Sashe 45
Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
littafin da ke cikin akin kamar yadda Boka Shaddas ya ba shi umarni. SHU'UMAR MASARAUTA *Littafin ku i ne 500 idan kina bu ata za ki biya ta wannan Account in Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.* Kamar kazar da ta tono wu a haka Jawahir take tafe a sanyaye jiki babu wari sakamakon yankan aunar da mutuwa ta yi musu kwatsam babi zato babu tsammani, hawaye ne bibbbuyu suke zuba daga idanunta gabanta na ci gaba da fa uwa ta bi ta hanyar baya zuwa sashen Fulani babba tana jin wani irin aci a zuciyarta. Tun bayan da Mai gado ta sanar da ita mutuwar Fulani babba duk wani tsoro da firgici suka aurace mata, babba tashin hankalinta bai wuce ta isa ta ga gawar Fulani babba ba, duk da ba ta da tabbacin za ta iya kwalli da gawar saboda yadda take jin ta. A zaune yake a kan kujerar gefensa kayan marmari da kayan lambu ne ya zura musu idanu tamkar yana son gano wani abu daga jikinsu, a baya ya auki hu ubar mahaifiyarsa game da kishiyar mahaifiyar tashi amma sannu a hankali da ya fara girma ya sauka daga dokin zugar da hu ubar tsiyar da take yi masa. Ajiyar zuciya ya sauke sannan a hankali ya furta. "Allah ya ji anta." Kamar daga sama haka ya fara jin shasshe ar kukanta, karaf idanunsa suka sauka a kanta. Zumbur! Ya mi e tsaye gabansa na fa uwa bakinsa na rawa ya furta, "Ke... ke ... ce?" Cak Jawahir ta tsaya cikin ka uwa sakamakon ganin Yarima Muhsin a gabanta, a hankali ta fara ja da baya har ta ji bango ya tokare ta. Takowa ya fara yi don ya sake gasgata idanunsa ba gizo suke yi masa ba, ya auki kwana da kwanaki yana zama a wurin ko Allah zai sa ya ganta amma ko mai kama da ita bai ta a gani ba. Duk taku aya idan ya yi sai ya ji bugun irjinsa ya tsananta, ganin haka ya sa Jawahir ta sake mannewa da bango ta ha a hannuwanta biyu alamar ro irjinta na bugawa ta furta. "Don Allah ka yi ha uri ranka shi da e, wallahi rannan ma tsautsayi ne." Jawahir ta arasa maganar tana runtse idanunta ganin ya arasa kanta gadan-gadan, sautin ajiyar zuciyarsa ta ji a fuskarta tana bu e idanu ta ga ya yi mata rumfa. "Kin ga ire-iren zargin da ake yi wa su Salame, ko da wasa kada na kuskura na ga kin shige wa wani namiji. 'Yar iska ita ce take mu'amala da maza ko kina son ke ma a dinga kiranki da wannan sunan?" Jawahir ta tuna irin hu ubar da Mai gado ta yi mata watarana. Take jikinta ya auki karkarwa, ta fara yun urin ja da baya amma babu zato ta ji ya fisgo hannunta ta fa o jikinsa. Wani irin zuuuu Yarima Muhsin ya ji saboda azaba bai san lokacin da ya fa i can gefe ba, wata irin azaba ya ji tana ratsa hannuwansa cike da ra i kamar ya sa hannuwansa a wuta. Cije baki ya yi yana yarfe hannu bai yi tsammani ba ya ji kukan wata ba ar saniya a bayansa, a hargitse ya ago da mamaki yana kallonta don ko a mafarki bai ta a ganin saniya mai girma da ba i kamarta ba. uri ta yi tana kallonsa tamkar wacce take shirin gwabza fa a, a hankali ya fara ja da baya Saniyar ta fara tunkaro shi har sai da ya dangana da wata bishiya da ke bayansa. Tun lokacin da Jawahir ta ga Yarima Muhsin ya fa i can gefe ta iba a guje don tseratar da kanta, jikinta na karkarwa ta arasa sashen Fulani babba sai a lokacin ta tsaya ta daidaita nutsuwarta. Ta sauke ajiyar zuciya tana mamakin abin da ya jefar da Yarima Muhsin a asa har ta ji yana zuba ihu, Yariman da duk fa in masarautar nan babu wanda ake tsoro kamarsa. Wani sabon tsoron ya dirar mata, tana tsoron Allah ya sa ba wani abin ne ya same shi ba. "Ko dai shi ma an iska ne?" Jawahir ta fa a a zuciyarta, ba ta samu damar ba wa kanta amsa ba kawai ta kutsa kai cikin gidan sakamakon jin sautin kukan 'yan uwan Fulani babba da suka araso daga masarautarsu. Kalaman Dattijo Maharaz ba su sa Kamalu ya saki jiki sosai ba don haka a arare ya sake zura kansa, urawa cikin farin dutsen idanu ya yi sannu a hankali ya ga fuskarsa na riki a tana sauyawa. Mamaki ya sake mamaye shi, yana shirin agowa ya ga wani farin maciji sol ya kananna e saman kansa a firgice ya ta are ya zunduma ihu cikin tashin hankali. Tsoronsa ya sake ninkuwa sakamakon jin yadda afarsa ta li am da asa, sai da Dajjito Maharaz ya ci dariya ya more sosai sannan ya furta. "Da alama Masarautar Huddam na gabda samun shugaban da zai dinga nisha antar da su, wannan macijin da kake gani ba zai bar kanka ba matu ar ba ka sake sunkuyar da kanka saman dutsen ba." Ganin ba shi da wata mafita ya sa Kamalu ya sunkuya ga namakinsa sai gani ya yi macijin ya warwaro daga kansa ya fa a ciki. Kamalu na shirin agowa ya ga fuskarsa ta fito dal kansa auke da wani rantsattsan rawani mai matu ar kyau da aukan idanu. Da mamaki ya kai hannunsa saman kansa yana shafawa, ya sake mayar da kansa saman dutsen yana kallo. "Ka dangwali wancan ta on da tafin hannuwanka ka shafa a jikin katangar can." Ba musu Kamalu ya sa hannu cikin tabon mai matu ar dan o ya manna a jikin katangar kamar yadda ya ga sawayen wasu a wurin. Yana gamawa Dattijo Maharaz ya ja shi suka nufi wata hanya mai auke da wa ansu manyan tukwanen asa, girman kowacce aya za a iya saka mutum a cikinta. A kan tukunya ta arshe suka tsaya Dattijo Maharaz ya furta, " ora hannuwanka akai." Gaba aya Kamalu ya osa da wannan abubuwan da yake saka shi, sai dai kuma haka kawai ya ji zuciyarsa ta gagara bijire masa. Yana ora hannuwansa ya ji wata irin busar sarewa a saman kansa, da sauri ya waigo Dattijo Maharaz ya sakar masa murmushi, shi kansa bai san dalili ba amma ya ji wani kaso na acin ran da ke zuciyarsa ya kau. Daga haka suka juya har za su tafi daga can bayansu suka ji an furta. "Wane ne kai? Mene ne dalilin zuwanka wurin nan mai tsohon tarihi?" Galadina ya yi maganar yana shan gaban Kamalu. Tun daga ranar da Shugaba ya kar i ragamar Fargi ya ci gaba da arin sarrafa al'amuran tsafinsa yana ba ta horon da ya dace, sai ya kasance ta taso cikin warewa da iya sarrafa al aluman tsafi da sihiri mutane har mamaki suke yi. A lokacin da ta ka shekara bakwai a duniya a lokacin Shugaba ya sake tsufa don haka koda aikin tsafi aka kawo masa, kusan tare suke aiwatarwa, da yake ta kasance mai kaifin basira har ta fishi gudanar da aiki nan take. Sai ya zamana girmamawar da ake yi wa mahaifinta da Shugaba ta fara karkata zuwa kanta, mahaifinta ko ka an bai damu ba sai ma tarin farinciki da yake mamaye shi yake sake tabbatar da a wannan lokacin ne ya san ya samu magajiya. Shi kuwa shugaba Zurrufu a kullin ya bu i ido ya ga yadda aukakarsa take yin asa sai ba inciki ya mamaye shi, tsanar Fargi ta sake mamaye zuciyarsa watarana har sai da ya ji tamkar ya hallaka ta. Amma kuma sai ya danne don har yanzu akwai ga ar da yake son kaiwa domin cikar muradinsa. A lokacin da Fargi ta cika shekara takwas cif a duniya a sannan babu wani irin tsafi, sihiri da siddabarun da ba ta iya ba. Kai tsaye bokaye da 'yan tsubbun da ke wajen gari suke kawo mata aiki don neman taimakonta, kuma duk aikin da ta saka a gaba sai ta yi galaba a kansa. Cikin wannan shekarun na matashiya Fargi sai aka samu sauye-sauye da dama ta angaren tsubbu da ci gaban samuwar kayan tsafe-tsafe, hatta masu zuwa neman taimako wurinsu sun samu ci gaba domin a wannan lokacin ba Bokaye ne ka ai suke zuwa wurinsu ba daga cikin masu zuwa wurinsu sun ha a da; Sarakun, masu neman Mulki ko wata aukaka, 'Yan kasuwa da masu bulaguro, Maharba, Mafarauta, Masunta, Mahauta, 'yan bori da Matan aure musamman wa anda suke da kishiya ko kuma wa anda za a yi wa kishiya. Sai ya kasnce kawunan mutanen Rumzu ya fara wayewa har sukan gina bukkoki da rumfunan da suke zama suna hutawa, har ma suka fara samar da ananan rumfunan kasuwa wasu daga cikinsu sukan fita wajen gari su yo sarin wani abu su kawo cikin dajin nasu su sayarwa. A kuma wannan lokacin sai Fargi ta sake samun horo daga jinsin ba en aljanun ashin asa, bisa yadda za ta dinga sarrafa tsafi da shanu musamman ba e da jajaye don aiwatar da duk wani ulli da take bu atar ullawa. Matsala aya ce ta fara yun urin ci wa Fargi tuwo a warya na rashin samun wadatattun shanun aiki, a lokacin da ta kai orafinta wurin Shugaban ba en Aljanun Sarki Kadmar. Sun jima suna tattanawa sannan suka tsaida matsayar idan ta amince sai su dinga ban gishiri na baka manda, wato ita ta dinga yi musu yankan duk abin da suke so su kuma za su dinga ba ta duk kalar saniyar da take bu ata a lokacin da za ta yi wani aiki. Zuciyar Fulani Umaima fari tass ta nufi sashen Sarki Abdul'aziz sai dai tana zuwa ta yi tursss sakamakon ganin Takawa da ta yi zaune shi da Mahaifin Fulani Babba sun saka gawarta a gaba suna yi mata addu'a. acin ranta bai oyu ba har sai da ta bayyana a fili don ko ka a ba ta ji labarin Mahaifin Fulani babba zai zo jana'iza ba, tun da tuntuni mahaifiyarta da 'yan uwanta suka iso cikin Masarautar kuma