← Book details Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 89

Sashe 42

Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da ina raye da ba na raye Allah ne yake kula da Abubakar amma duk ranar da asa ta rufe idona ban san yadda rayuwar Abubakar za ta kaya ba." Mai gado ta sake rushewa da matsanancin kuka sakamakon tuno ire-iren kalaman da Fulani babba take yawan furta mata a duk lokacin da suke zaune suna attaunawa. "Kai wai mene ne yake faruwa kuka cika mana gida da kuka kamar masu zaman makoki..." Kalaman Jakadiya suka katse sakamakon ganin Fulani babba a lullu e, babu wanda ya tanka mata don haka ta arasa bakin gadon ta yaye zanin da aka rufe ta, hannu ta kai saman irjinta a razane ta ja da baya. "Mai gado me yake faruwa?" "Babu Fulani babba, Jakadiya mun rasa Fulani wayyo Allahna!" Rass irjin Jakadiya ya buga, ta jingina da bango wata irin zufa na tsattsafo mata. Da sauri ta fice daga akin kai tsaye ta wuce sashen Fulani Umaima. "To Fulani Umaima shi kenan urun us! Ta faru da are an yi wa mai dami aya sata. Burinki ya cika Fulani ta bar miki duniyar sauran abin da ta bari sai ki ha a ki cinye." Jakadiya ta furta wa Fulani Umaima da ke har e a kan kujera. Wani sanyi ne ya ratsa zuciyarta shi kenan muradi da burinta zai ka ga ciki, amma a fili sai ta furta. "Jakadiya ya kamata ki iya zarge limzamin harshenki idan ba haka watarana za ki yi arin zancan da zai kai ki ga turnar danasani. Ko Fulani ta so ko kar taso idan lokacin tafiyarta ya yi sai ta je, Allah ya ji anta ya gafara sai ki sanarwa Takawa a yi a binne ta kin san jinkirin gawa yana kawo wamai cikin gida. Haka kawai su dinga firgita mu da tsakar dare, muna kasa fita fitsari." Kasa e Jakadiya ta yi tana sake jimanta tsantsar rashin imanin Fulani Umaima. "Wacce irin asasshiyar zuciya gare ki Umaima?" Fulani Umaima ta saki murmushi cike da izza, isa da asaita. Sai da ta zagaye Jakadiya ya kai sau biyar sannan ta furta. "Tambayar da a kullin nake wurga wa zuciyar tawa kenan amma har yau ta gagara nusar da ni al ibikarta, abu aya na sani dangane da kaina Jakadiya." Sai da ta koma kan kujerarta ta zauna, ta ora afa aya kan aya sannan ta ce. "Duk wani abu da nake so nake auna to zai kasance nawa ni ka ai har abada, ina da matsanancin kishi ba iya a kan mijina ba. Dalilin da ya sa nake kawar da duk wani abu da nake ganin zai zame mini shamaki a gabana, Jakadiya ba zan tsawaita miki ba amma ke kanki kin san Umaima ba kanwar lasa ba ce. Lumbu-lumbu ce wutar ayi idan kin so ki kira ni da suna cinnaka ban san na gida ba. Ki ci gaba da shiri Jakadiya kada ki fasa domin kwanciyar kura ba shi ke nuna yin nasara a kanta ba." Kallo aya za ka yi wa Jakadiya ka fahimci kwanciyar hankali ya yi aura daga jikinta, yayin da tashin hankali ya mamaye gangar jiki da tsokarta. Ganin idan ta ci gaba da tsaiwa tana iya zubewa asa saboda tashin hankali, ya sa ta fice daga akin Fulani Umaima kai tsaye ta wuce Sashen Sailuba. Take wani tunani ya fa o wa Fulani Umaima da sauri ta fice ta wuce sashen Mai martaba, a gaggauce ta fara bubbuga ofar cikin nuna tashin hankali. A tsammanin Takawa Mai gado ce ta sake dawowa don haka ya yi biris da ita. Kusan tun safe suka fara casar gero da sussuka, har kawo yamma abin da yake tsayar da su yin sallah ko cin abinci don haka Jawahir ta gaji li is sakamakon ta jima ba ta yi aiki mai yawa kamar na wannan ranar ba. A lokacin da suka fara arar gya a saman cikinta ne ta ji ya yi mata auuuu kamar wacce aka anawa dalma. A gigice ta kai hannu saman wurin da tambarin bishiyar yake wani irin zafi ta ji, har idon kunnenta ba gizo yake yi mata ba ji ta yi tamkar tambarin na fisgar hannunta. A sace ta fice daga wurin ba tare da kowa ya lura ba, can cikin dajin ta an nausa sai da ta waiga hagu da sannan ta aga rigarta. Jawur ta ga wurin ya yi zanen bishiyar ya ara fitowa ra au, wani irin tsoro ya kamata irjinta ya shiga bugawa da sauri. "A matsayina na mahaifiyarki ina mai alhinin sanar da ke daga yanzu a kowanne lokaci ofar unci da damuwarki na iya bu ewa, ni na hango miki abin da ba ki hango ba Jawahir amma tun da haka kika za a ga fili nan ga mai doki." A tsorace Jawahir ke kallon matar da ta ta a gani ta zo mata cikin mafarkinta, sai dai a yanzu iri- iri ta ganta cikin sura da ta ganta a cikin mafarki. Ja da baya ta fara yi tsorace kafin ta yi wani yun uri ta ga matar na yin baya-baya har gangar jikinta ya nutse a kikin murgujejiyar bishiyar kukar da ke gabanta ta ace mata at. Tsoro ne ya sake mamaye Jawahir da gudu ta falfala cikin tashin hankali ta nufi sashensu na Bayi. Uwar tuwo na ganinta ta fara wala mata kira amma ko waigenta ba ta yi ba, can saman gadon karan Maigado ta fa a ta janyo zanin gadon irjinta na bugawa jikinta na karkarwa ta lullu a. Nan take zazzabin ya lullu e mata jiki a angare aya kuma ra in tambarin cikinta ya haddasa mata rashin kuzari, da ta runtse ido matar take gani a lokacin da take nutsewa cikin jikin bishiyar, wannan ya sake aga mata hankali don ko a mafarki ba ta ta a ganin haka ba. "Ranka shi da e ka bu e mini yau mun yi babban rashi Fulani Umaima ce ke magana, wayyo Allah Fulani kaico rayuwar duniya zancan banza." Takawa ya ji kalamanta sama-sama, tasowa ya yi ya bu ofar da sauri Fulani Umaima ta fa a jikinsa ha e da fashewa da matsanancin kuka. A an rikice ya dube ta. "Me yake faruwa da Fulani ta shiga cikin firgici haka." "Wato ba ma ta Fulanin da ka ji na ambata kake ba kenan, ni dama ai haka nake so." Fulani Umaina ta yi maganar a zuciyarta. "Ranka shi da e Fulani ce babu, Fulani babba ta rasu dai rai ya yi halinsa. Mun rasa Fulani yanzu Jakadiya ke gaya mini mutuwarta." Cak Sarki Abdul'aziz ya yi wani abu na yi masa yaaaammm tun daga tafin afarsa har tsakiyar kansa, ture Fulani Umaima ya yi. "Fulani ba mu san lokacin da muka fara wasa da ku ba! Har rainin ya kai a zo a fa a mana wa annan maganganun?" Kalaman Sarki Abdul'aziz suka ratsa ta a lokacin da ya jingina da bango yana jin kansa ya yi masa nauyi kamar zai tarwatse. "Sarkina ka san tun da nake tare da kai ban ta a yi maka arya ba, yanzu aryar ma sai na rasa wa zan yi wa sai Fulani babba, dama ana yin arya da mutuwa Ranka shi da e?" Wani irin sanyi jikin Sarkin Abdul'aziz ya yi, kamar wanda aka zabura ya fita da sauri duk hanyar da ya bi sai dai Bayi su dinga zubewa asa suna kwasar gaisuwa amma ko kallonsu ba ya yi ballanta ya tanka musu. *Littafin ku i ne 500 idan kina bu ata za ki biya ta wannan Account in Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.* *Daga jiya zuwa yau na ga orafe- orafe ta pc da cikin group, wasu ma na ji sun ce sun daina karantawa sai sun tabbatar da mutuwar Fulani wasu kuma sun tafi hutu to dai duka a yi ha uri.* *Kamar yadda kuka sani kowanne bawa fa da kalar tashi addarar, rayuwa ma'auni ce akwai wanda idan ka dubi rayuwarsa za ka Ubangiji ya yalwata shi da dukiya, 'ya'ya, dangi da duk wani abin more rayuwa na farinciki kuma har arshen rayuwarsa, idan da wata matsala ma a ciki ba mai aga hankali ba ce sai ka ga kamar shi ya tsara wa rayuwarsa haka. Akwai kuma wanda za ka ga Allah ya jarabce shi da talauci, rashin lafiyar 'ya'ya jarabta kala-kala, rashin mahalli da sarausu. Wasu kuma ka ga Ubangiji yana ha a musu duka biyun.* *Salon labarin nan na daban ne don na karanta littafai ba aya ba ba biyu ba da zan ga an zalinci kishiya ko dai wani daga arshe shi wanda aka zalinta ya ga arshen wancen, wannan kusan ya zama gama-gari a cikin labarai ko ni na yi haka a ciki AN YA BAIWA CE. Alhalin a cikin duniyar nan akwai wa anda za a cuta arshe ma ba su san wanda ya cuce su in ba har su mutu, sai dai su wa anda suka yi abin daga arshe su tona asirin kansu ko kuma sakayya ta bayyana arara, kai wani lokacin ma sai shari'a a wurin Ubangiji. Akwai mahaukaciyar da na sani asiri aka mata ta haukace arshe mota ce ta bige ta ta mutu a cikin haukan, sai 'ya'yanta aka kwashe, ita kenan sai a ce don me ba ta san wanda ya mata asiri ba kuma ba ta ga arshen mai yin asirin ba? Ina san na nusar da cewa ita duniya ba komai kake nema ka samu, don akwai wacce na sani ta shafe shekaru ba ta ta a haihuwa ba ta fuskanci alubale daga dangin miji har shi mijin kansa, kwatsam ta samu ciki ba aramin buri ta ci a kan cikin ba arshe a wurin na uda ta mutu ita sai a ce don me ba ta ga abin da ta haifa ba? Wallahi Reality akwai wata ma ociyarmu da na sani, mijin ba shi da hali sosai ita matar ta yi wankau, sirfau, har gidajen masu hali take bi tana musu wanki daga baya Allah ya fara yalwata mijin a wannan ga ar ita kuma Allah ya mata rasuwa, arshe saboda iyali mijin aure ya yi kuma ya zama hamsha in mai ku i ku i sai da
Chapter 42 · 0% Book details