Sashe 79
Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
addu'a za ki masa, domin Ibrahim ya matu ar nuna miki kulawa." Sai da Yaya Halima ta sha kuka mai isarta sannan Mai martaba ya yi mata bayanin duk abin da ya faruwa a Masarautar Huddam, da kuma hukuncin da ya yanke game da ba wa Sarki Abdul'aziz auren wata 'yar tashi, daga arshe ya tabbatar mata da ita ce wacce ya za ar wa Sarki Abdul'aziz tun da ta samu lafiya. Jin kalaman Mahaifinta ba aramin imautata ya yi ba, ganin halin da ta shiga ya sa ya sallame ta a kan ta je ta yi nazari idan an kwana biyu zai sake ji daga gare ta. Daga can gefe Boka Shaddas ya tsaya yana kallon Shugaba Zurufu, yana son tambayarsa matsayin Basiru wani irin tsoro ya mamaye shi. Yana nan tsaye ya ga ya yayyfa wa Jawahir ruwa nan take ta fara motsi a hankali ta fara bu e idonta, zumbur ta mi e tsaye tana arewa wurin kallo sannu a hankali komai ya shiga dawo mata. Tsoro ya sake mamaye ta a lokacin da ta yi tozali da Shugaba Zurufu da yake a duke saboda tsufa. "Kamar kumbo kamar kayanta, wannan kama ta yi kama tamkar an tsaga kara ke da mahaifiyarki." Ja da baya Jawahir ta fara yi Shugaba Zurufa yana sake tunkararta. "Na riga da na cika aikinka ina ana Basiru yake?" Boka Shaddas ya furta murya babu alamun wasa. Waigowa Shugaba Zurufu ya yi a hankali jikinsa na karkarwa, fuska auke da murmushi ya zuba wa Boka Shaddas idanu har sai da gabansa ya fa i. Don ya tabbata banza ba ta kai zomo kasuwa wannan murmushin da Shugaba yake yi ba zai tashi a banza ba. "Me kake ci na baka na zuwa Shaddas ai duk gaggawar Ungozoma ta bari a haife." Boka Shaddas ya yi wafa bai tanka masa, Shugaba Zurufu ya fara matsawa gaban Jawahir sannan ya furta. aga mini rigarki." Rass gaban Jawahir ya fa i. "Don Allah waye kai, ku duba girman Allah kada ku cutar da ni." Cak Shugaba Zurufu ya tsaya yana jinjina kai sannan ya furta. "Tabbas ko iya haka Fargi ta bar mu ta kusa yin galaba a kanmu, ta ci alwashin ya a zuri'armu abin da ba ta sani ba har addininmu ta so dakushewa." Kafin ya rufe bakinsa ya ga wata tsuntsuwa ta ratso ta jikin bango cikin shammata ta warci littafin labarin Hidaya da tun kwantar da Jawahir a kan farin dutsen ya fa i a asa. Daga Boka Shaddas har Shugaba Zurufu bin tsuntsuwar suka yi da kallo, da sauri Shugaba ya yun ura da zummar ya wato shi amma sai ya gagara. Daga can bakin ofa wani Dattojo ne tafe da anyan naman bunsuru auke a saman kafa arsa, sai da ya arasa gaban Shugaba ya zube yana haki sannan ya furta. "An aiwatar da komai Shugaba shin akwai abin da kake bu ata?" Ganyen da ke aure a jikin dattijon Shugaba ya sunkuya ya goge gumin goshinsa cike da wula anci sannan ya furta. "Babu bu atar wani abu amma kalli can?" Ya yi maganar yana nuna wurin da Jawahir take tsaye. A gajiye Dattijon ya mi e yana bin wurin da kallo ha e da ura wa Jawahir ido, lokaci aya jikinsa ya auki karkarwa bakinsa na rawa ya nuna Jawahir yana fa in. "Faff... Fargi! Ke idanuwana suke gani ko gizo suke yi mini." Cikin yanayin mamaki Jawahir ta bi shi da kallo sam ba ta fahimci abin da suke nufi ba. "Shugaba Fargi ta dawo gare mu." Mahaifin Fargi ya yi maganar cikin tsananin farinciki, hawaye bibbiyu ya fara zuba daga idanunsa. "Na da e da fidda rai da sake yin tozali da ke ashe akwai sauran ganawarmu a gaba..." "Wannan ba Fargi ba ce." Kalaman Shugaba Zurufu suka katse Mahaifin Fargi. Shiru ya yi yana ci gaba da kallon Jawahir don da a ce ba laifi ba ne da ya musa kalaman da ya ji Shugaba ya yi. "Wannan jinin Fargi da Sarki Sulaimanu ce, kuma ni na aika aka auko mini ita domin na san mahaifiyarta ba za ta bar ni haka ba. Don haka za ta ci gaba da zama a ashin ikona, na sha ba ar wahala kafin na banka o ainihin wurin da ta oye ta. Tabbas Fargi hatsabibiya ce ta arshe, ni kuma na nuna mata duk girman kuka bagaruwa ce babba." Kuka Mahaifin Fargi ya fashe da shi yana jin tausayin rayuwar yarinyar da ba ta san rikiscin da ya wakana a shekaru goma sha shida da suka wuce ba. Ya san ba shi da ta cewa don haka ya ja bakinsa ya yi shiru, saboda tun ranar da Fargi ta bar cikin garin suka koma masa tamkar Bayi shi da mahaifiyarta da 'yan uwanta maza. "Na gaji da gafara sa ban ga aho ba Shugaba ka ba ni ana na wuce da shi." Boka Shaddas ya furta a agauce. Shugaba bai tanka masa ba wuce can bangon akin da ya ta oye Basiru sannan ya zura hannu ya janyo shi, cikin wata irin tafiyar ta ama da asaita Basiru yake taku ai yana bin mutanen kogon dutsen da kallo har suka arasa wurin mahaifinsa. Hannu Boka Shaddas ya kai zai ru o hannun Basiru da sauri ya Basiru ya aga masa hannu. "Dakata! Ni ba aramin yaro ba ne." Ya furta da wata irin atuwar murya. A an tsorace Boka Shaddas ya dube shi sannan ya mayar da kallonsa kan Shugaba. "Na ga sauye-sauye game da Basiru, me ya faru Shugaba Zurufu?" "Guda ka ba ni kuma ni ma guda na dam a maka ka ga babu kare bin damo!" Shubaba ya furta a ta aice. "Idan za ka wuce ka zo mu tafi ka da ka ata mini lokaci idan ba haka ba zan koma wurin da na fito." Basiru ya furta yana wurga jajayen idanunsa masu kama da sabon borkono. Boka Shaddas ba shi da mafita a dole ya rufa wa Basiru baya har suka fice daga cikin kogon dutsen, zuciyarsa na wasu-wasin sauyin da Basiru ya samu. Tun da Malam Umaru yanke jiki suka fa i ko ka an Bawa Lawandi bai motsa ba, shi kansa Umaru cikin fitar hayyaci yake juya kansa daga kwance ba tare da ya san inda kansa yake ba. Kamar daga sama Mai gado na zagayowa ta hange su a asa, cikin tashin hankali ta walla ihu ta fa a kan Umaru tana jijjiga shi ha e da kiran sunansa. Ganin kukan ba zai kai ta ba ya sa ta fita a guje tana kururuwa neman auki, nan take Bayi suka cika sashenta aka shiga yayyafa musu ruwa sai dai ko ka an Lawandi bai motsa ba a nan suka tabbatar da rai ya yi halinsa. Malam Umaru aka auka a ka kai akin Mai gado a lokacin ya daina jujjuya kansa sai dai zuru ya yi yana bin mutane da kallo, duk yadda Mai gado ta so ya yi magana sai dai ya bi ta da kallo. Wannan mummunan yanayin da ya afkar musu ba aramin a mutane ya yi ba, musamman mutuwar Bawa Lawandi da ya kasance mutum mai barkwanci ga kyakkyawar mu'amala da mutane. Duk wannan abin da yake faruwa babu wanda hankalinsa ya kai kan Jawahir, sai bayan da aka sallaci gawar Bawa Lawandi sannan Mai gado ta farga da rashin ganin Jawahir. Wani sabon tashin hankalin ne ya mamaye ta da aka bincika ciki da wajen Masarauta ba tare da anganta ba, hasali ma Ru ayya ta bada tabbacin ta ga shigarta aki, sai dai ta ce ba ta ga giftawarta ba. Nan take labarin atan Jawahir ya zagaye cikin masarautar sai dai wannan al'amarin ba aramin aga hankulan mutane ya yi ba sakamakon babu ba on fuska aya da suka yi tozali da shi ballantana a zargi wani abu daga gare shi. Shi kansa Sarki Abdul'aziz ya ka u da jin labarin abin da ya faru, a angare aya ya fara tunanin ko saboda Muhsin ya nuna ita yake so shi ya sa ta yi haka, don a lokacin da Muhsin ya yi maganar ya lura da acin rai a saman fuskarta. Tun a daren ranar Sarki Abdul'aziz ya sake baza sojojin masarautar da dogarawa don su ci gaba da binciken ciki da wajen masarauta ko za su gano wani labari. Lokacin da Kamalu ya ji labarin atan Jawahir zuciyarsa tamkar za ta buga shi ka ai ya dinga zagaye a aki yana sake jin haushin Muhsin ya mamaye shi, don shi ma gani yake duk ta silarsa ce Jawahir ta ace. Da zuciya ta ebe shi kasa ha uri ya yi ya wuce akin Muhsin, ko neman izini bai yi ba ya fa akin a lokacin ya samu Muhsin zaune ya zuba tagumi da hannuwansa biyu. "Tun wuri tun ba a je ko ina ba ka yi gaggawar janye soyayyarka a kan yarinyar nan domin ba ta aunarka, domin kana ganin yadda kalamansa suka sa aka neme ta sama da asa aka rasa." Kamalu ya furta da tsananin ba inciki. "Fi ce mini daga aki idan ba haka ba ranka ya yi mummunan aci! Kai ba ka san bala'i ne a gare mu ba? Ka da ka ga ina aga maka afa ka nemi ka shigar mini hanci da udundune, tun da ka bayyana gaba aya bala'i da musibu suke afkowa cikin masarautar nan wallahi kai ba aramin annoba ba ne..." Cikin hanzari Kamalu ya katse shi. "Wallahi-wallahi tun kafin gari ya waye ka fito da ita idan ba haka ka fuskanci hukuncin da mahaifiyarka take fuskanta a yanzu." Daga haka Kamalu ya fice daga akin a zuciye. Duk da dare ya fara yi sosai hakan bai hana ganin mutane sun yi carko-carko ba kowa cikin alhini da jimami, Kamalu har zai wuce sashensa Dattijo Maharaz ya fa o masa da sauri ya nufi sashen Sarki Abdul'aziz, a lokacin da ya shiga ya samu mahaifinsa yana zaune. Sai da suka sake gaisawa sannan ya an sunkuyar da kai asa ya furta. "Dama Ranka shi da e wata magana ce gare ni." "Tafi kanka tsaye Kamalu!" "Allah ya taimake ka dama ce wa na yi ko za a ji daga bakin Dattijo Maharaz a