, "Dama kana nan wai ina ka shiga?" Kamalu ya tambayi Maharzu cike da yarinta. "Kada ka bari rauninka ya bayyana a fili ta yadda magauta za su fahimci lagonka har su nemi cin galaba a kanka. Kalli can wurin." Dattijo Maharaz ya furta masa ha e da nuna masa bayansa. Wani yaro ya gani kusan sa'ansa ne a shekaru kwance a asa sai birgima yake yi yana iban asa yana ci yawu na dalala daga bakinsa. Hankali a tashe ya furta. "Waye wancan kuma me yake yi a wurin nan?" Murmushi Dattijo Maharazu ya yi ya kama hannun Kamalu suka arasa gaban Abubakar sannan ya furta, "Idan har an sarkin Masarutar nan zai kasance haka me kake tsammani a kanka?" A razane Kamalu ya dube shi, "Ka na nufin wannan a masarautar nan yake kuma an sarki ne?" Kafin Dattijo Maharzu ya ba shi amsa Kamalu ya ga matashin ya ago yana cizgar gashin kansa, gabansa ne ya fa i. Jikinsa ya yi matu ar sanyi, haka kawai yake jin kamar ya ta a ganin mai yanayin kamanninsa duk da wannan kallo aya za ka yi masa ka fahimci ba shi da lafiya sakamakon yadda surar hallitarsa ta koma. Daga can bayansa ya ji muryar Inna wuro ta araso tana fa in. "Kai Kamalu me kake yi a wurin nan da doshin magriba?" Idanun Kamalu suka ciko da walla ya nuna mata Abubakar ya furta, "Don Allah Inna wuro ki duba wannan wai shi ma an Mai martaba ne ki dubi irin halin da yake ciki." Sororo Inna wuro ta yi tana kallon wurin da yake nunawa babu abin da ta gani, tana shirin yin magana ta sake jin Kamalu ya furta. "Amma Dattijo Maharazu me ya sa Sarki ba ya ba shi kulawa, wacce irin larura gare shi?" Bayan sallar Isha'i Fulani Babba tana zaune sa o ya iso gare ta wai Mai martaba na gayyatarta cikin turakarsa, ta cika da mamaki matu a jiki a sanyaye ta yi wanka ta gyara jikinta ha e da feshe ko ina da turare sannan ta nufi sashen na shi gabanta na fa uwa. Banbarakwai take ji wai yau Takawa ne yake son tarawa da ita a turaka, farincikinta ya nunku don idan ba ta manta ba rabonta da Takawa tun da cikin Abubakar, sai kuma mafarkin da take yawan yi yana mu'amala da ita arfi da yaji a cikin mafarkinta. SHU'UMAR MASARAUTA *Littafin ku i ne 500 idan kina bu ata za ki biya ta wannan Account in Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.* A sanyaye Fulani babba ta aga labulen akin ta same shi kishingi e ya ci ado cikin jajayen kayan saki wa anda aka ratsa cin bakinsu da zaren zaiba, ba aramin kyau ya yi mata ba don rabon da su ke e kamar haka har ta manta. "Ke zinnariyar mata ce samun kamarki ko an duba dubban mata babu kamarki, wani lokacin idan na zauna sai na dinga gode wa Ubangiji da ya mallaka mini kyakkyawar sura da kyawun halayenki." Fulani babba ta saki murmushi a kunyace. "Kin kasance lantarkin da ke haske birnin zuciyata don Allah ki kasance da ni har arshen rayuwa Fatima." Muryar Takawa ta daki kunnuwanta cikin wata irin murya mai auke da shau in so da auna, tare da son nuna tsantsar kewa da begen masoya. "Ban san gaibu ba Fulanina amma ina mai kyautata miki zaton ke 'yar aljannah ce." "Na sani Fulanina ta dabance mai farar zuciya da ladabi da biyaya." "Idan ina kallon sura da kyawun halittarki sai na ga a duk fa in duniya babu wanda ya kai ni sa'a, sa'ar da nake fatan kasancewa da ita har cikin aljanna. Idan na ra a gangar jikina a naki ji nake tamkar na dawwama a haka ba tare da zare jikinki ba. Ke 'yar Aljanna ce sarauniya kuma gimbiya a wurina, ki adana wa annan kalaman duk rintsi ba zan iya rabuwa da ke ba." Lokaci aya ire-iren kalaman da Takawa yake yawan furta mata a shekarun baya suka dawo mata, ta tattaro murmushi tana jin wata irin warin gwiwa na ratsa ta har ta isa cikin tsakiyar akin. Hannuwa ya bu e mata yana daga kwance ha e da sakar mata murmushi, a kunyace ta sunne kanta asa ta arasa jikinsa kusan lokaci aya suka saki ajiyar zuciya. "Me ya sa kike ari- ari da mijinki ko don na ce zan ara aure ne Fulanina?" "Ko ka an aurenka bai ta aga mini hankali ba, da ace zan samu wannan kulawar ko mata ari idan ana yi ka je ka yi babu ruwana." Fulani Babba ta fa a a zuciyarta. Amma a fili sai ta furta. "Ba haka ba ne Sarkina." Ita kanta sai da ta ji wani iri a kalaman da ta furta masa, ta yi mamakin yadda ta ga Mai martaba yake ba ta kulawa hatta abinci tare suka ci wani abin da ya da a sanyaya ranta bai wuce yadda har kawo lokacin fitsarin da ke fita daga jikinta bai fita ba ballantana ya ata mata jiki. Daga haka sai hirar ta su ta fara sauya salo, tun Fulani babba na jin nauyi da kunyar mayar masa da martani har ta saki jikinta take sarrafa mijinta cikin kyatatawa. Wani sanyin da i da farinciki ne yake ratsa da ta ora wayar idonta a kan Takawa da ke yun urin mu'amala da ita, ita