Sashe 3
Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
ba ta isa ta ara koda taku aya ba. Fulani na zuwa sai da ta fara iban wani jan ruwa a cikin wani on kan warangwal ta wanke fuskarta, sannan ta nemi wuri ta zauna tana fuskantar Boka Bamagujen dutse. "Barka da aiki uban gidana." Jinjina kai ya yi ya furta. "Barkanki Fulanin Sarki Abdul'aziz." Shiru ne ya ratsa Fulani Umaima ta kawo ido ta sa wa Bamaguje, ya saki murmushi don ya san wace ce Umaima. Ga tsananin bu ata fal irjinta ga kuma ta ama da izzar mulki, kallo aya ya yi mata ya fahimci halin da take ciki. "Umaima kin yi ari." "Sanin haka ya sa na kawo ziyara a ranar da ka bu ata." Ta amsa masa a ta aice. "Kin aiwatar da komai yadda ya kamata, don haka kishiyarki ita da Sarki Abdul'aziz sai kallo sai hange daga nesa. Matu ar ba asirin nan ne ya karye ba, ba na jin kishiyarki za ta sake aukan ciki a doron asar nan. Ke ba ma ciki ba ina mai tabbatar miki ita da sake yin wata mu'amala da Sarki Abdul'aziz sai dai a lahira idan ana yi. Ina ragowar kayan aikin?" Ya wurga mata tambaya. Jin haka ya sa Umaima ta saki malalacin murmushi ta ebo gashin Fulani babba da gashin Sarki Abdul-aziz, ha e da asar ma abarta da ta gidan tururuwa ta mi a masa ba tare da ta tanka masa ba. "Mun sakar mata lalurar fitsarin kwance, kuma mun saka mata lalurar mantuwa da warin jiki." Bamaguje ya fa a yana jefa tarkacen da Fulani Umaima ta bashi a cikin wata tunkunya da ke cike da jini tana tafasa. Kusan duk abin da suke tattaunawa Maimuna tana jin su, haka kawai ta ji tausayin uwar akinta ya arsar mata. Musamman da ta tuna zallar cin amanar da take yi mata mai ha e da zagon asa. "Ina maganar cikin jikinta ya kwana?" Fulani ta tambaya cike da izza. Bamaguje ta ebi wani jini mai yau i ya watsa a jikin wani allon farin arfe. Take wa ansu inuwoyi suka bayyana, yana fara nazartarsu sai gani ya yi uff komai ya auke. Cikin da damuna ya sake iban jinin ya watsa har sai da ya yi haka sau uku sannan ya dubi Umaima cikin damuwa. "Kishiyarki a daren yau za ta haihu!" Dum! Fulani ta ji tsakiyar kanta ya sara kamar wacce aka buga wa guduma. Rai a ace ta dube shi. "Wanne irin mugun labari nake ji haka, zancen banza kenan afa ta mutu ta bar takalmi. Cikin jikinta ya fi komai aga mini hankali..." Da sauri ya katse ta. "Tun fil azal kundunsa rubuce yake da zanen addararsa, cikin kishiyarki shu'umin ciki ne lullu e yake da almara tamkar yadda masarautarku ta kasance SHU'UMAR MASARAUTA. Kamar yadda na gaya miki a yau za ta haihu..." Duk dakiya da arfin zuciya irin ta Fulani Umaima sai da hawaye ya su uto mata, Bamaguje ya tsaya yana kallonta ha e da jinjina kai. "Yau shekarata biyar kenan a cikin masarautar nan ko atan wata ban ta a yi ba, tun Fulani babba na da goyon fari Takawa ya auro ni. Bamaguje kana son na are rayuwata cikin anci da rashin mamora?" Girgiza kai ya yi, ya sauke ajiyar zuciya. "Wa ya ce miki ba za ki haihu ba?" Fulani ta zuba masa idanu zuciyarta na bugawa. "Yanzu haka kina auke da juna biyu na tsawon makwanni uku." Kamar a mafarki haka ta ji kalaman Bamaguje na ratsa majiyar sautinta. "Ki yi imani da ni Umaima matu ar ina numfashi ba za ki tozarta ba." Sanyi ta ji har cikin ranta. "Da kai na dogara Bamaguje na yi imani da kai tun da ba ka kunyata mahaifiyata ba na tabbata ba za ka tozarta ni ba." Ta yi maganar a raunane. Wata atuwar kunama ya auko da hannunsa ya ce, "Ba ni hannunki." A firgice ta wurga masa kallon baka da hankali, ya saki murmushi don ya fahimce ta. "Umaima kenan kura kike ga tsoro ga ban tsoro." Umaima ta ha e fuska kamar ba ita ba. "An ya kuwa? Kar fa ka manta ko kura ta rame ta fi arfin gawurtattun karnuka, dalilin haka ya sa masallacin kura ba a ba wa kare limanci." Murmushi Bamaguje ya yi. "Kwantar da hankalinki kamar kin fa a rijiya. Matso kusa ki ji." Bamaguje ya furta. Tun bai rufe baki ba Umaima ta matsa kusa da shi, ra a ya yi mata a cikin kunne lokaci aya ta bushe da wata iriyar dariya cike da farinciki. Ta koma mazauninta na farko tana sauraronsa. "Ki tabbatar da kin aiwatar da abin da na umarce ki, don kuwa kowa rai ya yi wa da i ba ya mai shi ba." "Bamaguje kenan! Ai ranar biyan bu ata rai ba a bakin komai yake ba." Umaima ta furta cike da nisha i. Kashe mata ido aya ya yi yana are mata kallo, ganin haka ya sa ta fahimci inda ya dosa. "Tukwina fa?" "Ka sallame ni kenan?" Ita ma ta wurga masa tambaya. Gya a mata kai ya yi Umaima ta mi e babu ko kunya ta sauke rigar tsubbun jikinta, Maimuna ta sunne kai asa zuciyarta na bugawa. A fakaice take are wa tsohon kallo cike da yami don ko ita da take baiwa gani take ba za ta iya ha a jiki da shi ba. Bamaguje na shirin ora hannu a jikinta ta an ja da baya ha e da sakin murmushin mugunta. "Na sadaukar maka da kishiyata a wannan daren, shi ne tukwicin da zan iya yi maka." Ba ta jira cewarsa ba ta ora rigar a jikinta. Bamaguje ya gya a mata sannan ya furta. "Za ku iya tafiya." Umaima ta yi masa jinjina da hannu sannan ta sake iban ruwan da ta wanke fuska da shi ta nufi wurin da Maimuna ke zaune hannunta auke da kunamar da Bamaguje ya dam a mata. Abin da suka aiwata a farkon zuwansu yanzun ma haka ne ya faru, sai da suka koma daidai wurin da suka bu e ido suka gan su tun farkon zuwansu sannan, Fulani Umaima ta aga ahon ta runtse ido ta busa ha e da kiran sunan Bamaguje. amshin akin Fulani ne ya ankarar da Maimuna dawowarsu gida, cike da girmamawa ta zube asa ta furta. "Allah huta gajiya uwar gijiyata." "A kullin ina sake jaddada miki bakinki anin afarki Maimuna, duk ranar da kika bari kwa arki ta yi ruwa na ji sirrina ya fita za ki bambamce mini tsakanin tsaba da tsakuwa." Fulani ta yi maganar cikin sigar garga i. "Maimuna ta du a kai asa. "Wace ni uwar gijiyata? Kada Allah ya nuna mini ranar da zan aikata miki wannan zunubin ranki shi da e." Fulani ta ta e baki, "Za ki iya tafiya." Da sauri Maimuna ta fice ko waige ba ta yi. Har za ta nufi sashen su na bayi sai uwar akinta Fulani babba ta fa o mata. Haka kawai ta ji sam ba ta kyauta ba. Zuciyarta ta ci gaba da azalzalarta da ta je ta ga halin da take ciki. Cikin san a ta nufi sashen Fulani babba gabanta na fa uwa. A haka ta ci gaba da tafiya har cikin akin, ras! irjinta ya buga jikinta ya auki karkarwa sakamkon ganin Fulanin a yashe babu sutura a jikinta. Wani tafkeken maciji ta gani a tsakanin afafuwanta ya kafa kansa a saitin asanta, ga wani irin gurnani da macijin ke yi. Idanun Fulani a rufe amma sai mutsu-mutsu take yi, da alama ma bacci take yi. Daga bayanta ta ji an dafa kafa arta, wani abu ne ya tsarga mata ta yi mutuwar tsaye cikin sanyin jiki ta waiwayo. Karaf idanunta suka sauka a kan Fulani Umaima da ta ha e girar sama da ta asa. _Ummou Aslam Bint Adam_ 07062062624. *SHU'UMAR MASARAUTA*