← Book details Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 89

Sashe 34

Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ma yau jin ta take kamar sauran mata don idan ba ta manta ba rabonta da shi an auki shekaru masu yawan gaske. Wani irin zafi ne ya fara ratsa asanta tamkar an sa kaifaffiyar wu a ana yun urin fisgo asanta ta arfin tsiya, wata irin ara ta ji Takawa ya saki a imauce ya ja da baya hankali a matu ar tashe. Jinin da ta gani yana tsattsafowa daga jikinsa ne ya sake tarwatsa ragowar warin gwiwarta. "Ni ba na kishi da ke domin na san na riga da gama da shafinki, domin da ke da babu a wurin Takawa aya kuke." Kalaman Fulani Umaima suka dawo mata ranar da wani sa ani da bai taka kara ya karya ba ya ha a su. "Ni fa hankalina bai kwanta da wannan kishiyar taki ba an ya kuwa babu sa hannunta a wannan ciwon naki?" Sai a yanzu kalaman Yaya Halima suka sake samun gurbin zama a zuciyarta. Numfashin Mai martaba ya katse mata tunani. "Don Allah ka yi ha uri! Ban san me ya haifar da hakan ba." Fulani babba ta fa a jiki a sanyaye, a angare aya kuma wata irin kunya ta mamaye ta. Da kallon tausayi ya bi ta sannan ya furta, "Kada ki damu In shaa Allah ranar Juma'a idan Malam Liman ya dawo zan sa a nema miki magani." Farincikin Fulani babba ya bayyana har a fili, ta share wallah tana sake jin aunar mijinta na taso mata. "Na gode ranka shi da e. Allah ya dawwamar mana da zaman lafiya har arshen rayuwarmu." Murmushi ya sakar mata sanna ya yun ura har lokacin jikinsa bai daina tsatssafar da jini ba, ga wani an zugi-zugi ha e da ra i da yake ji. ai tsaye ya wuce ban aki don ya gyara jikinsa. Da sauri Inna wuro ta janyo hannunsa gabanta na fa uwa, wato ana murna ba o ya tafi ashe yana bayan gari. Tun suna Rigar Ar o suka fahimci irin gane-ganen da yake yi tun yana aramin yaro, irjinta na bugawa ta dubi shi. "Babu abin da nake gani Kamalu don Allah daga yau kada ka sake zuwa wurin na." Kamar zai yi kuka ya bi ta da kallo. "Inna kin ga abin da yake yi." A an tsorace Inna wuro ta waiga wurin da yake nuna mata amma babu abin da ta iya gani. "Don Allah koma waye yake arin ta a mini a ya yi ha uri, ku yi ha uri In shaa Allah ba zai sake zuwa wurinku ba." Inna wuro na gama magana ta ja hannun Kamalu yana an cijewa da sauri Dattijo Maharaz ya arasa wurinsu ya ce. "Ka bi mari iyarka don ka yi dace da mari a na gari. Amma ina son yau da daddare ka ce musu su baka labarin abin da ya faru a Dajin Wushushe a daidai gefen oramar inya, a ranar bikin sha i." Kai kwai Kamalu ya iya gya a masa sakamaon fisgar hannunsa da Inna wuro take yi har suka arasa cikin sashensu na Bayi. Ganin yanayin yadda su Inna wuro suka shiga ya sa Baffajo ya ura mata ido. Duk abin da ya faru Inna wuro ta kwashe ta ba wa Baffajo labari, Baffajo ya kalli Kamalu sannan ya dafa kafa arsa. "Kamaludeen!" Baffajo ya kira shi da wani irin yanayi. "Ba tun yau ba jikina ya jima yana ba ni kai na musamman ne sai dai ina tsoron kada miyagun su saka mini kai a gaba. Don Allah ka ri a takatsantsan, ka ga yanzu kai da 'yar uwarka A'iru ne ka ai kuka rage mini." Murmushi Kamalu ya yi don a tsammaninsa Baffajo rufe shi zai yi da fa a, Inna wuro za ta yi magana Kamalu ya dakatar da ita. "Baffajo wai mene ne ya faru a Dajin Wushushe a daidai gefen oramar inya, ranar bikin sha i..." Kallon da ya ga sun wurga masa a tare kusan lokaci aya ne ya katse arshen maganarsa, take tsoro ya mamaye zuciyarsa ya an ja da baya. "Waye ya ce ka yi mana wannan tambayar?" "Ba komai za ka ri a sanar da su Baffajo ba, idan ka na son na dinga amsa maka tambayarka. Idan sun tambaye ka kawai ka ce musu mafarki ka yi, ka yi mini al awari?" Tsawar da Baffajo ya buga wa Kamalu ce ta dawo da shi hayyacinsa a lokacin da ya lula duniyar tunanin wata hira da suka ta a yi da Dattijo Maharazu. "Baffajo kawai a mafarki ne aka ce na tambaye ku!" "Daga yau idan na sake jin makamanciyar wannan maganar sai ranka ya yi mummunan aci ka ji me na ce?" Kamalu ya amsa wa Baffajo cikin matsanancin tsoro. Hawayen takaici, damuwa da tashin hankali ne ke rige-rigen tsiyayowa daga kwarmin idonta, ta tura kanta cikin afafuwanta kamar aramar yarinya sai da ta yi kuka mai isarta sannan Fulani babba ta furta. "Ya Ubangiji ina godiya bisa wannan jarabta da kake yi mini, Ya Allah ka yaye mini wannan miyagun al'amura da suke bijirowa rayuwata ko na yi mu'amala da mijina kamar kowacce mace." Kuka ne ya ci arfinta ta jima a haka sannan ta fa a ban aki ta watsa ruwa ta koma kan gado ta yi lamo kamar mara lafiya. Sai da dare ya tsala sosai kamar sabuwar munafuka Jakadiya ta bi bayan akunan Bayi ta nufi bakin wata bishiyar orawa hannunta aya auke da beran da Boka Shaddas ya ba ta, da sauri-sauri ta hau ha a rami ta tura beran da ransa cikin ramin ta mayar da asar ta rufe sannan ta taso zuciyar al kamar wacce aka yi wa bushara da Aljanna. A ranar Jakadiya bacci ta yi sosai don har sai da ta kusa makara sallar Asuba, saboda tsananin farinciki. Tun da Fulani Umaima ta zo duniya maganar auren Mai martaba ce abu na biyu da ya yi mummunan aga mata hankali, daga lokacin da Bamaguje ya sanar da ita Fulani Babba na da cikin Abubakar sai wannan maganar. Haka ta yi ta fa i tashi daga wannan boka zuwa wannan boka sai dai ita kanta tana zuwa ne amma babu wani sauyi ko ci gaba da ake samu daga wurin Mai martaba, sai ana iya kiran ci gaban na mai ha ar rijiya sakamakon wani zaman doya da majar da suka cigaba da yi, cikin tsangwama, kyara da hantara dga wurin Mai martaba. Ganin haka ya sa ta uduri niyyar zuwa wurin Takawa don ta kwantar da kai cikin kissa da kisisina. Wanka ta tsala ta yi kyau sosai sai dai kuma ta an fa a fuskarta ta yi fayau, bayan Sallar Magriba ta isa Turakar Mai martaba a lokacin ko iso ba ta jira ba. amshin turarenta ne ya buge shi, a hankali ya ago yana kallonta sai kuma ya kawar da kai gefe ya amsa mata sallamar a ciki. "Yanzu a kan antacciyar Baiwa Sailuba Mai marta ya mayar da ni bora, lallai duniya juyi-juyi kwa o ya buga tsalle ya fa a ruwan zafi." Fulani Umaima ta yi maganar a zuciya. Murmushin ya e ta aro ta yafa wa fuskarta sannan ta arasa har gaban gadon da yake kwance. "Ni mai laifi a gare ka ce kuma ban farka daga halin da na tsinci kaina a ciki ba sai da na fahimci muhimmancin abin da kake arin aiwatarwa. Don Allah ka yafe mini Sarkina, na gane kuskurena kuma a shirye nake na kar i duk wani hukunci daga gare ka komai tsaurinsa." Fulani Umaima ta arasa maganar cike da rauni, wallah ta fara gangaro mata ta fara shasshekar kuka mai jan hankali. "Tun da ma can ba mu ri e ki ba kawai mun aga miki afa ne domin mun lura kina bu atar haka." Wani ululun ba inciki ya sake mamaye ta ganin yadda yake sha mata amshi. Ta ru o hannuwansa har lokacin tana zubar da hawaye ta furta, "Sai nake ganin kamar Mai martaba bai gamsu da tubana ba, ranka shi da e za ka iya hukunta ni da duk abin da ka yi niyya matu ar zai sanyaya zuciyarka. Ban fahimci alkairi ne yake waso mana ofa game da auren Sailuba ba sai a mafarki da na yi jiya, tabbas Sailuba za ta zame mana tamkar yabanyar da kowanne manomi yake burin samu a gonarsa. Na ga tarun alkairai a game da ita har zuwa Yarima, dalilin da ya sa na fahimci kuskurena tun farko. Amma idan kana bu atar na baka wuri zan wuce ranka shi da e matu ar hakan zai sanyaya zuciyarka." Tun lokacin da ya ji Fulanin Umaima ta ambaci sunan Sailuba wani farinciki ya mamaye birnin zuciyarsa, tana shirin mi ewa ya kamo hannuwanta ya zaunar da ita kusa da shi. "Mun fahimci kuskurenki, don haka a kiyaye duk wani abu da zai ta a martabar da mutumcin Sailuba." A an razane ta dube shi jin wa annan kalaman na Takawa masu kama da ruwan dalma a cikin kunnuwanta, babu yadda ta iya haka ta danne ta alo murmushin arfin hali. Ta yi arin bin Yarima a sha ki a duk don ta kai ga cim ma muradinta. Dare ranar daga Fulani har Sarki Abdul'aziz sun gudanar da shi cikin matu ar farinciki musamman Fulani Umaima ta ga ta mantar da Takawa 'yar togaciyar da ta shiga tsakaninsu. Dalilin da ya sa ta sake sakin jiki aka shiga shagalin bukukun kamar babu komai a ranta. Rana ba ta arya sai dai uwar iya ta ji kunya. Kamar yadda Mai martaba ya fa a ranar juma'a aka aura auren Khadija da Yarima Safwan, sai kuma Sailuba da Sarki Abdul'aziz. Gidan ya kacame sosai ba i ta ko'ina arkowa suke suna taya Mai martaba murna. Kafin wani lokaci tuni masu wasan gargajiya da 'yan bori suka fara cin kasuwarsu cikin warewa da tabbatar da al'adun hausa. Jakadiya wani irin farinciki ta ri a ji kamar ta zuba ruwa a asa ta sha, haka daga angaren Bayi zuciyoyinsu tas sakamakon wannan ranar ta kasance musu tamkar ranar cin gashin kai. Bayan sallar juma'a aka shirya Khadija cikin shiga ta alfarma da asaita, aka mi a ta wurin Takawa ta kansa ya ri e mata hannu bayan ya yi mata
Chapter 34 · 0% Book details