← Book details Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 89

Sashe 37

Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.* Ganin tsaiwa da sa a da warwara ba zai kai ta ba ya sa Fulani Umaima wasa ofar da arfi ha e da oye sihirtacciyar butar a cikin zaninta. "Waye nan?" Ta ji an furta, ana arasowa wurin ofar. "Muna bu atar ganawa da Mai martaba."Cewar Fulani Umaima. Da mamaki Dogarin yake duban Fulani don a lokacin dare ya yi kusan sha biyu ta an gota. "Allah ya taimake ki ranka shi da e ya jima da kwanciya..." "Kana nufin ba zan iya ganinsa ba?" Fulani Umaima ta furta a harzu e. Babu musu ya turo ofar sai da ta shiga ta wurga masa harara sannan ta wuce cikin sashen Mai martaba. Tana shiga soron arshe ta ja ofarsa ta datse cikin san a ta wuce ta ofar sashen sha awatar Sarki Abdul'aziz, duhun daren bai sa Fulani Umaima ta tsorata ba don haka sai da ta yi tafiya mai nisa sannan ta tsugunna a bakin wata bishiya ta fara ha awa da sauri. Sai da ta tabbatar da ta yi ha a mai an zurfi sannan ta tura butar ta mayar da asar ta rufe, a fili ta saki murmushin samun nasara tana jin wani farinciki na ratsa ta tamkar wacca aka yi wa kyautar aljanna. Da sauri ta kewaya ta bu akin Sarki Abdul'aziz bakinta auke da sallama a lokacin tuni ya jima da yin bacci, sai da ta jima a tsaye tana kallonsa sannan ta bubbuga afarsa. Da mamaki yake kallonta ya yun ura ya tashi zaune yana shirin yin magana ta riga shi. "Wallahi tsora ta ni ake yi yanzu haka bacci ya gagari idanuna." Mamaki ya bayyana arara a fuskarsa. "Tsoro fa? Me yake tsora ta ki?" "Tafiya nake ji sai kuma na ji an koma!" Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya furta. "Shi kenan sai ki kwanta a nan." Yana gama maganar ya matsa mata, a yadda ta lura sam bai ji da in kwananta ba. A fakaice Fulani Umaima ta sakar masa harara. "Da ni kake zancan ba dai kana wani rawar afa a kan Fulani Babba ba kai wai mai mata, za mu gauraya ne." Fulani Umaima ta yi maganar a zuciyarta. Rage kayan jikinta ta fara yi sannan ta koma gefen Takawa ta kwanta zuciyarta al saboda tsabar farinciki kasa runtse idanunta ta yi ba ta san lokacin da bacci ya auke ta. "Akwai dalilai da dama da ya sa na auracewa dangina, asalina da tushena na guje su domin ni ban kasance tamkarsu ba, me ya sa kike son kawar da wayar idonki a kan abin da yake daidai? Ke ba kamar sauran mutanen da ke rayuwa a cikin wannan masarautar ba ne hasali ma mutane da dama suna farautar rayuwarki." Shiru Jawahir ta yi tana sauraron matar da tun ha uwarsu ta furta mata cewar ita mahaifiyarta ce. A hankali ta ga matar ta araso gabanta ta dafa kafa arta sannan ta ci gaba. "Ki je sashen Sarkin cikin masarautarku ki tone abin da matarsa Fulani Umaima ta binne idan ba haka ba Fulani babba za ta mutu, idan kika bari Umaima ta ci gaba da yin nasara a cikin masarautar nan ina mai tabbatar miki sai ta yi nasara a kanki. Sai ta dam a ruhinta ga hatsabibin boka Bamaguje kuma ki sani matu ar ruhinki ya je gare shi babu wani taimako da ni ko abin bauta za mu iya yi miki." Tsoro ne ya mamaye zuciya Jawahir, a sanyaye ta furta. "Wallahi tsoro nake ji idan Fulani Umaima ta kama ni kashe ni za ta sa a yi." Take annurin fuskar matar ya auke, ta fara ja da baya a hankali sannan ta daki guntun tsaki. "Tun ranar da na bu i ido a cikin zuri'ata ban ta a jin kalmar tsoro ta fito daga bakinsu ba, tabbas Shugaba Zurufu ya yi gaskiya ga irin abin da yake guje wa zuri'armu dangane da auren bare, auren da ba zuri'armu ba." Sai da matar ta tsaya cak fuska a ha "Jawahir!" Ta ambaci sunanta cikin wata irin murya. "Ki gaggauta zuwa ki lalata tsafaffiyar butar da ta binne, ki ebi ruwan kogin tsamiya ki kwara a a sashen Fulani babba idan kika bari ta yi nasara a kanta nan gaba tana iya yin galaba a kanki, wannan umarni ne nake ba ki a matsayina na mahaifiyarki." Firgigit Jawahir ta farka daga nnnauyan baccin da ya auke ta mai cike da tarkacan mafarkai kala-kala. A daidai lokacin Mai gado ta shiga akin ta ajiye butar da ta yi alwalar sallar Asuba. "Jawahir tashi ki yi sallah kin san anjima ka an za ku tafi sassa ar dawa." Da wani irin kallo ta bi Mai gado gabanta na fa uwa, wani irin tsoro na lullu e ta. A hankali ta furta. "Inna don Allah wata magana nake son yi miki amma don Allah kada ki buge ni." Rass gaban Mai gado ya fa i, a hankali ta koma kusa da ita ta zauna. Kasancewar Fulani Babba mai sanyin hali da rashin hatsaniya ya sa ko da aka kawo ta masarautar Huddam ba ta samu matsala da kowa ba, tana matu ar girmama Mai babban aki don ta auke tamkar mahaifiyarta. Sai da Fulani Asabe ta gama karantar halayen Fulani babba tsaf sannan ta nemi jan ta a jiki don ta haka take son cim ma manufarta, idan ta janyo ta jiki ta dinga bugar cikinta tana jin sirrin Sarki Abdul'aziz daga arshe kuma ta jefi tsuntsu biyu da dutse aya. Fulani babba zuciyarta aya ta aminta da Fulani Asabe amma da yake mahaifiyar Sarki Abdul'aziz ta san halinta sarai sai watarana ta sa aka kira mata ita aki ta nusar da ita halayen da abi'un mutanen cikin gidan don haka dole sai ta yi takatsantsan. Ba aramim da i ta ji ba ta sake godiya ga Allah, da Allah ya ha a ta da mahaifiyar miji ta gari don koda ta san masarautarsu ba ta kai wannan girma ba ta san suma suna fama da kacaniyar makirci da tuggu don haka sai ta iya zama da kowa a ruwan sanyi. Ganin hanyar da Fulani Asabe ta auka ba za ta bille mata sai wata dabarar ta fa o mata, ta ji da i sosai da wannan tunanin ya zo mata a daidai ga ar da take bu atar auki. anwarta Zulai da ke aure a Masarautar Bhahdi ce ta fa o mata da yake ta san tana da 'yan mata guda biyu, Umaima ita ce babba sai anwarta Zannira, ta na da yayye maza da anne maza. Takanas Fulani Asabe ta kai wa anwarta ziyara don a wannan karon ba za ta aika da sa o ba. "Zulai aure nake so na ulla tsakanin Umaima da Abdul'aziz, amma aure ba na zama dundundun ba." Mahaifiyar Fulani Umaima ta an yi jim. "Ban fahimce ki ba Yaya." "Ina nufin za ki ba ni Umaima na tafi da ita, ni zan yi duk shige da ficen da zan yi wurin malamai da bokaye don ta saye zuciyarsa. Babban burina ya aure ta duk wani ku irina sannu a hankali zan dinga zana mata tana aiwatarwa. arfi da yaji so nake sarautar Masarautar Huddam ta dawo hannun wannan yaron, idan ma mutuwa ce ta dace da Abdul'aziz ni ban damu ba domin kin fi kowa sanin yadda na allafa rai a kan karagar nan, saboda Masarautarmu ta sha bambam da masarautun nahiyar afirka gaba aya." Dariya mai sauti Zulai ta saki. "Sai yanzu na fahimci inda kika dosa don na san bakya wanki sai da zakara, ni dama tun da na fara jin kalamanki na san banza ba ta kai zomo kasuwa. Yanzu dai idan komai ya kammala me ye kasonmu?" Fulani Asabe ta bushe da dariyar farinciki tamkar bu atarta ta gama biya. "Babu abin da za ki bu ata ba zan aiwatar miki ba Zulai, ai ranar biyan bu ata rai ba a bakin komai yake ba." Sai da Mai gado ta aro mayafin jarumta ta yafa wa gangar jikinta sannan ta furta, "Mene ne Jawahir? Gaya mini babu abin da zan yi miki." Jawahir ta an fara murza hannunta a hankali tana jin gabanta na fa uwa ga wani irin ra i da tambarin cikinta yake yi mata ta furta. "Inna wannan matar da ta ce ita mahaifiyata yau ma na sake yin mafarki da ita, wai ta ce mini Fulani Umaima ta binne abin da Fulani babba za ta mutu..." Gaba aya abin da ya faru ta kwashe ta gaya wa Mai gado, da sauri Mai gado ta sa hannu ta rufe mata baki. Sai da ta tashi ta je ta tura ofar akinsu don kar wani ya ji abin da suke fa a sannan ta koma wurin da Jawahir take zaune. "Ki yi shiru da bakinki kin ji Jawahiruna. Ni ka ai ce mahaifiyarki ba ki da kowa sai ni kin ji, sharrin she anu ne suke saka ki yin mafarki amma zan sa Malam ya kar o miki turaren miyagu. Koda wasa kada ki sake ki fa awa kowa kin ji." Jawahir ta gya a kai a hankali kamar mai nazari sannan ta ce. "Kuma ta ce abin bauta zai yi fushi da ni mai tsanani idan na bari Fulani Umaima ta yi galaba a kaina.. "Kul Jawahir kina son ki jefa mu cikin kogon bala'in da za mu yi tsallen da har abada ba za mu iya fitowa ba?" Jawahir ta girgiza kai. "To kin ga daga yau duk ranar da kika yi mafarki da ita ki ce ke ba ki san wani abun bauta ba kin ji." Jawahir ta amsa sannan ta mi e har ta je bakin ofa ta dawo ta zauna. "Inna wallahi Yaya Habu tausayi yake ba ni saboda da guba a jikinsa." Wannan karon Mai gado ba ta dakatar da ita ba sai ma tambaya da ta wurga mata. "Guba wacce iri Jawahir?" Fulani babba sai da dare ya tsala sosai ta farka sakamakon yadda ta ji wuyanta ya sage mata, a hankali ta tashi har ta je bakin ofa ta koma ta sumbaci Abubakar. "Allah ya baka lafiya Abubakar ya nuna mini lokacin da zan ganka ka
Chapter 37 · 0% Book details