← Book details Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 89

Sashe 86

Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Shu'aibu, Alaramma da Babban Malami. Shu'aibu da Babban Malami dukkansu cikin siffar bil'adam suke tamkar mutane ba jinsin aljanu ba. "Barka da zuwa babban Malami, mun taso ka babu shiri a yi mini afuwa dole ce ta sa haka." Dattijo Maharaz ya furta cikin girmamawa. "Assalamu alaikum. Barkanka dai Dattijo Maharaz ai tun da na ji haka na san babban uzuri ne ya haifar da haka, amma ina fatan ba Dela ce ta auko mini wata maganar ba." Babban Malami ya furta yana kallon Abar bauta da har lokacin ba ta bayyana kanta sauran mutanen su ganta ba. Da mamaki Dattijo Maharaz ya ce. "Malam da ma ka santa ne?" Murmushin takaici Malam Liman ya yi ya ce. "Ban yi mamakin jin haka daga bakinka ba Marahaz, domin tun shekaru masu yawa a baya na sallama Dela daga matsayin 'yata. Ka san a ne ka haife shi ba ka haifi halinsa ba." Mamaki ya sake mamaye Dattijo Maharaz da su Sarki Sulaimanu, nan take ya zayyane wa Babban malami duk abin da yake faruwa yana gama sauraronsa ya furta. "Innalillahi Wa'inna'lahir Raji'un! Yanzu Dela hatsabibancinki har ya kai ki dinga ha a kanki da Ubangiji Dela? Na yi da-na-sanin haihuwarki tir da irinki a doron asa." "Tun da ka sallama ni me ya yi saura Don Allah Baba ka tsame kanka daga cikin maganar nan." Abar bauta ta furta cikin tsiwa. Mamaki ne ya mamaye mutanen wurin wai Abar bautarsu da ta ce musu ita take hallitarsu take ciyar da su ta shayar da su ita ce har take da mahaifi kuma yake tsaye a gabansu. "Tun da har kika shiga hurumin Ubangiji ai sai in da arfina ya are a kanki, ko ka an rayuwarki ba ta da amfani, ashe kin san da Ubangiji kika ora su a wata hanyar daban. Allah wadaran halinki Dela na san har abada ba za ki sauya halinki ba." Malam Liman ya yi maganar wallah na zuba daga idonsa. Sai da suka aura alwala shi da Alaramma sannan suka fara karanta ayoyin da suke magana akan azaba, nan take ita da mu arrabanta suka fara ihu da araji cikin tashin hankali. Tsiraru daga cikin mutanen wurin suka fara yanke jiki suna fa uwa na su aljanun suna tashi, sun jima suna karatun Al ur'ani tun suna jin muryoyi daban-daban har sautin ya fara raguwa wanda hakane ne ya tabbatar musu da sun one wasu sai abin da ba a rasa ba. Zumjuttu tun da aka fara karatun ta gudu cikin jin tsananin azaba. Suna nan tsaye carko-carko suka ga wata hallita ta bayyana, tamkar tsuntsu haka take. Kanta akwai manyan aho guda biyu, ta bayanta akwai jela sai afafuwanta kamar na doki idanun uku a fuskarta. Da gudu suka ja da baya har su Sarki Abdul'azia, cikin acin rai Mahaifinta ya ce. "Ki dubi dubban al'ummar nan ina za ki je da hakkinsu, tun wuri ki fito ki sanar da su ke ba Ubangiji ba ce. Ke hallitar Allah ce kuma ko a yanzu zai iya aukar rayuwarki. Ki sanarda su Allah S.W.A. Shi ne Ubangiji sammai da assai, Ubangijin mutum da alja kuma Ubangiji duk wata halitta da ke fa in duniyar nan." *SHU'UMAR MASARAUTA* *45* *Littafin ku i ne 500 idan kina bu ata za ki biya ta wannan Account in Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*
Chapter 86 · 0% Book details