← Book details Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 89

Sashe 56

Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

riski tambayar Sarki Hafiz a tsakar kaina. Yadda Basiru ya yun ura da sauro zai wafce littafin ne ya sa Boka Shaddas ya yi saurin rufe shi, da mamaki yake bin Basiru da kallo cikin wayancewa ya furta. "Ya kai babban boka mai ta ama da tsafi da sihiri. Ni fa na agauta mu kai arshen labarin nan, don haka nake son kar a na arasa shi ko ma cim ma abin da muka sa a gaba." Ajiyar zuciya Boka Shaddas ya yi a karo na farko da ya ji ya ora zarginsa a kan Basiru, don haka bai tanka masa ba sai da tashi ya arasa can wurin da ya auko littafin ya mayar da shi cikin ashin asa, sannan ya koma gefen Basiru ya zauna. Sai da Furhussam ya saki murmushi sannan ya furta, "Saboda ba zan juri ganin tana ba wa 'ya'yan da ba nawa ba kula, don a lokacin kusan haihuwata uku da ita." Jinjina kai Sarki Abdul'aziz ya yi cike da tsananin mamaki. Ya riski Furhussam ya ci gaba da cewa. "Tun yaron nan yana tsumma muke kula da al'amuran rayuwarsa, kai hatta addinin da yake kai ba don son raina yake yi ba sai don babu yadda zan yi ne. A shekarun baya na so na auke hankalinsa zuwa ga addininmu na bautar ruwa, sai Hullat ta garga e ni da na yale shi ya yi addinin da yake so don ko ka an ba ta son abin da zai takura wa Kamalu. Cikin haka yake rayuwa kuma duk shekara ina aukarsa na sake gabatar da shi ga zuri'ata a matsayinsa na mamamallakin karaga kuma mijin mafi soyuwar jikata, sai dai nakan jefa masa wasu-wasu har na ya dinga ganin abin kamar ya faru kamar kuma bai faru a gaske ba. Akwai lokaci da dama da matar ubansa take nufarsa da miyagun abubuwa da kaina nake karya shi ko na dakatar da shi, kuma ina mata wannan kawaicin ne saboda kusancina da mahaifinta amma da tuni na hallaka ta. Girmansa da nake gani ne ya sa ko zancan hakan ban ta a yi masa ba, har dai ta ha ura ta watsar da komai. A yanzu haka zancan da nake yi maka saura watanni uku cif-cif mu yi shagalin bikin tariyarsu, don haka na ci alwashin matu ar ina raye babu yaron nan babu auren wata hallita bayan jikata. Sannan wannan butar da ya zo ya ajiye ka san ta mece ce?" Tun Furhussam bai ambaci sunan Sarki Abdul'aziz ba ya girgiza masa kai, sannan Furhussam ya ci gaba da cewa. "Wannan sihirtacciyar butar a allah ta shafe sama da shekara dubu biyar, kuma an tono ta ne daga ashin asar Rumi da ke fadar Sarki en aljanun ashin duwatsu. Ha a Kamalu ya ora warya a gurbinta, domin alwashi ne ga magabatanmu a kan wannan butar ga duk wanda ya dawo da ita duk abin da ya yi niyya dangane da bu atar ransa nan take za a zartar masa da ita. Amma na yi mamakin dalilin da ya sa Fargi ba ta aiko iyarta ta zartar da wannan aikin ba." Da mamaki Sarki Abdul'aziz ya furta. "Shin dama wata ce ta turo shi? Wace ce ce ita?" "Ba fa ar labarinta ne ya kawo ni ba Sarki Abdul'aziz, ka bari idan na zartar da abin da yake gabana zan iya fe e maka biri har wutsiyarsa." Fursussam ya furta cike sa agauta. "Sarki Abdul'aziz ina son ka are wa yaron nan kallo tun daga yatsun afarsa har zuwa tsakiyar kansa." Dattijo Maharaz ya furta yana har e hannuwansa biyu a irji. Lokaci na farko kenan da irjin Sarkin Abdul'aziz ya buga a daidai lokacin da ya sauke wayar idonsa a saman yatsun Kamalu da ke auke da cindo irin nasa, ya ci gaba da kallonsa har zuwa saman yatsun hannuwansa da ba su da maraba da na jikinsa. Tarin tunaninnika suka rikito wa kwanyarsa, don haka ya ago da mamaki yana shirin wurga wa Dattijo Maharaz tambaya ya katse shi. "Wannan yaron makusancinka ne, magajinka ne kuma shi in jininka ne." Mamakin Sarki Abdul'aziz ya ninku a sanyaye ya ce. "Ban gane ba Dattijo Maharaz." "Ina nufin wannan yaron Kamalu da muke dambarwa a kansa anka ne na cikinka halak-malak, kuma babu ko tantama ko a yanzu zai iya hayewa saman karagarka." Cikin shammata Furhussam ya auki Kamalu ya bigi bangon akin nan take ya ace da shi, hankalin Dattijo Maharaz ba aramin tashi ya yi ba. A gaggauce ya dubi Sarki Abdul'aziz ya furta, "Kada ka furta wannan maganar ga kowa har sai na dawo gare ka." Daga haka shi ma Dattijo Maharz ya ace daga wurin. Bamaguje shi da Fulani Umaima ba su sauka a ko'ina ba sai a kogon dutsen tsafin Shugaba Zurufu, yana raka e a jikin bango ya tsufa tukuf don har ya fi Bamaguje tsuf a nesa ba kusa ba. Kallo aya idan ka yi masa ba za ka ta a tsammanin zai iya motsi ba ballantaba ya iya aiwatar da wani mugun abu. urrr ya yi wa Fulani Umaima da ke raka e a gefe tana zare idanu cikin tashin hankali. "A wacce rana kika haifi Basiru?" Shugaba Zurufu ya wurga mata tambaya yana kafe ta da shanyayyun idanunsa. "Wallahi na manta ba zan iya tunawa ba." "Kin haifi asara! Domin kin ebo ruwan dafa kanki Umaima. Yanzu dai ina son ki ebo mini gashin kansa, ki kuma ki ebo mini sawun afarsa. Kuma zan ba ki asirin da zai taimaka miki wanda da za ki kawo mini wannan Yarinyar da afafuwanta har cikin kogon tsafina, domin na yi binciken abin da Bamaguje zai bincika a kanta." Tun bai gama maganar ba gaban Fulani Umaima yake fa uwa, don yadda take shakkar Basiru ko Takawa ba ta tsoronsa haka. Za ta yi magana ta ji wannan abin ya sake tunku o mata cikin azaba ta zuba ihu tana rirri e Bamaguje, a hankali ta ji ya fara lafa mata sai ga wani ruwa tamkar na mugunya yana gangarowa daga asanta. A duddu e haka Shugaba Zurufu ya tako a hankali har ya arasa gabanta ya tsugunna, kuka Fulani Umaima ta fashe da shi ta dubi Bamaguje. "Bamaguje ka shiga lamurana ka duba halin da nake ciki." Wannan karon a fili ya nuna tausayinta don haka ya sunkuyar da kansa asa. "Har a kullin ina fa a miki hannunka ba ya ta a ru ewa ka yanke ka wurgar, tun a ranar da kika ziyarce ni na fuskanci matsalarki Umaima. Sai dai kash! Har kawo yau na gagara samun mafitar ciwon da yake tattare da ke, bayan wancan dalilin na littafin labarin Hidaya dama na ci alwashin kawo ki wurin Shugaba domin ya taimaka miki." Shugaba zurufu ya auki wata tsumburarriyar mujiya ya ora a asan Fulani Umaima nan take ta fara tsotsa tamkar wacce take cin abinci. "Ka yi alfahari da tsafi da sihiri Bamaguje tabbas za ta warke, da a ce wannan mujiyar ba ta sha gur ataccan ruwan nan ba da ba za ta ta a warkewa ba." Daga Bamaguje har Fulani Umaima rige-rigen sauke ajiyar zuciya suka yi, Bamaguje na shirin sake yin magana Shugaba ya katse shi. "Sai dai ba zan aiwatar da aikinta ba har sai na kammala sauran wa anda muka saka a gaba, yanzu dai ta tabbata ta cika al awarin da ta aukar mana na kawo gashin jikin Basiru da yarinyar nan." Da sauri Fulani Umaima ta hau gya a kai sannan Shugaba ya ebo tarin magunguna da kayan tsubbace-tsubbace ya dam a mata ha e da sallamarsu. Suna isa tsibirin Bamaguje Fulani Umaima ta dube shi cikin damuwa, sannan ta zayyane masa abin da yake tsakanin Yarima Muhsin da Jawahir. Sai da ya yi shiru kamar ba zai amsa ba sannan ya yace da dariya ya furta. "Kada ki damu da wannan Umaima, ki zuba idanu domin Shugaba Zurufu hatsabibin mutum ne. Tun da kika ji na jinjina wa zalinci da tsantsar mugun aikinsa kin san ba zan yi mana za en tumun dare ba." Jiki a sanyaye Fulani Umaima ta gya a masa kai, ta mi e cikin hawaye don duk lokacin da wannan naman hallitar ya tunku o mata ji take tamkar ranta zai fita. Fulani Umaima har ta fara tafiya Bamaguje ya ce. "Umaima!" Yanayin yadda ya yi maganar ya sa ta tsaya cak, sannan ta waigo tana share hawaye. "Ina son sanar da ke wata muhimmiyar magana amma ina tunanin ma'aunin da za ki jinginata, amma zan taushi zuciya har zuwa bayan warwarar matsalolin da kike ciki domin ranar wanka ba a oyon cibi." A wannan karon ma sake jinjina kanta ta yi don haka ta ci gaba da tafiya har ta koma cikin masarautar Huddam. Har Yarima Muhsin ya jima da fita Jawahir ba ta iya tashi zaune ba, sai can bayan wani lokaci tana kwance a uryar gado ta ji an aga labulen akin. Uwar soro ce ta saki murmushi sannanta ce. "Jawahiru wato yau kin tsokano wutsiyar an autan dodo ko? Wallahi sai kin yaba wa aya za inta." Daga haka ta fice daga akin tana sakin murmushin mugunta. "Ina tsananin aunarki! Saboda ke farincikina ce." Ra au kalaman Muhsin suka dawo cikin kwanyarta, take irjinta ya hau dakan lugude. "Ke fa baiwa ce me Yarima ya gani a jikinki da zai ce yana so? An ya ba kunnuwanki ne suke neman yaudararki ba?" aya daga cikin tsagin zuciyarta ya garga e ta. Tana nan zaune ta ga Mai gado ta fa akin kallo aya za ka yi mata ka fahimci tana cikin matsananciyar damuwa. "Wanne laifin kika yi wa Yarima da na ji an ce ya biyo ki har cikin aki? Jawahir wai me ya sa ba kya tunawa da matsayinmu a cikin gidan ne? Mu fa bayi ne antattu a kan me za ki dinga shiga hurumin an masu gida?" Lokaci aya Jawahir ta duburburce don ko karen hauka ne ya cije ta ba za ta ta a ce wa Innarta Yarima ce wa ya yi yaja sonta. "Inna tsautsayi ne ya sa na bige shi." Jawahir ta furta a sanyaye. "Ki shiga hankalinki Jawahir, kin san dai yadda Yarima yake a cikin gidan nan idan ba
Chapter 56 · 0% Book details