Sashe 87
Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lokacin da Fargi ta isa wurin abar bauta zubewa ta yi bisa gwiwoyinta ta rushe da matsanancin kuka, sai da ta yi mai isarta sannan ta yi sujjada a gaban bishiyar ta furta. "A kowanne lokaci Shugaba zai iya aukan mummunan mataki a kaina, Abar bauta da ke na dogara ke ce madogarata." "Zan taimaka miki da dukkan taimakon da muka saba yi miki, ki tashi ki koma gida a daren yau ki dawo gare mu domin akwai bu atun mutane da dama a gabanmu idan muka gama da su za mu ji da na ki." Abar bauta ta furta mata cikin kulawa, sai a lokacin Fargi ta ji warin gwiwa ta yun ura za ta tafi, sai dai mi ewar da za ta yi ta ji mararta ta karta mata. A hankali ta fara takawa kafin ta arasa gidansu ta lura da inkiyar da Sarku Sulaimanu yake yi mata idan ya kawo mata ziyara, sai da ta an jingina da bishiyar Tsamiyar da ke gefenta sannan ta furta alasiman tsafinta ta ace daga wurin, a inda suka saba ha uwa ta same shi yana ganinta ya arasa sa sauri ya ri o hannunta. "Uwar Biyu barka da fitowa." Daidaita nutsuwarta ta yi don kada ya fahimci damuwarta. "Yau ka yi mini kyau Sarkina?" Fargi ta furta tana zuba masa idanu. "Ni kuma kin rame mini yau Fargi me yake damunki?" "Ciwon mara nake sama-sama." Ta furta tana an yamutsa fuska. Da sauri ya ce, 'To ko dai abin ya zo ne?" Rufe idanunta ta yi da sauri cikin jin kunya, ya ri e hanunta suka arasa wurin dokinsa. Tabarmar kabar da ke saman dokinsa ya auko ya shinfi a musu suka zauna suna ci gaba da hira, tun da Sarki Sulaimanu yake zuwa wurin Fargi bai ta a da ewa a wurinta kamar na wannan lokacin ba, don har sai da duhun magriba ya yi suna zaune a wurin. Sun yi hira sosai wata hirar ma ba sa dire ta Fargi take auko masa wata. Wata su yi a kan abin da za ta haifa wata kuma a kan yanayin rayuwa, har a game da iyayenta sai da ta sanar da shi don haka duka damuwar da take ciki ta yaye mata. A wannan ranar Sarki Sulaimanu har zai hau dokinsa ya tafi Fargi ta coge wuri aya a kan sai ya yi mata rakiya, wannan ita ce rana ta farko da Sarki Sulaimanu ya ta a bayyana a zahiri ya yi wa Fargi rakiya har zuwa ofar gidansu, duk nutanen da suka wuce sai sun bi su da kallo amma shakkun Fargi ya sa ba wanda ya tanka mata. A ofar gida ma sun jima suna hira har sai da Fargi ta gaji don kanta ta sallame shi sannan ya tafi da cewar zai dawo washegari ya sake ganin sau in jikin nata. Da kansa ya shigar mata da duk kayayyakin da taho mata da shi gefen bukkarta sannan ya tafi har sai da Fargi ta daina hangensa sannan ta koma cikin gida. Washegari asubar fari suka ji hayaniya da kace-nace a ofar gidansu kafin sun yi wani yun uri su ka ji an fara kai duka kan kararen da suka zagaye akunan bukkokinsu da shi. "A kashe ta sai an kashe ta tun da ta aikata babban kuskure wannan umarni ne daga wurin Shugaba." "Ba za mu saurarawa maci amanar zuri'armu ba." "A fito mana da Fargi domin ba za ta watsa wa Shugaba asa a ido ba." Ire-iren kalaman da suka dinga ji suna tashi kenan daga bakunan mutane, cikin firgici Mahaifiyar Fargi ta ri o hannunta ta bayan bukkarsu ta furta. "Maza ku gudu Fargi, ba na son Shugaba ya kashe mini ki, ace daga wurin nan Fargi tsafi da sihiri zai dafa miki." Ganin tashin hankalin da mahaifanta ke ciki ya sa ta fara zubar da wallah, ba ta son barinsu cikin tashin hankali don haka ta girgiza kanta tana fa "Ba zan iya barinku ba ban san halin da za ku shiga ba..." "Ki fita ki gudu na ce miki Fargi." Mahaifinta ya katse ta cikin araji. Duk yadda Fargi ta so sarrafa al' alamin tsafinta domin ta gudu sai ta kasa, don haka ta fa aki da sauri ta auki wani sabon ganye ta aure shi katamau a jikinta ta soka wata tsafaffiyar askarta a ugu da sauran tarkacanta, ta waiga tana aga wa mahaifanta hannu sannan ta sa a ta bayan bukkar ta fice, duk da tana jin ciwon baya da marar hakan bai hana ta yin gudu tun arfinta ba, sai da ta an yi nisa sannan mutanen garin suka rushe duk wata bukka da ke gidan a arinsu na ganin sun gano Fargi arfi da yaji, da suka fahimci ta gudu sai Shugaba ya ba su umarni da su rarrabu wuri-wuri ko za su samu nasarar kamo ta. Abu aya ya ba shi mamaki yadda ya gagara sarrafa tsafinsa domin ya gano wurin da take, ya san dai ya dakushe na ta tsafin amma bai san me ya hana na shi ya yi tasiri ba. Abin da Shugaba bai sani ba tun da Abar bauta ta lura yana da niyyar kashe ta, a ranar sai ta dakusar masa da tsafinsa. A galabaice ta fa i a wani aramin auye ta ebi ruwa ta sha saboda gudun da ta sha, tana nan zaune ta fara jin taku a hankali. Mi ewar da za ta yi ta yi arba da wa ansu matasa biyu daga cikin mutanen garinsu, da sauri suka araso wurinta aya daga ciki ya kai mata naushi a ciki. Azaba ta sa ta fa i gefe ta auki wani ganyen bishiya ta hura iskar bakinta ta wurga musu, ganyen na sauka a fuskarsu ta kama da wuta. Wani irin azababban ciwon mara ya da baya ne ya ha e mata, a daddafe ta iya matsawa daga cikin wannan auyen ta tsallake wani asurgumin dajin da ke gabanta, a lokacin ta da isa ta galabaita sosai don haka ta fa i a gefan wata bishiyar kuka, da fa uwarta babu jimawa ta fara jin motsin tafiyar mutane a tsorace ta ago don a tunaninta wasu daga cikin mutanen nata ne suka sake cim mata, amma ganin ba in fuska ya sa ta sake kwantar da kanta ciwo ya sake taso mata gadan-gadan, har zuwa lokacin da Mai gado ta arasa wurinta Malam Umaru ya juya musu baya ta haihu. Cikin anin lokaci mutuwar Malam Umaru ta kara e cikin masarautar Huddam, musammam ma Bayi ba aramin ka uwa suka yi da jin mutuwarsa ba, kuma har lokacin ba su daina mamakin dalilin kwanciyar Malam Umar jinya da atan Jawahir ba da in-da awa da suka ji abin da aka ce Malam Unaru ya fa a kafin Allah ya yi masa rasuwa. Da farko an so a sallace shi a ranar amma kasancewar Magriba ta kawo kai ya sa aka bada shawarar barin gawarsa zuwa wayewar gari, Kamalu , Baffajo da sauran mutanen da suke mutumci da Malam Umaru ne suka ce za ku kwana da shi, domin kowa yaba kyawun halinsa yake da kyakkyawar mu'amalarsa da mutane. Kunyar duniya ce ta mamaye Dela musamamn yadda ta ga mutane suke bin ta da kallon mamaki, wasu daga ciki har sun fara tofa albarkacin bakinsu yayin da wasu har kawo lokacin tsoranta bai gama barin zuciyarsu ba. "Baba me kake so na ce maka bayan ka riga da ka gama tona mini asiri? Duk wannan wula ancin da kuka yi mini bai isa ba..." A fusace Babban Malami ya yi kanta ya kai mata duka, Dattijo Maharaz ya an ru o hannunsa sanna ya furta. "Ka yi ha uri Babban Malami ai In shaa Allahu komai ya zo arshe. Idan za ta tuba sai a yale ta ta ci gaba da rayuwarta..." "Ba za ta ta a tuba ba Maharaz! Na san wace ce Dela 'ya ta ce fa. Ya zama wajibi a one ta kowa ma ya huta." Rufe bakin Babban Malami suka ci gaba da one Dela da ayoyin Ubangiji. ".Na daina na tuba don Allah kada ku hallaka ni." Dela ta furta a galabaice, babu wanda ya saurara mata daga cikinsu har sai da suka ga ta fa i gefe aya babu numfashi a jikinta. "Alhamdulillah!" Ita ce kalmar da suka furta gaba aya, jikin mutanen Rumzu ba aramin sanyi ya yi da ganin abin da ya faru ba. Wa anda suke gaban Babban Malami lokaci aya suka zube a gabansa ganin haka ya sa sauran da ke bayansu gaba aya suka tsugunna alamar sun sallama masa. "A shirye muke da mu bauta maka tun da har muka ga ka kawo arshen Abar bautar da muke bautawa tun iyaye da kakanni, tabbas mun gasgata ita ba abar bauta ba ce tun da har mun fahimci raununta." Tashin hankali ya bayyana arara a fuskar Babban Malami don haka cikin hanzari ya furta. "Ni ba Ubangiji ba ne kamar yadda Dela ba ta kasance Ubangiji ba, ni hallitar Allah ne kuma shi ne ya kawo arshenta saboda ayoyinSa ne muka karanta har muka hallaka ta. Ni da sauran wa annan bayin Allahn duka Shi muke bautawa, ku sani Dela ta yi wasa da hankalunku ne saboda wa ansu abubuwan almara da take aiwatar muku, shi ya sa har kuka ba ta matsayin da ba ta cancanta ba. Shi jinsin aljani ba kamar mutum ba ne, Allah ya huwace mana baiwar da za mu iya riki a duk wata hallita da muke so, kuma muna iya aiwatar da duk siddabarun da muke so a wurin da addini ha i da addu'o'i suka yi rauni. Don haka a yanzu ma ba ku makara ba, za ku iya kar ar wannan Addinin ku yi ri o da shi kuma ya zame muku makamin da za ku ya i duk wani hatsabibi ko hatsabiyar da ke doron asa duk makirci da arfin tsafinsa, domin ba su isa su ja da arfin ikon Allah ba. Yanzu idan kuka yi imani da ni watarana na mutu wa za ku ri a a matsayin abin bauta?" Babban Malami ya wurga musu tambaya, gaba aya suka yi shiru don jikinsu ba aramin sanyi ya yi ba ganin haka