Sashe 77
Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dumm Sarki Abdul'aziz ya ji irjinsa ya buba, tamkar an buga masa guduma. Kunyar Sarki Sulaimanu ta lullu e shi. "Mun riga da mun zartar da hukunci Galadima, sanin kanka ne ba ma yin magana biyu." Muhsin ya ago a zabure ya dubi Mahaifinsa. "To a yanzu ba sai gobe ba za ka fara! Magana biyu ba, yau in nan za ka fara tun da yaro ya ce ba ya so, kai ma kuma na ga ba auren dole nan aka yi maka..." "Galadima a bamu guri!" Sarki Abdul'aziz ya sake katse shi a fusace. "Ka yi mini afuwa Mai martaba idan kalamaina za su sosa maka rai, ni ne dai mahaifin yarinyar nan kuma ni na tako har nan na nemi arzi in ha a wannan ala ar. Kuma a yanzu ina mai neman alfarmar Sarki Abdul'aziz da a bar yaron nan ya auri wacce yake so, ita kuma 'yar wurina ina nema mata auren Kamalu idan hakan ba zai zama da matsala ba." Sarki Sulaiman ya furta yana zuba maganansa a wurin Sarki Abdul'aziz. A razane Kamalu ya dago jin furucin Sarki Sulaimanu. at! Shi kenan, an gama magana yaro ya auri son ransa dama ai matar mutum kabarinsa." Galadima ya furta. A fusace Sarki Abdul'aziz ya ce. "Ba za mu ruguje maganar da muka gina a baya ba..." "Idan har ina da alfarma a wurinka ka yi yadda muka bu ata Sarki Abdul'aziz." Sarki Sulaiman ya katse shi. Rai a ace Sarki Abdul'aziz ya ce, "Ka sanar da iyayen yarinyar da kake so su turo magabatansu wurin Galadima ya aiwatar da duk abin da ya dace." Daga Kalamu har Jawahir kusan mutuwar zaune suka yi kowa da abin da yake wassafawa a zuciyarsa, a angare aya tsoron Sarki Abdul'aziz ya mamaye su don tun ranar da asirin Fulani Umaima ya tonu ba su ara ganin acin ransa haka ba. "Ni babu wacce nake so sai Jawahir." Rass! Gaban Jawahir ya fa i, jikinta ya auki karkarwa tamkar mazari. Sarki Abdul'aziz ya ura masa idanu sannan ya saki murmushi irin nasu na manya. "Kai Muhsin me kake nufi? Kana nufin duk wannan ha ilon da na yi ya tashi a banza? Na auka za ka ce a ha a ku da 'yar wurina Ummi?" A wannan karon ba Sarki Abdul'aziz ba har Sarki Sulaiman sai da ya saki murmushi, don gaba aya sun fahimci inda Galadima ya dosa. "Ni gaskiya Ummi ba ma tsarar aurena ba ce, Jawahir nake so." Muhsin ya furta har lokacin idanunsa a kan Jawahir da ta sunkuyar da kanta asa. "Jawahir 'yarmu ce sai mun ji ta bakinta tukunna saboda ita ma ba za mu yi mata auren dole ba." Dam! irjin Muhsin ya buga, nan take hankalinsa ya tashi don ya san ko ka an Jawahir ba ta aunarsa. "Kamalu ka ji hukuncin da muka yanke a kanka?" "Eh na ji ranka shi da e, Allah ya sa haka ne ya fi zama alheri." Kamalu ya yi maganar murya a sanyaye don wannan maganar ba aramin aga hankalinsa ta yi ba, don dai ba ya san ya watsa wa mahaifinsa asa a ido ne kawai ya amince. "Za ku iya ba mu wuri muna bu atar tattaunawa da Sarki Sulaimanu, a sanar da Baffajo muna son ganinsa bayan sallar magriba." Tun Sarki Abdul'aziz bai gama magana ba Muhsin ya fice fuuu, da ma shi Galadima tun da ya ji sun raba hanya da Muhsin ya karka e rigarsa ya yi gaba yana masifa da tsine-tsine. Kamalu da Jawahir kamar wa anda aka zarewa laka a jika suka russuna suka yi godiya suka fice, har Jawahir ta fita Sarki Sulaiman yana bin ta da kallo. Kamalu sauri ya fara yi tamkar zai ta shi sama ya wuce sashensa, yana shiga Bayi suka fara yi masa barka da shigowa ko kallonsu bai yi ba don yadda kansa yake sara masa tamkar zai tsage masa gida biyu. Damuwa auke a fuskar Inna wuro ta shiga akin Kamalu don ta ga lokacin da ya shiga fuska babu walwala, sallama ta yi masa da yar ya iya amsawa yana ganinta ya tashi zaune. A gefensa ta zauna ta zuba masa idanu, a hankali ya fara motsa baki. "Inna Mai martaba ne!" Rass gabanta ya fa i amma sai ta dake ta furta, "Me yake faruwa?" "Wai aure zai yi mini, amma Inna kada ki gaya wa Baffajo don na ji ya ce zai same shi ya yi masa maganar na san kuma a kanta za su tattauna." Murmushi ne ya bayyana a fuskar Inna wuro. "Kamalu don za a yi maka aure ne ka shiga damuwa? Ba ka san shi ne mutumcinka ba, kai don Allah bari na wuce wallahi har ka tsinkar mini da zuciya na auka wani abu ne. Kai Allah na gode maka Allah ka sa zan ga auren Kamaluna" Inna wuro ta yi maganar ta na ficewa daga akin cikin tsananin farinciki. Jawahir kai tsaye sashensu ta nufa zuciya babu da i, can cikin aki ta shige a lokacin Mai gado na akin Abubakar tana koya masa yadda ake tafiya don lokacin ya fara tsaiwa har yana iya mi ewa tsaye ya tsaya yam da afafuwansa, sai dai har lokacin kallo aya za ka yi masa ka fahimci ba shi da cikakkiyar lafiya. Jigum ta yi tana nazari don ta san ko karen hauka ne ya cije ta ba za ta ta a furta wa Sarki Abdul'aziz ba ta aunar ansa ba. Kamar wacce aka tsikara da sauri ta mi e ta auko littafin labarin Hidaya, kamar marar gaskiya haka ta ra e daga bayan ofa sannan ta bu o shi ta ci gaba da karantawa. Da mamaki Sarki Hafiz ya dube ni ya dubi wurin da nake kallo ya girgiza mini kai. "Idan har muka ce miki mun ga wata hallita a wurin can to mun yi arya. Babu wanda muke gani, idan kuma ke wayar idonki na gane miki sai dai idan fatalwarsa ce." "Mece ce Fatalwa?" Na wurgawa Sarki Hafiz tambaya. "Fatalwa wata hallita ce da take wakiltar mamaci take tsoratar da mutane ta cikin siffar mamaci, wata kuma ta ci gaba da gudanar da aikin alheri. Ke wata ma har fansa take dawowa ta auka. A ta aice dai ruhin mutum bayan ya mutu ne yake tashi ya dinga bin wa anda suka san shi a baya yana tsorata su wasu kuma ba sa tsoratarwa." Jinjina kaina na yi don maganar na ji ta yi mini nauyi aka. "Kuma wannan harsashen gaske ne wanda ya mutu yana fatalwa? Ko kuma dai kawai camfi ne?" Na sake wurga masa tambaya. "Ni dai da idanuna ban ta a ganin fatalwa ba, na dai ji ana fa in haka tun iyaye da kakanni. Amma gudun shakku, za ki iya tambayarsa domin muma mu ji daga gare shi." Tun Sarki Hafiz bai arasa kalamansa magana ba na hangi mahaifina ya tunkaro ni, sai da ya araso gabana ya furta. "Tabbas a kalaman Sarki Hafiz babu arya gaba aya ba sa ganina amma yanzu zan bu e musu idanu." Rufe bakinsa na ga su Fulani Hawwa kulu sun an ja da baya a tsorace. "Kada ku tsorota ha a ni ba mai cutarwa ba ne " Ya furta musu sannan ya sake har e hannuwansa a irji. "Ban so na bayyana ba amma ya zame mini wajibi tun da a yanzu kin haye karagarki, ni ba mahaifinki ba ne. Ni aminin mahaifinki ne wanda ya yi rainonki tare da mahaifinki. Na za i na ci gaba da zuwar miki a siffar mahaifinki ne domin na orar da al awarin aminina. Kuma lokaci ya yi da zan mallaka miki takobinki, takobin da burin mutane da dama suke mafarkin mallakarsa. Akwai wata yarinya da za ta zo cikin zamani mai tsawo, matu ar ta samu sukunin mallakar wannan takobin sai ta gagarewa duk wani hatsabibi da matsafi a nan duniya. Ita kanta yarinyar maha i ce, maha in duk wani silar gawurta da shahara a fa in duniya. Wa annan maha an ba za su ta a tasiri ba har sa sun mallaki wani kundin littafi da zan mallaka miki, kundin da nake fatan za ki zayyane duk labarin rayuwarki tun daga farko har arshe." Murmushi na sakar masa cikin girmamawa na furta. "Tabbas ka kasance amini na gari, ire-irenku sun yi aranci a duniya domin amana ta yi rauni. Amma wani hanzari ba gudu ba, a kwanaki na ji wani matashi yana ce mini ya samu 'yanci a lokacin da nake rufe, shin me hakan yake nufi?" "Yana nufin ya ku uta daga aurin da Sarauniya wato ssrauniyar da ta kasance daga zuri'ar Sarki Hafiz, ita ta sa aka yi masa aurin, Boka Tanko ne ya yi mata aikin a wa ansu shekaru da suka wuce." Aminin mahaifina da ke auke da siffar mahaifina ya furta mini. Mun jima muna tattauna wa ansu muhimman maganganu kafin daga bisa, ya auko wannan littafin da na juye tarihin rayuwata a ciki ya dam a mini. Ya ha a mini da takobin da ya al awarta mini. Daga arshe kuma ya auke ni muka yi tafiya mai nisa sannan ya kai ni bakin wani shuri ya ce na zura takobin da hannuna tare da yankar gefen hannuna na tsartar da jinina a kai, bayan na aiwatar na ga yana kallona. "Ina fatan yadda kika zura takobin nam, wacce za ta tono shi ta kasance tana daga cikin tsatsonki ce." Sam ban fahimci abin da yake nufi ba, daga haka muka baro wurin muka koma cikin masarautarmu. Tun daga wannan ranar sarautar masarautarmu ta dawo hannuna, na ci gaba da kulawa da angaren Bayi hatta wahalar da suke sha a baya sun samu afuwarta. Ban bar Sarki Hafiz haka ba har sai da na ba shi sarautar Wazirin masarauta, tun Fulani Hawwa kulu na nuna yashu da hassadarta a kaina har ta zubar da makamanta. Tafiya ta mi a sosai har soyayya mai arfi ta shiga tsakanina da Yarima an Sarki Hafiz, kuma hakan ba aramin da i ya yi masa ba. Ba a auki lokaci mai tsayi ba aka aura aurenmu muka ci gaba da rayuwa cikin farinciki a farkon auranmu. Jawahir ta ago kanta tana sauke ajiyar