Sashe 10
Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
zafi ta yi fakare tana sauraronsu. Yaya Halima cike da damuwa ta jinjina kai. "Kin sanar da Mai martaba?" Girgiza mata kai kawai ta yi don ba ta son ta bu e baki har ta iya sanar da danginta zaman doya da manjar da ke tsakaninta da Takawa. Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta furta, "Ya zama wajibi na sanar da Yakumbo a nemar miki magani, domin wannan fitsarin ba na lafiya ba ne. Ni fa dama zuciyata da hankalina ba su ta a aminta da wannan kishiyar taki ba..." Da sauri Fulani Babba ta katse ta. "Yaya kada ki zargi Umaima domin ban ta a zarginta a kan wani mugun abu ba, zamana da ita babu wata matsala ni dai a yi mini magani amma Allah ya sani babu sa hannun Umaima a lalurata." Inuwar da Yaya Halima ta hango a wurin labule ya sa ta furta. "Waye a wurin nan?" Jikina na rawa Jakadiya ta fa akin tana fa in, "Allah ya taimaki Fulanin Takawa, uwar yariman gobe da yardar Allah. Dama ruwan wanka na kwashe na zo sanar da uwar gijiyata." Daga cikin akin Fulani Babba ta furta. "Sa onki ya isa Jakadiya." "Godiya nake zinariya fara mai farar aniya bangon talakawa da marasa gata, Allah ya raya mana yarima ya gaji karagar da babu kamarta a fa in nahiyar nan." Yaya Halima ta amsa tana bin Jakadiya ta kallon tuhuma. Sai da ta ga Jakadiya ta fita sannan ta furta. "Da alama wannan farar zuciya taki na iya kai wankin hula ya kai ki dare, jikina yana ba ni idon masarautar nan yana kanki." "Yaya Halima shi zato zunubi ne! Don haka..." Da sauri ta katse ta. "Dama ki ajiye zurfin cikinki kin amayar mini da abin da yake cikinki domin abokin kuka ba a oye masa mutuwa." Idanun Fulani Babba ya ciko da walla don ita ka ai ta san zafin da zuciyarta take yi mata, amma sanin Yaya Halima na daga cikin irin marasa ha uri ya sa ta danne damuwarta ta furta. "Babu wani abu da yake damuna Yaya Halima, idan ma akwai na fauwala wa Allah saboda saniyar da ba ta da jela Ubangiji ne ke kore mata uda." Yaya Halima ta ta e baki ta fice ba tare da tanka mata ba, Fulani Babba da ta yi shirin wanka tana kai idanunta kan jaririnta. A kullin ta kalle shi zuciyarta na wasu-wasi a kan ingancin lafiyarsa, sai dai babu yadda za ta yi tun da ba fada gare ta a wurin Takawa ba balle ta yi masa bayanin halin da jaririn yake ciki. Kamar za ta tashi sama haka Jakadiya ta yi sashen Fulani Umaima a lokacin Fulani na sha ar bacci ko sallar asuba ba ta yi ba duk da gari ya waye garau, da farko Bayin da ke kula da ita sun sanar da Jakadiya Fulani na bacci. Amma da yake bakinta cike yake fal da tsegumi a dole haka ta shiga tana ta ranga a sallama. Kamar a mafarki Fulani Umaima ta ji sallamar Jakadiya wanda hakan ne ya alamta mata akwai wani muhimmin abin da yake tafe da ita, tana daga kwance ta sa a yi wa Jakadiya iso har cikin turakarta. Jakadiya na shiga ta zube a asa, "Hutawarki lafiya tauraruwar Mai martaba uwar yariman gobe da yardar Ubangiji. A yi mini aikin gafara na tashi uwar gijiyata a farar safiya..." Da hannu Fulani Umaima ta katse ta, kamar ba za ta yi magana ba sannan ta ce. "Akwai magana a bakinki Jakadiya don na tabbata banza ba ta kai zomo kasuwa." Jakadiya ta yi mata jinjina da hannu. "Allah ya ara yawan rai wannan yarinyar da nake ganinta mai hankali ashe lumbu-lumbu ce wutar ayi?" "Jakadiya tafi kanki tsaye. Fulani Umaima ta fa a a gajarce. "Halima yayar waccan ragowar fitsarin, ita na ji tana shirin allo mana ruwa. Ni kuma na ce har gaban abada kwa armu ba za ta yi ruwa tsululu ba, sai dai a mutu har liman kowa ya rasa sallah..." Jakadiya ta kwashe duk maganganun da ta ji Fulani Babba suna yi ita da Yaya Halima. Murmushi Fulani Umaima ta saki. "Daga kallon da na ga tana bi na da shi ya sa na fahimci ruwa ba zai ta a tsami banza ba. Ta shi ki je Jakadiya idan hantsi ya fito ki dawo akwai kyautar samirar alkaki da nakiya, zan ha a miki da fallan zani da gorar ma i. Na rantse da Allah sai na tabbatar wa Halima ba a taka shuri kowanne iri a zauna lafiya." Jakadiya ta sake zubewa. "Godiya nake uwar akina, godiya nake zinariyar Mai martaba uwar duka mazauna asar Huddam da kewayenta. Allah ya bu i ido lafiya ya kawo mana Yarima cikin oshin lafiya." Fulani Umaima ba ta amsa ba, inkiya ta yi mata da ido. Ganin haka ya sa Jakadiya ta fice daga akin don ta san ba za ta amsa mata ba. Washegari ya kama suna jaririn Fulani Babba ya ci suna Abubukar Sadiq, haka kawai Sarki Abdul'aziz ya tsinci kansa cikin farin ciki duk ba ya iya nuna soyayyarsa game da yaron, ya so a gayyaci masu wasannin al'adar bahaushe amma wata irin fargaba yake ji da tsoron Fulani Umaima a zuciyarsa. Da ya yi wani yun uri sai ya ji kamar idan ya aikata bai kyauta wa Fulani Umaima ba. A haka aka ci taron suna sai dai hatta Bayin da ke cikin masarautar ranar sai ta zame musu daban sakamakon walwala da suka samu ta hanyar sauya abinci da sakewa. Fulani Umaima ta saki jiki sosai a ranar da kanta ta gayyaci 'yan wasan tauri aka gudanar da wasanni, tamkar babu wani mugun uduri a zuciyarta. Bayan suna da kwana biyu 'yan uwan Fulani Babba suka tattara kayansu suka koma masarautarsu, ko a ranar da za su tafi sai da Yaya Halima ta jaddada wa Fulani Babba suna komawa za a aiko mata da magungunan da suka da ce. Ita ma kuma Fulani Umaima a ranar da suka tafi a ranar ta dira wurin Bamaguje ta shimfi e masa bukatunta, kuma take ya zartar mata da su, ha e da jinjina mata bisa aikin Baiwa Maimuna da ta aiwatar ba tare da an samu matsala ba. Sai dai abu aya da ya sanar mata ne ya nemi hargitsa kwanyarta har ta koma gida ta gagara runtsawa tana tunanin makomar abin da zai biyo baya. *Masu ganin laifin Fulani Babba na rashin yin addu'a kada ku manta labarin an sanya ya faru a shekaru saba'in baya da suka wuce (1953) Kun ga a lokacin ilimin addini bai yawaita ba, ba kamar yanzu da ilimi ya zaman ruwan dare ba. A mafi yawan wancan lokacin, camfi da tsubbace-tsubbace sun fi arfi a kan yawaitar addu'a, babu wayewar kan da idan abu ya same ka kace bari ka du ufa ba dare ba rana ka kai wa Allah kukanka.* _Ummou Aslam Bint Adam_ 07062062624 *SHU'UMAR MASARAUTA*