Sashe 75
Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
koma gida, kallon fuskokinsu ka ai zai tabbatar maka da unsassun labaran da suke tafe da su. Sai dai kuma arin wani farinciki tun mai martaba bai shiga cikin gida ba, ya samu kyakkyawan albishiri in samu lafiyar Yaya Halima daga ciwon haukan da take yi shekara da shekaru. Saboda tsabar farinciki Takawa da kansa ya nufi akin da Yaya Halima take zaune, jikinta duk a sanyaye ta bishi da kallo har ya arasa gabanta. "Halimatuna wai da gaske kin samu lafiya?" Hawayen da take ma alewa suka samu sukunin allewa, ta rushe da matsanancin kuka ha e da fa a wa jikinsa."Ranka shi da e wai ni ce na yi ciwon hauka? Kai ma ka yarda a baya na yi ciwon hauka?" Ajiyar zuciya ya sauke, ya sa hannuwa biyu ya zaunar da ita sannan ya furta. "Halimatu ba na son rigima, don Allah ina son ki kwanta ki huta zuwa dare zan zauna mu tattauna da ke." Gya a masa kai ta yi ya mu e ya fice daga akin. Kusan gaba aya iyalansa ya tara a babbar rumfarsa suka shiga mayar da abin da ya faru tun daga farko har ashe. "Ranka shi da e ba aramin mamakin abin da ya faru da yarinyar nan muka yi ba. Baiwa Zahra'u ta kai mata abinci za ta fito kenan ta ji ta wallah wata irin ara, ta shiga kururuwa kamar za ta tayar da gidan, da yar muka samu aka rirri e ta kawai sai gani muka yi yarinya ta fara wata irin zabura tana karkarwa. Daga nan kawai sai gani muka yi ta yanke jiki ta fa i, bayan an zuba mata ruwa ta farfa o sai gani muka yi tana bin mu aya bayan aya tana kallo. Daga haka ta fara wurgo mana tambayoyi har dai muka fahimci ta dawo hayyacinta." Fulani Sadi a kishiyar Mahaifiyar Fulani babba ta yi maganr cikin farinciki. Ita ce matar mai martaba ta hu u. Mai martaba ban da murmushi babu abin da yake, "Tabbas addu'a ba ta fa uwa asa banza kuma duk abin da ka yi ha uri za ka ci ribarsa. Allah ya sake shiga tsakanin na gari da mugu." Gaba aya suka amsa masa da Amin. Bayan ya sallame su ya bada umarnin a yi gumba, uli- uli da tuwon sadaka domin godiya ga Ubangiji bisa wa annan abubuwan farinciki da na akacin haka da ya same shi. Sannu a hankali Sarki Abdul'aziz ya sa aka ci gaba da ba wa Kamalu horon yadda 'ya'yan Sarki ke gudanar da al'amaransu, bai sha wata wahala ba tun da dama ya san wa ansu daga ciki al'adun don haka ba a auki lokaci ba ya goge tamkar ba shi ba. Sai dai har wannan lokacin bai fasa hul a da sauran abokansa na baya ba wa anda suka kasance 'ya'yan Bayi. Su Inna wuro tuni suka koma sashen da Sarki Abdul'aziz ya gina musu, ita kanta Mai gado a wannan lokacin Takawa ya ba su umarnin komawa wasu manyan akuna da ke ma otaka da sashen Fulani babba, sakamakon yadda take ba wa su Abubakar kulawar da ta dace tamkar ita ta haife su. Sai ya zamana ita ma Jawahir ta samu fada a wurin Sarki Abdul'aziz ya auke ta tamkar 'yar cikinsa. Haka kawai wani lokacin idan Mai gado take zuba wa Kamalu idanu tana jin walla na zuba mata. "Allah sarki rayuwa kenan, Allah ba ya ta a barin wani don wani ya ji da "Rayuwa darasi ce! Da ace mahaifiyarku na raye ban san irin farincikin da za ta yi ba, sai ga shi duk wata kulawa da farinciki da kuke samu asa ta tur e idanunta." "Allah Ya gafarta miki Fulani, ina ma kina raye Takawa yake ba wa iyakinki wannan kulawar da a kullin kike mafarkinta. Na sake aminta da ba kowanne abu ne mai rai yake nema ya samu ba." Ire-iren kalaman da Mai gado idan ta zauna zuciyarta ke sa a mata, sai dai a hakan ma ba aramin da i take ji ba don ba ta ta a tsammanin bayan rasuwar Fulani za su samu koda arzi in rabin kulawar daTakawa yake basu a yanzu ba. Kuma da faruwar haka babu jimawa Sarki Abdul'aziz ya rubuta wa Sailuba takardar saki har guda uku, a ranar Sailuba ta ci kuka tamkar ranta zai fita. Babu yadda ta iya haka ta tattara kayanta ta koma akin mahaifiyarta da zama. A wannan lokacin kuma duk lokacin da damuwa ta cunkushe Muhsin ba shi da wurin zama sai harabar wurin da ta raba akunan mahaifiyarsa da sashen da su Jawahir suka koma. Wani lokacin yana cin sa'ar ganinta wani lokacin kuma haka zai araci zamansa har ya tashi ba tare da ya ga gilmawarta ba. Watarana Kamalu na akinsa ya aiki wani Bawa a kan ya kira masa Jawahir, lokacin da sa on ya isa kunnenta kamar ba za ta je ba sai kuma Mai gado ta kora ta. Yana zaune a kan tabarmar kaba, ya ga ta yi masa erere a ka. "Lafiya ka aika kirana?" Jawahir ta furta erere daga tsaye. "Ki shiga ki gyara mini aki akwai kayan wankin da na ajiye ki ha a ki wanke su, idan kin gama ki dawo ki..." "Wallahi ni ba baiwarka ba ce, kai shaida ne ko wankin kayana wani lokacin Inna ke yi mini. Malam idan za ka ware wannan bunguzar rigar jikin naka ka share akinka ka wanke kayanka tun wuri ka ware, yoo Allah na tuba aikin arfi wanne iri ne ba ka iya ba. Lalla samun sararin kuturu ga a a cikin rama..." Da sauri Kamalu ya katse ta. "Ba na son sakarci ni kike fa a wa haka?" Baki sake Jawahir take bin sa da kallo. Ya mi e tsam ba tare da ya tanka mata ba, sai da ya datse ofar shigowa sashensa sannan ya zaro wata murtukekiyar dorina. A tsorace Jawahir ta ja da baya cikin zaro idanu. "Don Allah ka yi ha uri!" "Kura kenan ga tsoro ga ban tsoro, a haka ta nuna tafi kowa rashin tsoro amma kuma farar kura ce." Kamalu ya fa a a ransa. "Idan ba ki wuce kin aiwatar da abin da na saka ki ba wallahi sai ranki ya yi mummunan aci." Kamalu ya yi maganar cikin tsare gida. Kamar sabuwar munafuka haka Jawahir ta sunne kai asa ta wuce tana aikin lokaci-lokaci tana yi masa Allah ya isa asa- asa don kar ya ji. "Mai martaba mun tako ne sakamon mun samu labarin duk abin da faru, na da i da rashinsa, don haka muka ce afa da afa sai mun araso. Allah ya kiyaye gaba, Muna taya ku murna matu a da bayyanar wannan yaro Kamalu." Sarki Sulaiman ya furta bayan sun gama gaisawa da Sarki Abdul'aziz cikin mutumci da karamci. "Mai martaba Sarki Sulaimanu kuma fa fa uwa ce ta yi daidai da zama." Sarki Abdul'aziz ya fa a yana gyara zama. "Ai haka ake so Sarki Abdul'aziz wacce magana ce a bakinka?" "Maganar auren yaran nan, dama a cikin raina nake shirin turo da Shamaki domin ya nemo mana izini a wurinka. Za mu zo gaisuwar iyaye da kawo ku in na gani ina so." Fuskar Sarki Sulaiman ta sake fa a da fara'a." "Muna muraba da wannan maganar Sarki Abdul'aziz Ubangiji ya tabbatar mana da alherinsa." Sarki Sulaimu ya furta sannan suka amsa lokaci aya. Tun Jawahir na no ewa har ta sake jikinta ganin yadda Kamalu ya tsare gida yake buga mata tsawa, wani abin takaici da ya cika ta bai wuce yadda ya bu ofar gidan Bayin da ke hidima a sashensa suka dinga shiga suna ganin irin wula ancin da yake yi mata ba. Sai da ta gama wanke jinga-jibgan rigunan alkyabbunsa sannan ta koma gefe tana yarfe gumi, tausayi ta ba shi har ransa, ya gintse murmushin da yake cinsa. "Akwai alkaki da nakiya a rumfa idan kin gama." Harara ta wurga masa murya a ciki ta furta. 'Ba na ci." aga kafa a ya yi cikin halin ko in kula ya juya zai shiga aki Bawa Bala ya arasa cikin girmamawa ya zube asa ya furta. "Allah ya taimake ki Takawa yana bu atar ganinka yanzu." Da kai kawai Kamalu ya amsa wa Bawan ya juya, hanyar fita ya nufa take wasu Bayi maza guda biyu suka rufa masa baya. Hannu ya aga musu da sauri suka koma ya ci gaba da tafiya, wafa Jawahir ta yi tana bin igiyar da ta shanya kayan da kallo wani takaici ya sake lullu "Da ace ina da iko da tuni na kar a na fanshe ki masoyiyata." Kalaman Bawa Auwalu ya ratsa ta, ba tun yau Auwalu yake nuna mata soyayya ba amma ko ka an ba ta ba shi fuska ba. Harara ta watsa masa ta fice daga gidan, har za ta wuce sashensu wata dabara ta fa o mata. A fili ta saki murmushin eta don ta ci alwashin Kamalu ba zai ci banza ba a kan mugunta da wula ancin da ya yi mata, sai da ta shiga sashensu ta sauya kayan jikinta sannan ta nufi sashen Sarki Abdul'aziz. Bakin Kamalu auke da sallama ya shiga akin saukar ba in Sarki Abdul'aziz, sai da suka amsa masa sannan ya shiga ciki. A asa ya zube cikin girmamawa ya dubi Sarki Sulaiman ya furta. "Barka da zuwa ranka shi da e, da fatan an samu al'ummar Masarautar Huddam lafiya." "Barka dai Sadauki, ya fama da jama'a." Sarki Sulaiman ya furta ya saka hannu a cikin aljihunsa. "Jama'a Alhamdulillah ranka shi da e." Wa ansu zobunan azurfa ne guda uku dukkansu duk iri aya, ya mi a wa Kamalu sannan ya furta. "Ga kyautar azurfa daga gare ni, ga kuma arin alkyabbu ka auki naka da na sirikina sai kuma da abokin tagwaitagarka." Sarki Abdul'aziz ba aramin farinciki ya yi ba. "Muna godiya ranka shi da e, Allah ya ara wa Sarki lafiya. Ubangiji ya tsare gabansa da bayanka." Cikin jin da i Sarki Sulaiman ya amsa da "Amin ." Ya dubi Sarki Sulaiman. "Sarki Sulaimanu me ya sa ba ka gajiya? A ce duk lokacin da za ka ziyarce mu sai ka...?" "Kyauta ce daga mahaifi zuwa wurin 'ya'yansa."