Sashe 51
Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
take gumi ya shiga keto mata. "Ka da ka mini haka Bamaguje, Umaima duk ba ta san wannan ala ar da ke tsakaninku ba, ka yi ha uri kada ka hallaka ta." Bamaguje bai tanka mata ba ya nuna wurin da Umaima ke ame ya nuna ta da sanda, take ta zube asa yaraf cikin kururuwa da tashin hankali ta shiga kwalla ihun azaba. Da wata irin murya ya ambaci sunanta mai amsa-amo, nan take Fulani Umaima ta shiga nutsuwarta. A tsorace ta sake ja da baya don ba aramin tsoron Bamaguje ne ya mamaye ta ba, jikinta na karkarwa hawaye na zuba ta matsa ta ci gaba da ja baya. "Ki zo nan! Idan ba haka ba ranki zai yi mummunan aci." Tun bai rufe baki ba ta tafi da sauri ta zube a gabansa. "Ka yi mini rai, tuba nake Bamaguje wallahi ba zan sake..." "Dakata!" Bamaguje ya katse ta rai a matu ace, ta sha ganin acin ran Bamaguje da dama amma ba ta ta a ganin irin acin ransa na wannan ranar ba. "Kalli can." Ya furta mata yana nuna mata sihirtaccan bangon dutsensa. Daga mahaifiyar Umaima har ita rige-rigen kallon wurin suke, nan take hoton Jawahir ya bayyana a dadai lokacin da take ulo butar da Umaima ta binne har zuwa zuba ruwan da ta yi a sashenta. Sai da suka gama gani hoto mai motsin ya auke. "Ba ta san kin binne ba, ba ta ganki a lokacin da kika binne ba hasali ma da ace wani ya ganki a lokacin sa kike gudanar da aiki, daga mutuwar kishiyarki har zuwa oyin jikin Sailuba ba zai ta a tabbata ba. Wace ce ita? Kuma wa ya sanar da ita wurin da kika binne har da yadda za ta gudanar da makarin aikin?" Bamaguje ya watsa wa Umaima tambayoyi fuska a ha "Wallahi ban santa ba, ban san wa ya sanar da ita ba. Hasali ma ban ta a saninta a cikin masarautarmu ba, ina tunanin ma ila Jakadiya ce za ta turo ta..." "Da ace Jakadiya ta san da wannan ba za ta nemi agajin kowa ba da kanta za ta tone ba tare da wani ya sani ba, kuma yarinyar nan na rayuwa a cikin masarautarku don haka ina bu atar ki shiga lungu da sa on masarautar ki kawo mini ita. Ina son sanin wace ce ita? Domin na tabbata banza ba ta kai zomo kasuwa, wannan asirin ba ita aka yi wa ba, ba ta da ala a da masarautar nan me zai sa ta tone asirin tun da ba amfani zai yi mata ba." Shiru Fulani Umaima ta yi tana nazari sannan ta furta. "Zan yi duk yadda ka ce Bamaguje." "Kina shashanci anki Basiru ta auke littafina ya kai wa mahaifinsa, ki sani wannan shi ne kuskure na farko da kika tafka a rayuwarki. Kin yi biyu-babu, domin butar da aka tone ita ce jigon mallakar da aka yi wa Sarki Abdul'aziz, kin rasa zuciyarsa kin rasa iko da mallakar da kike masa Umaima. Kin san a yanzu wacce nasara ka ai ta rage miki?" Da sauri Fulani Umaima ta girgiza kai, nasararki aya an binne kishiyarki da fatar da kika saka mata a asanta wanda hakan zai sa har abada Sailuba ba za ta warke ba, amma bayan wannan ba na jin akwai wata ragowar wata nasara da kike da ita." "Kana nufin a yanzu Takawa zai iya juya mini baya?" Umaima ta tambaya cikin tashin hankali. "Ki rabu da maganar Takawa ki ji da annobar da kika haifo Umaima, kin fi kowa sanin rashin tausayi da arfin zuciyata tun da na jimanta miki haihuwar an bokan da kika yi kin san tsugunne ba ta are miki ba. Basiri sai ya zame miki annobar da za ta nemi gagare miki domin mahafinsa ya jima da tsaface shi. Na san mahaifinsa Shaddas hatsabibin gaske ne kuma akwai wata 'yar ji iyar tsattsamar ala a a tsakaninmu don haka babu wani abu da zan iya yi miki akai, ruwanki ne ki je wurinsa ku sasanta domin ya sakar miki anki, ruwanki ne kuma ki bar masa shi gaba aya. Ku tashi ku ba ni wuri, Umaima sai na ji daga gare wato kawo mini yarinyar da za ki yi. Wata ila na tausaya miki idan akwai wani taimakon da zan iya yi miki." Fulani Umaima har ta bu e baki za ta yi magana Mahaifiyarta ta dakatar da ita, a sanyaye suka mi e suka yi masa sallama sannan suka koma cikin masarautar zuciya babu da Mahaifiyar Umaima fa a ta yi mata sosai cikin acin rai, Fulani Umaima tana hawaye ta sanar da mhaifiyarta duk abin da ya faru tsakaninta da Basiru. Babban tashin hankalinta bai wuce yadda Bamaguje ya tabbatar mata ta zarginta a kan Basiru ba, don ta jima tana ora ayar tambaya a kan shi. "Kamalu shin ka ji zafin maganar da ta su uce daga bakinmu har ka nemi aurace mana ne? Allah ya sani ba ni na haife ka ba Kamalu amma yadda nake jin A'iru haka nake jin ka a cikin zuciyata..." Da sauri Kamalu ya katse Baffajo. "Don Allah ka daina haka Baffajo, wallahi ba haka ba ne! Kuma daga yau ba na son ku sake kallona a matsayin wanda ba ku kuka haifa ba, da ku na rayu da ku na bu e ido don haka ba ni da wasu iyayen bayanku. Na fahimci kowanne an'adam da kalar tashi addarar Baffajo, wannan ita ce tawa addarar kuma ina godiya da Allah ya jefa ni hannunku. Wata ila ma zamana a gabanku shi ne mafi alheri a rayuwata." Cike da jin da i Baffajo ya rungume Kamalu sannan suka arasa wurin Inna wuro da ke cikin aki cike da damuwa. Kwanan Mahaifiyarta aya suka tattara suka koma masarautarsu, Fulani Umaima ta shiga cikin matsananciyar damuwa lokaci aya ta fige ta rame wa anda ba su san halinta ba har gani suke tamkar mutuwar Fulani babba ce ta buge ta. Sai da aka shafe kwana uku cif Fulani Umaima na shige da ficen son ganin ta gano wannan baiwar da Bamaguje ya ba ta umarni a kanta amma ko mai urmushin kamarta ba ta gani. 'Yan uwan Fulani babba na matu ar ba wa Abubkar kulawar da ta dace, a haka kwanaki suka shu e har aka yi addu'ar sadakar bakwai suka tattara gaba aya suka koma masarautarsu. Mahaifiyar Fulani babba ta so a ba su Abubakar ta tafi da shi, amma sai Takawa bai amince da hakan ba don a lokacin wata irin soyayyar Abubakar da sauran 'yan uwansa yake ji har cikin ransa. Kuma a wannan lokacin ne Sarki Abdul'aziz ya zartar da umarnin gaba aya Bayin Fulani babba na baya za su ci gaba da ba wa Abubakar kulawar da ta dace, Mai gado ba aramin farinciki ta yi da jin haka ba. Don haka ita da Baiwa Zainaba suka ci gaba da ba shi kulawa kamar yadda suka yi wa Mahaifiyarsa al awari tun tana raye, kuma da yake ya saba da su sosai babu wata matsala da ake samu daga wurinsa. Duk yadda Muhsin ya so kawar da Jawahir daga zuciyarsa abin ya gagara, a angare aya kuma ga jinyar hannuwansa da yake yi don ma onuwar ta fara warkewa. Ya sha tambayar kansa inda yarinyar take amma duk yadda ya kai ga yin bincike ya gagara gano ta, tun yana mu'amala da 'ya'yan bayi a tunaninsa za su gusar masa da sha'awarta har ya ha ura ya watsar. Idan tunaninta ya yi masa yawa har gani yake ko gamo ya yi da aljana bai sani ba take wahalar da rayuwarsa. A yadda yake jin aunarta gani yake ko aljana ce zai iya zama da ita ko da kuwa zai koma cikin jinsin aljanu da zama. Sai da Sailuba ta gama sauraron Jakadiya ta share hawayenta cikin matsananciyar damuwa ta furta. "Yanzu Inna shi kenan haka zan dawwama cikin wannan warin? Ki duba ki ga irin korar karen da Takawa yake mini." Jakadiya ta an juyar da kai ta tsartar da yawu saboda warin da ya bugo ta sannan ta furta. "Wannan matsalar za ta zo arshe ki bar aga hankalinki Sailubata, babban burina na cika wa Boka Shaddas al awarinsa. Yanzu bari mu fara da wannan kuliyar." Jakadiya ta zaro yamusasshiyar Magen da Boka Shaddas ya bata, ta orata a kan wani ba in jini mai wari nan take Magen ta fara lasa jikinta na kammaninta suka fara riki a suna sauyawa. Sannan ta fara ambatar sunan Fulani Umaima sau uku, tana gama ambatar sunan Fulani Umaima ta sunkuya daidai kan magen da kallon wala- walan idanunta kan iya tsorata mai kallonta ta furta. "Maza ki dawwama kina ambatar sunan Umaima da muryar tsoratarwa, ki saka mata wasu-wasi a kan muryar marigayya Fulani babba. Maza ki tafi da izinin Boka Shaddas da sirrin tsafinsa." Rufe bakin Jakadiya babu wuya sai magen ta fice a guje ta bi ta saman katanga, kai tsaye ta wuce sashen Fulani Umaima, ta shige akinta da shigarta babu jimawa ta ace daga kamar babu ita. Fulani Umaima na zaune ta zuba tagumi kamar a mafarki ta ji muryar Fulani babba tana fa in, "Umaima kin cutar da ni." A firgice ta ago tana waige-waige cikin tashin hankali. *SHU'UMAR MASARAUTA* *27* *Littafin ku i ne 500 idan kina bu ata za ki biya ta wannan Account in Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.* Tun daga ranar da mahaifiyar Fulani Umaima ta sa afarta ta bar masarautar ta du ufa wurin ganin ta yi duk abin da za ta yi dangane da 'yar uwarta Fulani Asabe. Tun a lokacin ta so Bamaguje ya kashe yayartata amma sai hakan ya gagara sakamakon da ragowar kwanakinta a gaba, dalilin haka ya sa ya yi musu aikin rufin baki ta yadda Fulani Asabe da su Galadima ba za su ara maganar mulki ko rabuwar Umaima da Sarki Abdul'aziz ba. A haka rayuwa ta ci gaba da tafiya tsakanin Fulani Umaima da Fulani babba babu wani zama mara da i, sai dai tun da Umaima ta auri Takawa kyakkyawar ala ar da ke tsakaninta da shi ta