← Book details Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 89

Sashe 18

Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga aukan tsattsauran mataki don haka a kiyaye. *Masu orafe- orafe ta pc da groups zan rage 100 daga yau zuwa ranar da zan gama free pages. Free pages za su are a page a 10 daga yanzu zuwa ranar duk mai son karanta littafin za ta turo 400* SHAFI NA TARA Ayarin dakarun masarautar da ke tafe da su Baffajo tafe suke cikin gajiya sakamakon doguwar tafiyar da suka yi, a farfajiyar wata bishiya suka yada zango suna hutawa sai bayan sun huta sannan suka ci gaba da tafiya, cikin zuciyarsu kowa da abin da yake ayyanawa. Ganin magriba ta fara dosowa ya sa suka yanke shawarar kwana a cikin dajin washegari da asuba sai su ora daga inda suke tsaya. auyen Gangare Ganin yanayin da Umaru ya koma gida da shi ya sa Mai gado shan jinin jikinta. "Mai gida ya kuka yi da Mai gari na ganka duk a sanyaye." asa ya yi da murya ya furta. "Ina yarinyar nan take? Zan kai ta gidan Mai gari" Kallon rashin yarda ta bi shi da shi ta sake gyara goyon Jawahir da ke bayanta. "Me za ta yi a gidan." Kamar zai yi kuka Umaru ya ce, "Malam Malmo Mai gado ban san ya za mu yi ba, sun bu aci na mallaka wa Mai gari ita." Rass! Ta ji gabanta ya fa i, sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta yi asa da murya. "Ba zan iya rabuwa da Jawahir ba Mai gida, na san Malam Malmo sarai ba zai wuce tsubace-tsubbace zai yi da ita ba." Umaru ya waiga kamar wanda ake kallo duk a tsorace ya ce. "Ya zamu yi yanzu? Mene ne mafita?" Masarautar Huddam Wuni guda haka Fulani Umaima ta yi shi cikin rashin warin jiki, ba ta san dalili ba amma haka kawai za ta ji gabanta na fa uwa. Har ta so dannewa ta ji zuciyarta na azalzala ba za ta iya jure rashin zuwa wurin Bamaguje ba. Tsufansa ya sake fitowa sosai don jiki da hannuwansa har karkarwa suke yi. "Ta zo duniya da arfin iko, shi kuma yana gab da dawowa gidansu na gado." Bamaguje ya furta bayan ya gama sauraron orafin Fulani Umaima. Ta ago a hargitse bakinta na rawa, irjinta na dakan lugude. "Su waye? Kuma daga ina suke." "Garaje ga dami, da ina da ke gaggawa Umaima. Na auka za ki tambayi ala ar shi da masarauta da ita kanta yarinyar." Ajiyar zuciya ta sauke. "Tamkar tagwaye haka suka kasance tsakaninta da Hidaya, sai dai waccan ruwan sanyi ce salam a kan wannan. Ban san a wanne muhalli zan tirke ta ba, abu aya na sani ita ta kasance daga cikin wata irin zuri'a masu matu ar hatsarin gaske. Na ga takobi a cikin jininta sannan wuta na gewaye sashenta, takaicina aya Mahaifiyarta ta riga da ta binne duk wani al'amari da sirrin da ke unshe a cikin rayuwarta. Daga ni har sauran matsafan duniya duk wani bincike da za mu yi ba za mu tantance takamaiman ainihin tushenta ba. Sai dai kuskure guda mahaifiyarta ta tafka wanda da shi ka ai za mu iya cin galaba a kan wannan yarinyar." Cike da zumu i Fulani Umaima ta furta. "Mene ne shi? Duk wuya duk tsaninsa zan nemo shi..." "Bincike ya bayyana mini tana da matu ar tasiri a rayuwarsa. Ina nufin jaririn da kika sa Maimuna ta fitar da shi shekara goma sha aya baya, shi yake gab da shigowa gidan sarautarku. Sai dai kuma ita da shi za su kasance tamkar wuta da ruwa a fannin gaba, kowannensu ba zai aunaci an'uwansa ba. Shigarsa tamkar dasa nakiyar da ke tashin zamani da al aryarki ne, ba tun yau ba; na gaya miki shi ba kamar an uwansa ba ne. Ruhinsa auke yake da zaratan dakarun da ke sarrafa zuciya da tunaninsa, tun ranar haihuwarsa na fahimci zanen addararsa ya wanzu dalilin da ya sa na baki shawarar matse kunamar nan a cikin bakinsa, ashe tagwaye ne halwar tsafina ya gagara nuna mini. Tun yana jariri ya sauka a fadar Sarkin fararen aljanun doron asa, da ke tsakiyar dajin Wuruju a daidai wurin da Baiwa Maimuna ta dire shi. Sun na a masa kambun da babu mai iya sauke shi sai mutum aya wato wannan yarinyar." Bamaguje ya arasa maganar yana haska wa Fulani Umaima inuwar wata yarinyar. Ta tsinci muryarsa ya ci gaba da fa "Mu koma maganarmu ta baya na kuskuren da mahaifiyar Fargi ta tafka. Ta bar tauraron 'yarta a sake wanda duk wani matsafi kallo aya ko bincike aya idan ya yi a kanta zai fahimci muhimmancinta gare sa. Duk wanda ya mallaki ruhinta shi zai kasance mafi shahara a fa in yankin nan a angaren gawurtar tsafi da sihiri, runduna ce guda a tare da ita domin mahaifiyarta kafin ta mutu ta riga da ta juye mata nata jinin a jikinta." "Mene ne mafita, don ta ni gaba aya a mutu har liman a rasa mai jan sallah." Cewar Fulani Umaima da zuciyarta ta gama ashewa. "A baya na fid da rai da samun wannan aukakar, amma idan kin yadda me zai hana mu jefi tsuntau biyu da dutse aya?" Mai Gado "Guduwa ita ce mafita, sai dai mu bar garin nan amma ka san muddin muna cikin auyen nan Malmo ba zai bar mu da sauran numfashi ba." Shiru ya yi yana tunanin shawarar da ta kawo, ganin ya tsaya yana nazari ya sa Mai gado ta fa aki ta aura kayansu a cikin ankwali ta fito. "Allah ya sani na auki aniyar kula da yarinyar nan, Malmo azzalumin mutum ne, na san halinsa sarai tun da ya allafa rai a kan yarinyar nan ko mun dam a musu ita sai sun hallaka mu don gudun tonuwar asirinsu." Mai gado ta fa a tana mi a wa Umaru ullin kayansu, sai da ya kar a sannan ya furta. "Na gode wa Allah ya sa kika fahimtar da ni da tuni na sa mun yi tsalle mun afka cikin rijiya gaba dubu. Yanzu dai babu sauran lokaci mu bi ta ofar baya." Cikin sauri Mai gado da Umaru suka hanka e katangar karan da ke gewaye da gidan, kamar masu shirin tashi sama haka suka dinga sauri suna kutsawa ta ciki bishiyu duk da a lokacin magriba ta kawo kai. Sai da suka yi tafiya mai nisan gaske sannan suka arasa wani aramin gari a lokacin dare ya tsala sosai babu haske sai na farin wata, a gajiye suka zube a gefen ganuwar garin suna sauke ajiyar zuciya. Cike da galabaita Jawahir ta fara mutsu-mutsu sai a lokacin suka shiga damuwar abin da za su sama mata ta sha. Gorar ruwa Mai gado ta kunto ta ba ta sannan suka yi jigum-jigum, har sun zauna da sunan hutawa Umaru ya furta. "Mai gado an ya wurin nan yana da kyau kuwa? Me zai hana mu arasa cikin garin nan mu nemi alfarma?" Mai gado ta yi murmushin takaici, "Duk in da za mu je matu ar za su fahimci ba na shayar da yarinyar nan dole za su harbo jirginmu, kuma su ora mana zargi da tambayoyi a kanmu. Abin da muke gudu kuma ya faru ka ga an i cin biri an ci dila." Umaru ya yi jum sannan ya furta. "Ina ganin mu arasa bakin kasuwa mu kwana asubar fari sai mu bar garin, mu ora daga inda muka tsaya." Ta gamsu da shawararsa don haka suka yi gaba suna tambayar kasuwar garin har Allah ya datar da su, suna gab da shiga kasuwa suka ga wata mai fura da nono suka siya nono sannan suka arasa. A bayan rumfunan kasuwar suka yada zango bayan sun take wa Jawahir cikinta da nono, babu jimawa baccin gajiya mai nauyi ya yi awon gaba da su. Sanyin asuba ne ya bige su suka farka don haka kamar marasa gaskiya suka sake nufar doguwar hanyar suka ci gaba da tafiya. Ba su yi tafiya mai nisa ba suka tsaya suka gabatar da sallah sannan suka ora daga inda suka tsaya. Sai da suka yi tafiya mai nisan gaske sannan suka tarad da wani ayarin mutane, yara, manya, maza da mata. Sai kuma Dogarawan da ke kai kawo a kansu, kallo aya Umaru ya yi musu ya fahimci bayi ne aka kama. Da yake suna an nesa da su da sauri Umaru ya ja hannun Mai gado ya furta, "Maza zo mu gudu idan Dogaran nan suka gan mu na tabbata kashinmu ya bushe don mun zama Bayi na har abada." Yana rufe baki suka juya da sauri. Cak! Suka tsaya cikin fa uwar gaba, Mai gado ta ri o hannun Umaru jiki na karkarwa. "Gidan uban wa za ku gudu?" Kalaman Sojan masarautar mai irar samudawa ya ratsa su, gaba ayansu aka rasa mai bakin magana. Ganin haka ya sa Dogarin tsula wa Umaru bulala a baya, cikin azaba ya hau susar baya yana fa in. "Tuba nake ranka shi da e ba guduwa za mu yi don Allah ku yi mana rai." Da hannu Dogarin ya nuna musu hanyar da sauran mutanen da ke zaune a asa suke, babu musu Mai gado da Umaru suka bi hanyar ba tare da sun furta komai ba. Tun da suka tunkari wurin mutanen wurin suka zuba musu na mujiya suna kallonsu. Bai san dalili ba haka kawai yake jin irjinsa na bugawa, zuciyarsa kamar za ta yi tsalle ta hudo irjinsa. Duk taku aya da Mai gado take yi tana kusanto shi ji yake kamar ana ana wa zuciyarsa ruwan dalma, da wata irin uda da wani surutai da ya gagare tantance harafi aya ballantana ya yi wa kalaman nasu hisabi. Da yake hannunwansa biyu a aure suke a jikin itace, kansa ya tura cikin afafuwansa yana runtse ido. Bai yi aune ba ya fara jin sautin kukanta a tsakar kansa, yana yun urin bu e idonsa kamar a mafarki ya ji an furta. "Ita daban ce don haka ta fito daga cikin wani irin ahali, tarayyarku alheri ce mai samar da taimakon juna a
Chapter 18 · 0% Book details