Sashe 71
Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
a lokacin da bai za ta ba." Boka Shaddas ya furta cike da cin alwashi. Wa ansu tarkacan magunguna ya ebo ya fara watsawa jikinsa, ya shiga yin turarrika sannan ya zauna a gaban wutar tsafinsa yana tunanin hanyar da za bi don ya isa cikin Masarautar Huddam ya auko Jawahir in da Shugaba ya saka shi ko ya samu damar fanso Basiru da tasirin tsafin da ya dogara da shi. Sai da wa annan Dattijan sarakunan suka ci suka sha suka huta sannan Sarki Abdul'aziz ya gabatar musu da Kamalu da matsayinsa a wurinsu. Mahaifin Fulani babba har sai da ya zubar da walla sannan ya rungume Kamalu yana jin aunarsa a ransa, aya bayan aya haka Mai martaba da manyan yayyan Fulani babba suka dinga jan Kamalu har su Khadija suka rungume shi suna kuka, tare ta labarta masa irin halin uncin da mahaifiyarsu ta shiga a lokacin da tana raye, musamman Khadija da ita ta fi sanin sirrin damuwar da ke damun mahaifiyarsu. Sai da wurin ya lafa da hatsaniya sannan Sarki Haruna ya fara magana. "Sarki Abdul'aziz muna zaune takarda ta iso gare mu dangane da 'yata Umaima, na gagara fahimtar sa on da ke ciki musamman da a ciki ka ce babu bu atar a sanar da mahaufiyarta abin da yake faruwa." Tun da ya fara magana Fulani Kilishi ta yi zuru gabanta na fa uwa, don tun da suka zo ba su ji a fitar sunan Umaima ba, kuma ba ta samu damar ewa da Muhsin ba ballantana ta ji halin da mahaifiyarsa take ciki. "Allah ya taimake ka ina ganin wa a a bakin mai ita ta fi da in sauraro, ayi mini afuwa zan gabatar da wa ansu mutane domin tattaunawarmu ta samu abin da ake bu ata." Amsa masa ya yi sannan Sarki Abdul'aziz da kansa ya shiga uwar akinsa ya yi magana a daidai shurin Dattijo Maharaz, bayan ya gabatar masa da abin da yake tafe da shi Dattijo Maharaz ya amsa da cewa. "Babu damuwa Sarki Abdul'aziz zan zo gare ku yanzu nan, don haka za ka iya sa wa a kawo ita Umaima domin a yi komai a fili ba tare da kowa ya ga an zalince shi ba." Cike da ladabi Sarki Abdul'aziz ya amsa wa Dattijo Maharaz sannan ya mi e ya fice, bayan komawarsa ya bada umarnin a je a taho da Jakadiya da Umaima. Sarki Abdul'aziz ya shiga babu jimawa sai ga Dattijo Maharaz sun shiga akin, hannunsa ri e da Boka Bamaguje suna tafe yana dogara sanda jikinsa na karkarwa. Daga can gefen bangon da ke fuskantar su Mai martaba Haruna suka zauna, suna zama aka shiga da su Fulani Umaima aka watsar da su a gefe tamkar kayan wanki, tun da suka shiga akin ya dum! Saboda wari nan take kowa ya sa gefen rigarsa ya toshe hancinsa. "Wannan tattaunawar ba za ta yiwu a haka ba har sai an tsaface su Sarki Abdul'aziz, shi kansa Bamaguje yana bu atar kintsawa." Dattijo Maharaz ya furta. "Babu wata kintsawa da zan yi ni wanka bai dame ni ba, shin ka ta a ganin Boka ko mai sihiri irina cikin tsafta ne? Mu gabatar da abin da yake gabanmu domin a yanzu haka akwai wata tarzomar da ke dumfaro ni, bayan wannan kuma ba ni da wadatacciyar lafiya kai shaida ne Maharaz a lokacin da ka je ka taho da ni." Bamaguje ya furta cike da agauta, ganin Bamaguje na som ba su matsala ya sa Sarki Abdul'aziz ya sa aka fara shiga da turarrukan wuta kala-kala ana sakawa domin samun sau in warin da yake addabarsu. Har Bamaguje zai fara magana Takawa ya sa aka kira su Inna wuro don ba aramin girma da mutumci yake ba su ba. Sai da Sarki Abdul'aziz ya gabatar wa Bamaguje mutanen akin sannan ya tsahirta suka zuba masa ido gaba aya suna jiran jin daga gare shi. Tun shigar Bamaguje Mahaifiyar Fulani Umaima take ta zabga gumi cikin tashin hankali, kuma yanayin da Fulani Umaima take ciki na sauyawar kammani ya sa babu wanda ya gane ta. "Sarki Abdul'aziz wannan ai karatun baya ne ake son ara maimaitawa, me kuke so na ce muku bayan fa in Umaima iyar cikina ce? Ga Kilishi nan ita shaida ce, tun tana budurwa take ziyartar wurina har bayan aurenta da Sarki Haruna, ita ta sani har yarjejniya muka yi yanzu kuma me ya rage." A zabure Sarki Haruna ya furta. "Me wannan mashirikin yake nufi? Kana nufin Umaima 'yata ita ce 'yar cikinka? Sarki Abdul'aziz Ina Umaiman take ne?" Da hannu Sarki Abdul'aziz ya nuna wurin da Fulani Umaima take kwance, lokaci aya jikinsu ya yi sanyi mamaki halin da take ciki ya kama su. Ganin Mai martaba Sarki Haruna na son nuna gardama ya sa Dattijo Maharza da Bamaguje suka fayyace masa komai tun daga farko har arshe, idanunsa na zubar da wallah ya waiga wurin Fulani Kilishi ya ce. "Shin abin da wannan Bokan ya fa a haka ne?" Kuka ta fashe da shi cikin nadama ta ce. "Ka gafarce ni ranka shi da e wallahi sharrin shai an.." "Sharrin shai an ko? Ki je Kilishi ke da Allah, amma ba zan iya ci gaba da zama da ke ba na sake ki saki uku! Ban san hukunci da Abdul'aziz zai yanke ba amma matu ar ya sallame ta ke za ki auki 'yarki ki tafi da ita." Murya na rawa hawaye na zuba ya waiga wurin Sarki Abdul'aziz sai da ru o hannunsa cikin walla ya ci gaba da cewa. "Ka gafarce ni Sarki Abdul'aziz bisa duk rashin imanin da Umaima ta aikata, duk hukuncin da ya dace ka auka a kanta kuma idan har akwai wani taimako dangane da hukuncin da za ka yanke a kanta a shirye nake na ba ka gudummawa ari bisa ari. Zan wuce gida don zuciyata zafi take idan na ci gaba da kallon wa annan miyagun mutanen zuciyata za ta iya bugawa." Ya arasa maganar yana yun urin mi ewa, fadawansa suka kare shi ya tashi har ya fara tafiya ya waigo ya kalli Fulani Kilishi. "Kin ci amanata kin zalince ni ki je ke da Allah, ga mahaifin 'yarki nan idan kin gama idda sai ki aure shi ki ora daga inda kuka tsaya." Daga haka ya saka kai fice zuciyarsa na yi masa aci. Fulani Umaima ban da ruwan hawaye babu abin da take yi, wahala ta sa ko magana ta kasa yi. Fulani Kilishi suka ji ta tsuntsire da dariya ta fara fisgar gashin kanta tana kai wa baki. Da sauri Sarki Abdul'aziz ya sa aka fita da ita ya bayar da umarnin da a fice da ita daga cikin masarautar gaba aya. Lokacin da Dogarawan suka fita da ita keken dokin su Sarki Haruna ya fito, ganin haka ya sa ta bi keken dokin da gudu tana she a dariya tana ce wa sai ta bi Sarki Haruna. Da Dogaran suka ga ta rage musu aiki sai suka juya suka koma cikin masarautar cike da jimamin abubuwan da yake faruwa. Shiru akin ya auka kowa da abin da yake jimantawa a zuciyarsa, Yarima Muhsin tun da aka shigo da mahaifiyarsa ya kauda kansa gefe yana zubar da walla. "Duk da ta aikata babban laifi mafi girma ita in uwar 'ya'yanka ce, me ya sa ka sa aka aikata mata wannan mummunan hukuncin? Wannan yaron Kamalu dama can Allah ya addara wannan addarar a kansa, yanzu ka ga a silar shi wa annan bayin Allahn suka shigo cikin masarautar nan. Ka ga kuwa bai da..." A an hanzarce Sarki Abdul'aziz ya katse Mai martaba mahaifin Fulani babba don ji yake zuciyarsa na tafasa. "Ranka shi da e kada ku manta ita fa ta raba mu da uwargidanmi kuma uwar 'ya'yanmu, ta raba sha uwar tsakanin a da mahaifiyasa, hasali ma ta raba ta da duniyar baki aya." Sarki Abdul'aziz ya arasa maganar muryarsa tana rawa. "Wallahi ko da Umaima ko babu Umaima sai Fatima ta mutu a wannan lokacin, kada ka manta kowanne bawa a rubuce kundin addararsa yake tun kafin zuwansa duniya, duk wani ciwo da ka ga ya samu Fatima dama can Ubangiji ya addara mata faruwarsa sai dai ta kasance ita ce sanadinta." Ajiyar zuciya Sarki Abdul'aziz ya sauke ya an ha iyi yawu mai aci, sannan ya russuna cikin girmamawa ya furta. "Ku gafarce mu ranka shi da e idan kalamanmu za su sosa muku rai, amma Allah Ya sani ba za mu iya yafe mata cin kashin da ta aikata wa Fatima ba." Daga haka Sarki Abdul'aziz ya sa aka sake fitar da Jakadiya da Fulani Umaima zuwa akin duhu. Kalaman da Sarki Abdul'aziz ya furta ba aramin faranta zuciyar mahaifiyar Fulani baba da 'yan uwan ya yi ba, Dattijo Maharaz ya dubi Mai martaba ya ce. "Ranka shi da e ni kuma wata alfarma na zo nema ban sani ba ko zan iya samu a wurinka?" Gaba aya mutanen akin suka tattara hankulansu wurin Dattijo Maharaz, "Ina sauraronka Dattijon arzi i wacce irin bu ata ce?" "Ina nemar wa Sarki Abdul'aziz arzi in sake nema masa iri a wurinka, ina nufin ina nema masa auren aya daga cikin 'ya'yanka domin ta maye gurbin Marigayya." Wani da i Sarki Abdul'aziz ya ji har cikin ransa, ya an saki murmushi amma shi kansa ya san zai yi wuya mai martaba ya sake aura masa wata 'yar ta sa. "Mun kar i alfarmarka Dattijo Maharaz, za mu duba a cikin iyalanmu wacce ta fi dace wa da shi. Bayan ita ko akwai wata bu atar?" Tashinta daga bacci kenan ta ji kanta ya sara mata, ta jima ba ta ji irin haka ba don haka ta an jingina da bango tana murza idanu. Ba ta ga Mai gado a akin ba kuma da ma ta san ba lallai ta ganta na tun da suna can suna hidimar abincin tarbar ba i, lalubulen akin ta ji yana ka awa a hankali ta kai idanunta wurin. A firgice ta mi e tsaye gabanta na fa uwa tsoro ya mamaye ta, kamar yadda ta saba ganinta cikin shirgarta ta kullin yau in ma a haka take a tsaye tana sakar mata murmushi. A an tsorace Jawahir