Sashe 44
Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ji kamar ana fisgar hannunta, ta ja da baya da sauri a tsorace. "Wacce matar kika gani, kuma yaushe Jawahir?" Mai gado ta tambaye ta a firgice. "Inna ina arar gya a kawai na ji cikina yana zafi..." Take ta kwashe duk abin da ya faru ta gaya wa Mai gado. Kamar wacce ruwa ya cinye haka Mai gado ta yi shiru, fargaba, tsoro da tashin hankali suka mamaye ta. "Kada ku damu da sanin zubi da surar halittata, wannan 'yar tawa ita za ta fayyace muku asalin jinsin halittar da na fito." Kalaman mahaifiyar Jawahir suka dawo wa Mai gado cikin kunnenta, da yake zuciyarta a dagule take nan take ta sake fashewa da kuka domin ba ta za in da ya wuce yin kukan. "Inna wallahi tsoro nake ji ta ce abin bauta zai yi fushi da ni." Mai gado ta dafa ta a sayaye. "Kada ki damu Jawahir idan Malam ya shigo zan sanar masa halin da kike ciki, babu abin da zai faru da ke sai alkairi." Mai gado ta furta tana kallon Jawahir. "Inna wallahi Fulani babba ta ce ki daina hana ni shiga wurinta, don Allah ki bari na je kitso zan yi mata." "Daga wurin Fulani babba nake na ci abinci kuma ga alkaki ta ce a kawo miki." "Inna kin ga sabbin kayan da Fulani ta ba ni wannan ma warwaronta ne da yari ta ce na je na sanya ranar juma'a." "Wallahi Inna Fulani tausayi take ba ni idan na ga tana kuka kamar ba matar Takawa ba, Allah da ina da dama sai na kori Fulani Umaima daga gidan nan." Ire-iren kalaman Jawahir na baya suka shiga dawo wa Mai gado, wanda Jawahir take gaya mata game da Fulani babba. Duk da ta san babu abin da suka ha a da Fulani amma akwai sha uwa don haka tausayin Jawahir ya kamata ta san jin mutuwar Fulani babba ba aramin ka a ta zai yi ba. "Inna kukan me kike azu." "Ina koka mana game da sabuwar rayuwar da za mu fuskanta nan gaba Jawahir, ina koka mana maraici, ka aici da alhinin da za mu shiga. Ta kasance gatanmu a lokacin da ba mu da gata, ta rungume mu hannuwa bibbiyu tamkar ba bayi antattu a wurinta ba." Take gaban Jawahir ya fa "Jawahir mun rasa Fulani Babba Allah ya yi mata rasuwa shi kenan Jawahir..." Kalaman Mai gado suka katse sakamakon kukan da ya ci arfinta. "Ki je sashen Sarkin cikin masarautarku ki tone abin da matarsa ta binne idan ba haka ba, Fulani babba za ta mutu. Idan kika bari Fulani Umaima ta ci gaba da yin nasara a cikin masarautar nan ina mai tabbata miki sai ta yi nasara akanki. Sai ta dam a ruhinki wurin hatsabibin boka Bamaguje, kuma ki sani idan kika bari rihinki ya je gare shi babu wani taimako da ni ko abin bauta za mu yi miki. Kin ga kenan an arar da gishiri duka a dahuwar aho ba tare da bu ata ta biya ba, na tashi a banza ba tare da cikar muradina ba." Kalaman matar da ta zo mata a mafarki wacce ta gani a azu suka dawo mata, hantar cikinta ta ka a zuciyata ta hau dakan lugude tamkar za ta yi tsalle ta hudo irjinta. "Mutuwa fa Inna? Kina nufin Fulani Babba dai tamu ce ta mutu." Salatin da suka ji daga waje da kururuwa ne ya sa Mai gado ta yi saurin fita, wasu daga cikin Bayin tuni suka fara koke-koke da kururuwa wannan ta sa jikinta ya sake yin sanyi don ta fahimci labarin mutuwar ya zo gare su. annan sawayen hannuwana tsofaffin Sarakunan masarautar da suka yi zamani a masarautar nan ne, wannan ramin ta on da kake gani tun zamanin mahaifina ya ha a shi. Dubi can ka gani." Dattijo Maharaz ya nuna wa Kamalu wani farin dutse cikinsa wani mudubi ne mai aukar ido. "Le a fuskarka ka gani!" Babu musu Kamalu ya le a fuskarsa, a an razane ya ago kansa cikin tsoro. Dattijo Maharaz ya saki murmushi, "Kada ka tsorata Sadauki sake le a fuskarka hakan ya kasance tamkar sunna ne a cikin masarautar nan ga duk wani mai matu ar muhimmanci gare ta." Kafin wani lokaci tuni maganar mutuwar Fulani babba ta zaga lungu da sa on da ke masarautar Huddam, mutane da dama sun jimanta mutuwarta kama daga cikin Bayi Kuyangu, Dogarai Hadimai da duk wa anda suke rayuwa a cikin masarautar. Duk wanda zai bu e baki sai dai ya fa i alkairi da kyawun halinta, a angare guda kuma mutane suka fara jimanta yanayin sabuwar rayuwar da Abubakar zai fuskanta ta maraici a nan gaba. Tun ba a auki lokaci ba Sarki Abdul'aziz ya sa aka rubuta wasi a zuwa masaarautar Mahaifan Fulani babba domin a shaida musu da mutuwarta cikin gaggawa, tun daga cikin gari har zuwa sauran asashen da ke ma ota da asar Huddam suka shiga aiko masa da tarin takardun ta'aziya. "Ha a mun yi babban rashin da har abada ba za mu samun gurbin da zai maye mana shi ba, Allah ya huci zuciyar Mai martaba ya sanya maka dangana. A madadina da na iyalan asa da masarautar Huddam muna mai yi maka ta'aziyar rashin Fulani Babba." Fulani Umaima ta arasa maganar cikin zubar da walla. Sai da ya share walla ya dube ta. "Shi kenan fa Fulani ta yi nisa da mu? Umaima kina ganin zan ci gaba da jin da in gudanar da al'amuran mulkin asar nan a yanzu." "Idan ba za ka iya ba ai sai ka yi murabus ka dam awa Yarima Muhsin tun dama a yanzu ya kawo arfi." Ta furta a zuciya tana watsa masa harara a fakaice. "Da taimakon Allah ka haye wannan karagar Sarkina kuma na tabbata da taimakonSa za ka ci gaba da gudanar da al'amuran masarautar nan. Ka yi tawakkali domin Ubangiji da ya ba mu Fulani Shi ne ya bu ace ta a daidai wannan lokacin. A wannan lokacin addu'armu ka ai Fulani take bu ata Ranka shi da e." Ajiyar zuciya ya sauke idanunsa ya runtse da suka yi jawur. "Ina sake alfahari da ke Umaima Allah ya yi miki albarka, ita kuma halinta na gari ya bita." Fulani Umaima ta sunne kai asa sannan ta amsa. "Amma wani hanzari ba gudu ba ranka shi da e, na ce mai zai hana idan aka shirya Fulani a dawo da ita sashenka tun da dai kwanan keso za ta yi ina ga sai ya fi don ka samu damar yi mata addu'a cikin nutsuwa, addu'arka na da matu ar tasiri a gare ta. Ni kaina zan zauna tare da kai don abin da ya yi Fulani shi ya yi ni, kaico rayuwar duniya kaico mutuwa ta yi mana yankan auna." Fulani Umaima ta arasa maganar tana fashewa da matsanancin kuka. Jikin Sarki Abdul'aziz ya yi sanyi, don haka kai tsaye ya amsa a ganinsa zancen da Fulani Umaima ta yi har a zuciyarta ma haka ne. A tsaye yake ya yi tsirara a bakin wata orama wacce take cike da jini, mamaki ne ya matu ar kama shi sakamakon wayar gari da ya yi ya tsinci kansa a wurin kamar yadda yake yawan ganinsa a mafarki. Waigawa ya yi yana arewa ba on wurin kallo yana tunanin inda ya ta a ganinsa a makamancin wurin nan. Yana shirin yin magana yaji an she o masa wani ruwa kamar an aurye namansa sannan aka fara wa ansu irin surutai da ba ya iya gane su, an jima ana abu aya sannan ya ji an sake kwara masa ruwan a jikinsa. Ta cikin oramar jinin ya ga wani mutum ya fito daga ciki hannunsa auke da wata gajeriyar wu a, ba a wuluk sai she i take yi. Mamakinsa ya sake ninkuwa sakamakon ganin matsananciyar kamar da suke yi da mutumin. "Ba kai ba ne shugaba da nake yawan mafarki da shi?" Boka Shadda ya bushe da dariya, "Ba kama ba ce taurarona ni in dai ne." Yawu Basiru ya ha iya cike da mamaki. "To ya aka yi na gan ni a nan? Wai ma wane ne kai?" Basiru ya yi maganar a zuciyarsa. Bai gama sa a da warwara ba ya ji mutumin ya fesa masa wani ruwa a fuskarsa, take ya ji wani yanayi ya ratsa shi zuciyarsa ta shiga azalzalarsa, babu zato mutumin ya burma masa wu ar hannunsa a ahon zuciyarsa sai dai ko ka an bai ji zafi ba sai ma wani irin sanyi da ya fara ratsa ilahirin jikinsa. Ya waiga cikin sanyin jiki yana kallon boka Shaddas. "Ungo saka rigarka!" Boka Shaddas ya furta yana mi a masa kayansa, babu musu Basiru ya kar i kayansa ya fara sawa Shaddas ya furta. "Daga nan maza ka je akin mahaifiyarka ka bu e akwatin da take oye duk wani sirrinta, za ka ga wani tsafataccan littafi ka kawo mini. Kada ka manta duk abin da za ka yi mini domin nasararmu ce, kai jajirtacce ne kada ka ba ni kunya magajin babban bokan da babu kamarsa a fa in nahiyar nan." Jin kanbabawar da Boka Shaddas yake yi masa ya sa Basiri sake samun warin gwiwa bayan wankan tsafin da aka yi masa, cike da arfin zuciya ya fice daga cikin kogon tsafin. Lokacin da ta ji labarin an kai gawar Fulani babba turakar Takawa farinciki ne ya lullu e ta, aurarriyar fatar da ke hannunta ta shiga juyawa tana sakin murmushi a hankali. Babban mayafi ta auko ta na e jikinta da shi sannan ta lalubo carbin da sai da ta sha wuya kafin ta samo shi, ta soke ulalliyar fatar wurinta ta janyo auren akinta ta fito, sannan ta garga i Bayinta da ko da wasa kada wanda ya tura mata aki kai tsaye ta nufi sashen Sarki Abdul'aziz da udurin duk rintsi sai ta aiwatar da mugun udurinta kafin gawar Fulani babba ta bar wannan gidan. Tana fita Basiru ya fito daga bayan katangar da yake oya, ya saki dariyar farinciki mummunar fuskarsa ta sake tur unewa sannan ya fa a cikin akin mahaifiyarsa, da niyyar cim ma urinsa da na shugabansa don ya ci alwashin duk rintsi sai ya auko