← Book details Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 89

Sashe 81

Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

cikinki!" Dire kalamansa ya yi daidai da jin cikinta ya auki ra i kamar yadda yake yi mata idan tambarin cikinta zai bayyana. Tsoro ya sake mamaye ta, jikinta ya ci gaba da karkarwa ganin ta kai arshen bango ta dur ushe a saman gwiwoyinta ta furta."Don Allah kada ka cutar da ni, ka yi ha uri idan wani laifin na yi maka." Jin sautin muryar Jawahir ya sake karya zuciyar Mahaifin Fargi. "Zan yi wata doguwar tafiya mai nisan gaske, tafiyar ba a waiwaye ballanta a dawo baya. Don girman tsafi da sihirin da na bu e ido kuna auwatarwa, iyayena ku yafe mini idan akwai laifin da na yi muku a baya." Kalama Fargi na bawa suka dawo masa cikin kunnuwansa ana gobe za ta yi tafiyar da har kawo wannan ranar ba ta waiwayo su ba tamkar yadda ta fa a. Goge wallar idonsa ya yi ya fara tunkarar Shugaba yana jin wata irin warin gwiwa na ratsa shi, don ba ya jin zai yarda ya sake rasa jinin Fargi a karo na biyu. "Biyayya ga Shugaba girmamawa amma ce, amma biyayyar da yankin nan suke yi wa Shugaba ita take ba shi lasisin da yake cin karensa babu babbaka a kanmu. Don natsayin abar bauta mu zama jajjirtattu a kan 'yancinmu, hakan ne zai arsa wa Shugaba shukku a ka cin kashin da yake aiwatar mana." Ya sake tuna kalaman da Fargi ta fa a masa a ranar da za ta yi bankwana da su. Kafin Mahaifin Fargi ya arasa tuni Shugaba ya isa gaban Fargi, ganin ya tunkaro ta da wani dogon aho ya sa tsoronta ya tsananta har ta fa i a can gefen. Da arfin tsiya Shugaba ya aga rigarta ya sa ahon hannunsa da niyyar zu e duk wata kariya da tasirin da tambarin cikinta ke auke da shi. Wani irin jan haske mai kama da harshen wuta ya mamaye fuskarsa, wata irin azaba ta mamaye saman fuskarsa mai auke da ra i. Tun da ya ga wannan jan hasken ya gifta masa bai sake ganin komai ba sai ma wani irin zafi da yake ji tamkar an watsa masa ruwan barkono, mamaki ne ya kama Jawahir arara ha e da tsoro. Hannunta ta kai saman cikinta tana mamakin wai yau wuta ce ta fito daga cikin cikinta. araji da ihun azabar da Shugaba yake yi ya ratsa cikin kogon dutsen gaba aya, har ya fara gayyato tsirarun mutanen da ke ma otaka da shi. Mahaifin Fargi na ganin haka ya arasa wurin Jawahir yana kukan farinciki. "Tsafi ya albarkaci rayuwarki, saihiri ya ci gaba da baki kariya har abada." "Ni ba matsafiya ba ce, kuma Inna ta ce mini sihiri da tsafi haramun ne ga duk wanda yake yi, idan ya mutu zai dawwama a wutar jahannama." Jawahir ta fa a tana an ja da baya, duk da shi ta lura ba ya burin cutar da ita amma shi inma ba ta amince da shi. Daga bakin ofar shigowa cikin kogon dutsen suka hangi tsirarun mutane na shigowa fuskokinsu auke da yanayin mamaki. Shugaba can gefe ya fa i har lokaci murza idanu yake kuma fuskarsa babu alamar onuwa ko jin ciwo, hatta idanunsa tangaram suke a bu e sai dai gaba aya baya ganin komai sai duhu. Sai da mutanen suka gama shigowa sannan suka ga Fargi ta ratso ta jikin bangon kogon dutsen, da mamaki suke bin ta da kallo wa ansu da suka san Fargi a baya baki sake suka fara kallon Jawahir suna kallon Fargi da ke tunkaro su. Kai tsaye wurin Shugaba ta isa sai da ta tsugunna ta dafa kafa arsa tun ba ta fara magana ba gaban Shugaba ya fa "Ya aka yi tasirin tsafinki ya haure nawa? Tabbas kin yi nasara a kaina Fargi." "Na sha fa a maka dama mai laya ya kiyayi mai zamani! Ita rana dubu ta arawo ce guda aya ce tak ta me kaya." Tana gama maganar ta watsa masa wani farin garin magani, sannan ta arasa wurin Jawahir da har lokaci tana asa a kwance ta ago ta. "Ba tun yau ba, na fa a miki tsoro ba ya daga cikin abi'a ko halayen zuri'ata. Ki zama mai kare kanki ba sai wani ya kare ki ba." Jawahir ba ta iya furta komai ba, ta ru o hannunta suka arasa wurin Mahaifinta. Da hannu ya shafa fuskarta lokaci aya hawaye ya fara bin kumatunta. "Wannan jininka ce, jikarka ce wato 'yar cikin Farginka." Haka kawai Sarki Sulaiman ya ji zuciyarsa duk babu da i abin duniya goma da ashirin ya mamaye shi, tunanin Fargi da rayuwarsu ta baya ta shiga dawo masa don haka ko da daddare da yar bacci ya yi awon gaba da shi, hatta iyalansa sai da suka lura da yanayin da yake ciki. Wani irin bacci ya dinga yi mara da i cike da mafarkan Fargi masu tsayawa a rai. Tun asuba ba ta yi ba bacci ya aurace masa, don haka ya ci alwashin a wannan ranar sai ya ziyarci Yankin Rumzu sai dai duk abin da zai faru da shi ya faru. Duk da a baya ma yakan badda kama ya je da kayan abinci ni i-ni i ya sa a kai wa iyayen Fargi kuma har kawo wannan lokacin bai daina zuwa ba. Ya tashi da niyyar tafiya sai kuma aka wayi gari Mai babban aki babu lafiya, don haka ya ha urewa zuwa har zuwa washegari idan jikinta ya yi kyau saboda yanayin girma ga shekarun da suka fara cim mata. Mai gado kusan yadda ta ga rana haka ta arasa ganin dare saboda tashin hankalin rashin sanin halin da Jawahir take ciki da matsanancin halin da Malam Umaru yake ciki na jinya, sai dai har gari ya waye babu wani ci gaba a ciwon Malam Umaru, hatta tsarki da alwala ita ta aura masa tana rayawa a ranta wata ila ko niyya ce ya yi ya gabatar da sallar asuba. Gari na wayewa aka dinga shiga yi mata jaje da dubiyar halin da mijinta yake ciki, hatta Ru ayya sai da jikinta ya yi sanyi ganin halin da yake ciki da kuma atan Jawahir Don haka Inna wuro ita ta ci gaba da ba su kulawar duk abin da Mai gado ta saba yi musu, Abubakar da yar ya ya yarda ta ba shi abinci don sai da Mai gado ta je ta saka baki sannan ya yarda. Basiru na isa Masarautar Huddam kai tsaye akin duhu wurin da aka rufe su Fulani Umaima ya nufa, wari da arnin da ke tashi a wurin bai hana shi tunkarar ofar ba. Da arfi ya doka ofar da afarsa ofar ta karye cikin takun isa ya shiga akin hannunsa auke da tsafatacciyar askar. Jakadiya da ke zaune a zube kamar kayan wanki cikin tashin hankali ta fara sakin fitsari, duk da jikinta babu wari haka ta fara jan jikinta da yar domin ceton ranta saboda a tsammaninta Basiru kashe su zai yi. Fulani Umaima ta takure a arshen bango ta yi saranda don azabar da take ciki gara mutuwarta da rayuwarta. Har Basiru ya arasa motsin kirki ba ta iya yi ba sai bin sa da take yi da jemammun idanunta, ta rame sosai ta yi wani irin ba i ga wa ansu ananan farare da jajayen tsutsotsi da ke manne a fatar jikinta. Sai da ya tsugunna a gabanta ya girgiza kai yana yamutsa fuska sannan ya furta. "Ki kwantar da hankalinki ba kashe ki zan yi ba, an wani abu zan samu a wurinki wanda zai amfani duniyata. Don ma maha in ya zame mini dole na ha a da ke saboda tasirinki na kasancewarki a matsayin uwa da babu abin da zai kawo ni wannan akin." "Don Allah kada ka cutar da ni Basiru, don na san nahaifinka ya gama horar da kai al'amuran tsafi da sihiri." Fulani Umaima ta yi maganar murya can asa saboda galabaita. "Kin san an ce kowa ya biya allonsa ya wanke, ba don kin ata rawarki da tsalle ba ai da tuni kina can kina cin duniya da tsinken tsire. Yanzu dai tun da kin tsinci talatarki a laraba ha uri ya zame miki dole, kin ga nan gaba idan aikina ya biyo ta kanki shi kenan." Muhsin na gama maganar ya ture Fulani Umaima a asa, tsafatacciyar askar hannunsa ya sa ya fara re ar gashin kanta yana zubawa a cikin wani anin on tsafi, sai da ya aske gashin kanta tas sannan ya yanki faratan afafuwanta. Bayan ya gama ya soki cinyarta da askar nan take jini ya fara tsattsafowa ya dinga lakuta da wani farin yalle yana goge jinin. Tun da ya fara gogar jinin jikinta ta fara jin wani irin zuuu kamar ana zu e jininta, tana nan zaune hawaye ya wanke mata fuska babu yadda za ta yi, tana gani ya gama ya fice daga akin. Sai ya fice Jakadiya ta samu sukunin sauke ajiyar zuciya, duk da ta san wace ce Fulani Umaima a warewa wurin mugunta amma ganin yadda siffa da kammainta ya sauya sai da ta bata tausayi, duk da ita inma abar tausayin ce. Sarki Abdul'aziz shiru ya yi bayan ya gama sauraren Dattijo Maharaz, ya dubi Kamalu da lokaci guda ya ga ya zabge sannan ya mayar da kallonsa wurin Dattijo Maharaz. "Yanzu me ye abin yi tsoho mai ran arfe?" "Tafiya asar Sarki Sulaimanu! Don haka ne ma jiya da daddare ban ziyarce ka ba." "Amma kuma mahaifiyarta tana cikin ki ima bisa abin da ya faru da mai gidanta, kuna ganin za mu iya sanar da ita abin da yake faruwa?" Sarki Abdul'aziz ya tambaya. "Zuwa da Mai gado wannan garin yana da matu ar muhimmanci, ni na san su waye al'ummar rumzu kuma na san kafiya da taurin kansu." Dattijo Maharaz ya waiga wurin Kamalu sannan ya ci gaba da cewa. "Kamalu ka kula da Malam Umaru sai ka nemi wasu Bayin su taya ka kula da shi." Kamalu bai so haka ba amma kuma mutumci da imar Dattijo Maharaz ya sa ba zai iya musa masa ba. A safiyar wannan ranar Sarki Abdul'aziz da kansa ya sa aka shirya masa keken dokinsa da sauran tantina, mutane sun
Chapter 81 · 0% Book details