Sashe 83
Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
shigarsu cikin garin su Sarki Abdul'aziz suka sha jinin jikinsu kallo aya za ka yi musu ka fahimci a an tsorace suke. "Amma me ye fa'idar yin hakan da ka yi Sarki Sulaimanu?" Sarki Abdul'aziz ya tambaya. "Saboda sun gama tsaface garinsu, tun tasowa ta har zuwa yanzu ban ta a jin labarin garin da ya yi shuhura a kan aikin tsafi da sihiri tamkar wannan ba. Yin hakan ne zai ba ku damar shi ga cikin garin nan hankali kwance, idan ban yi haka ba akwai matsaltsalun da za su iya biyo baya." Jinjina kai Sarki Abdul'aziz yana mamakin arfin tsafi da sihirin al'ummar Rumzu. Sarki Sulaiman ya sha mamaki da ya ga garin a yaye tamkar babu mutane don sai tsirari daga cikinsu, kuma duk wanda ya gansu haka zai bi su da kallo har sai sun ace wa ganinsu sakamkon bambamcin shigar da suke da ita. Tun daga nesa Jawahir ta hango Keken dokin Sarki Abdul'aziz, wani irin farinciki ya lulli e ta ta zabure za ta tafi da gudu, Fargi ta dam e hannunta da arfi. Nan take idanun Jawahur ya ciko da walla, yadda suka hango cincirindon mutane a hanyar kogon dutsen Shugaba ne ya ja hankalin Sarki Sulaimanu, don da har ya yi niyyar fara zuwa gidansu Fargi domin su an huta idan ya so sai Sarki Abdul'aziz ya gudanar da abin da yake tafe da shi, tun da har kawo lokacin bai san dalilin yin wannan tafiyar ba. Sannu a hankali komai ya shiga dawo masa dangane da ala ar da ke tsakaninsa da Fargi a lokacin baya. "Sadaukina yanzu fa watarana sai mu zo garin nan mu da 'ya'yanmu idan ka mayar da ni Masarautarku ko?" Kalama Fargi na baya suka shiga dawo masa a lokacin da ba su jima da yin aure ba. Ganin yanayin shigarsu ya sa tun da suka tunkari kogon dutsen mutanen da ke wurin suka shiga darewa suna ba su hanya, Tun da Mai gado ta hango Jawahir ta tafi da gudu cikin kuka ta rungume ta ita ma Jawahir ta saka kukan farinciki, da farko ya yi tsammanin idanunsa gizo suke yi masa amma da ya arasa gabanta a nan ya tabbatar da wayar idonsa ba yaudararsa take yi ba. Jikinsa ne ya auki karkarwa kamar mazari irjinsa ya shiga bugu da arfi zuciyarsa tamkar za ta hudo irjinsa, da hannu ya shiga nuna ta bakinsa na rawa ya furta. "Far... Fargi ke ce wayar idona ke gane mini?" Idanunta suka ciko walla tsantsar tausayinsa ya mamaye ta, ganin haka ya raunata zuciyar Dattijo Maharaz. Jikinsa shi ma ba aramin sanyi ya yi ba yana fargabar kalaman da za su fito daga bakin Fargi don ya san ba zai ta a yi wa Sarki Sulaimanu da i ba, dangane da tsammanin da yake yi a kan Fargi ce a gabansa. Da ido sauran mutane suka ci gaba da bin su da kallo, Sarki Sulaimanu ya waigo wurin Sarki Abdul'aziz cikin farinciki ya ce. "Ikon Allah ikon gaske, ashe rabon mu gana da Fargi ne ya sa kuka kawo mini wannan gayyatar Sarki Abdul'aziz." Dattijo Maharaz ya yi murmushi sannan ya nuna Jawahir ya furta. "Wannan ita ce silar zuwanmu wurinta, shin har yanzu ba ka gane wace ce ita ba Sarki Sulaimanu?" urr ya yi Jawahir yana kallonta yana son furta abin da yake cikin zuciyarsa amma tsoron kada ya canka ba daidai ba ya dakatar da shi. "Tun ranr da na fara ha uwa da ita Fargi nake gani a wayar idon, kuma jikina yana ba ni akwai wata muhimmiyar ala ar da ke tsakaninsu." Sarki Sulaimanu ya furta cike da shau "Wannan yarinyar 'yarka ce, jininka ce ta cikinka." Saukar kalaman Dattijo Maharaz suka yi daidai da jin dum! Da Mai gado ta yi tsakar kanta, Sarki Abdul'aziz ya zaro ido cikin tsananin mamaki. "Duk rintsi kada ku furta wannan yarinya ba jininku ba ce, don na san dangina da bibiya ko bayan wasu shekaru na tabbata za su iya banka o labulen sirrin da na binne." Furucin Mahaifiyar Jawahir na baya ya sake dawo wa Mai gado, ta ji wani sabon tashin hankali ya tsarga mata. "Kana nufin wannan 'yar Fargi ce?" Sarki Sulaiman ya tambaya kai tsaye. Dattijo Maharaz ya ba shi amsa. 'Tabbas Biri ya yi kama da mutum, wallahi tun ranar da na fara ganinta a Masarautar Huddam na sha jinin jikina." Sarki Sulaimanu ya arasa maganar yana rungume Jawahir a jikinsa. "Ranka shi da e idan Jawahir 'yarsa ce mene ne makomata a wurin Jawahir? A gafarce ni idan da kuskure a kalaman da zan fa a, amma sam wannan ba shi ne ainihin mahaifinta ba. Mahaifin Jawahir yana gida ba shi da lafiya, ni nan ni ce mahaifiyarta ni na auki cikinta har zuwa haihuwa." A wannan lokacin Sarki Abdul'aziz ya an shiga ru ani, tabbas a tarihin da ya ji Jawahir na daga cikin zuri'ar Rumzu, kuma a iya saninsa Malam Umaru da Mai gado ne iyayenta. "Me yake shirin faruwa?" Ya furta a fili cikin tsananin mamaki. "Wallahi-wallahi Fargi matata ce ta sunnah, kuma a shekarun baya akwai cikina a jikinta wanda ba na ko tantama wannan 'yata ce. Don Allah Fargi ki sanar da su gaskiya..." "Ka gafarce ni Sarki Sulaimanu bisa abin da zai fito daga bakina." Ta furta tana an sunkuyar da kai asa, jikinsa ne ya auki karkawa irjinsa ya buga tsoron abin da za ta fa a ya mamaye shi. Wannan shi ne ga oshi ga kwanan yunwa, fargabarsa ba ta wuce kada ya ga samu ya ga rashi ba don ko tantama ba ya yi wannan 'yar cikinsa. "A zahiri na tabbata kowa kallona yake a matsayin Fargi amma ni ba Fargi ba ce." A zabure Sarki Sulaimanu da Mahaifin Fargi suke dube ta jin kalaman da ta furta. "Fargi ta mutu bayan haihuwar 'yarta Jawahir yau kimanin shekara goma sha Shida kenan, na kasance ina amfani da surarta bisa yarjejeniyar da suka ulla tsakaninta da abar bauta tun a wani dare da ta ta a kai wa abar bauta kokenta. Sunana na ainihi Zumjuttu na kasance aya daga cikin jinsin aljanun da ke aukar surar Mammaci suna gudanar da wasu al'amuran na shi na yau da kullum, kafin Fargi ta mutu ta yi wa abar bauta tukwicin da ita kuma ta dam a mini wannan ragamar a hannuna, domin na kular mata da duk shige da ficen halin da Jawahir take ciki, har zuwa lokacin da za ta yi tozali da mahaifinta. Kuma koda wani mugun abin ake son na aiwatar da zarar an yi mini yanka an zubar da jini domin na dinga razanarwa ina firgitarwa, an riga da an gama biya kuma ba ya juya wa wannan aikin baya, wanda dalilin haka ne za ku ji ana ce wa fatalwar mutum tana tsoratar da mutane. Daga arshe dai na sauke wannan nauyin da kula da Jawahir, sai kuma Abar bauta ta ora mini wani nauyin na mallakawa Jawahir hatsabibin littafin da Hidaya ta ba da labarinta a ciki, silar haka na dinga zuwar mata a fili wani lokacin kuma a cikin mafarkinta. Na ci gaba da kai kawo a cikin rayuwarta har zuwa lokacin Jawahir ta mallaki wannan takobin kamar yadda kuke gani." Aljanar da ke magana da surar Fargi ta arasa maganar tana ago hannun Jawahir . A razane Dattijo Maharaz ya ago yana duban Zumjuttu rai a matu ace. "Amma me ya sa sai a wannan lokacin za ku ci amanar abin da ta dam a muku, me ya sa ba ki fayyace ainihin abin da ya sa kike bibiyarta ba?" Dattijo Maharaz ya yi maganar rai a ace. "Saboda a daidai wannan ga ar muka fi bu atarta, kana tunanin taurarin abar bauta za su sauka a kanta ba tare da wani dalili ba? Idan ba ka sani ba ka sani wa annan taurarin sun sauka a kanta tun tana cikin mahaifiyarta, ka ga kuwa ai kai ma ka san banza ba ta kai zomo kasuwa." "Lallai kuwa akwai sauran rina a kaba." Dattijo Maharaz ya furta jiki a sanyaye. Mai gado ta rushe da matsanancin kuka don ba ta ta a tsammanin wannan rana za ta zo a gare su ba, ganin Dattijo Maharaz da aljanar da ke auke da surar Fargi sun fayyace komai dangane da Jawahir ya sa ta share hawayenta ta fara gaya musu ala ar da ke tsakaninta da ita, tun daga lokacin da suka tsinci mahaifiyarta a daji tana na uda har zuwa mutuwarta da rainon Jawahir har zuwa girmanta. Shugaba da ke dur ushe a asa ya fara lalube da hannunsa sannan ya furta. "Hakika kin yaudare ni Zumjuttu, ashe ke kura ce lulli e da fatar akuya ban sani ba? Kin ci amanata na ba ki yarda ashe ke za ki zama silar dur ushewata, a tunanina da guntun binciken da na gudanar a halwar tsafina kullin Fargi nake gani. Don haka kacokam na mayar da hankalina wurin ganin arfi da yaji sai na dakushe ta, ba zan fasa fa a miki ba ko a haka kika bar ni kin yi nasara a kaina." Haushin Shugaba ya mamaye Sarki Sulaimanu, sai da ya ha iyi yawu mai aci sannan ya mi a hannu zai ri o Jawahiru da sauri Zumjuttu ta janye Jawahir. Dattijo Maharaz ya na e hannuwa a irji yana kallon abin da Zumjuttu take yun urin aiwatarwa. "A baya ku kuke da iko akan Jawahir amma wannan lokacin sai yadda abar bauta ta yi da ita, matsayinta na yanzu ya sha bambam da na baya. Idan kuna tantama za ku iya sarrafa ta ku gani." Ba Mai gado da Sarki Sulaimanu ba hatta Dattijo Maharaz sai da ya tsora ta da jin kalamanta, don ya san ba ananan hatsabibai ba ne. " "Amma me ya sa kuka son cutar da yarinya arama, wacce ba ta san duk abin fa yake faruwa ba." Mahaifin Fargi ya yi maganar yana hawaye, mutanen wurin suka yi tsit kowa yana mamakin abin da yake faruwa. "Saboda Mahaifiyarta ta sadaukar mana da ruhinta da surarta domin kula da abin cikinta, bari na fayyace muku abin da ba ku sani ba hatta gawar mahaifiyarta sai da ta zama mallakinmu