← Book details Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 89

Sashe 40

Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sauke na sake zuba masa idanu. "A labarin da aka ba ni kakanki tun tasowarsa ya kasance hatsabibi mara tsoro, don an ce wa ansu daga cikin jinsin aljanu har tsoronsa suke ji. A wannan lokacin kuma a kwai an sarkin ba en aljanu Darri da ya taso cikin ta adiranci da hatsabibanci kuma ko ka an ba sa ga maciji da kakanki, a wannan lokacin sai shi Aljani Dharri ya so auren Kakarki dalili kenan da ya ara tsaurara tsattsamar ala arsu. Da yake sun bu e wa kakanki idanu sai ya zamana yana ganinsu muraran har su yi ta sa'insa, daga arshe dai Kakanki ya yi galaba a kanshi don haka sai ya karya adarin Darri, duk hatsabibancinsa sai ya yi la was kuma ya zubar da makamansa. Kwatsam babu zato bayan wa ansu shekaru masu tsayi sai aka wayi gari an autan Dharri ya kamu da matsananciyar soyayya da mahaifiyarki. Da farko mahaifiyarki ba ta san Buhsu ba mutum ba ne, domin idan ya tashi zuwar mata a surarsa ta bil'adam yake zuwa. Sai da ya fahimci soyayyarsa ta yi arfi a zuciyarta sannan ya bayyana mata ainihin zubi da surar hallitarsa. Da yake shi so undunbala yake ya hana ganin laifi ko gezau mahaifiyarki ba ta ji za ta iya rabuwa da shi ba, sai ma soyayyarsa da ta mamaye zuciyarta. Akwai abin da na manta ban sanar da ke ba." Jin kalaman Sarki Hafiz ya sa na ago da sauri ina kallonsa, ya jinjina mini sannan ha e da fa A razane Fulani Umaima ta rufe littafin babu shiri sakamakon jin muryar Jakadiya ra au a tsakiyar akinta, da sauri ta mayar da littafin ta mi e ta fito fuska ba yabo ba fallasa. "Umaima wani sabon labari na ji da farar safiyar nan shi ne na zo na ji wanne tuggun kika ha a wa baiwar Allahr da ba ta ji ba; ba ta gani ba?" A yamutse Fulani Umaima ta dube ta. "Wai dama kura ce za ta ce wa kare maye? To wai ma wane dare ne jemage be gani ba? Zuwa kika yi ki raina mini hankali Jakadiya da za ki kawo mini wannan maganar?" "Fulani na san rashin imaninki sarai, ni kin gan ni na fara tuba ga Ubangiji don zalinci da muka shuka a gidan nan na fara fargaba da tunanin ranar girbarsa." Jakadiya ta yi maganar kamar wacce tsoron Allah ya samu matsuguni a zuciyarta. Shewa Fulani Umaima ta yi sannan ta furta. "Duk ma abin da kika yi tsammani zan iya aikatawa Jakadiya, kin fi kowa sanin wace ce Umaima don haka ofa a bu e take da za ki iya zartar da hisabinki a kaina." Gaban Jakadiya ya fa i, don wata irin fargaba ce ta dirar mata. Ganin ba ta da abin fa a ya sa ta fice daga akin kai tsaye da fa a sashen Fulani Babba. irjin Kamalu ya ci gaba da bugawa jin labarin da Baffajo yake ba shi, wani irin nauyi kansa ya yi har yaji afafuwansa na yun urin bijirewa nauyinsa. Da sauri ya fice daga akin, ya ci gaba da wurga afarsa cikin sauri ba tare da ya san inda yake sa afarsa ba. Can wani an siririn lungu ya bi mai tsananin duhun itace, ya sa mu bakin bishiyar orawar da ke wurin ya zauna. Hannuwa biyu ya sa ya dafe kansa cikin matsananciyar damuwa, tamkar aramin yaro haka walla ta fara bin idanuwansa zuciyarsa na yi masa una. "A wannan lokacin da kake ciki sam kuka ba zai fisshe ka ba, kuka da raunin zuciya bai yi daidai da tsarin zubin hallita da ruhinka ba. Ina sake yi maka tuni da kai ba kamar su ba ne, ina ora ka a hanya ne saboda aminantakar da ke tsakanina da marigayi Sarki Muhammad Safwan. Ba ni da ikon da zan shiga huruminka domin zuri'ar da ke tare da kai akwai ji iyar 'yar tsamar da ke tsakaninmu don haka na ke yun urin ora ka a hanya, idan na nemi na fayyace maka komai zan iya jefa zuri'ata da ta mutanen cikin gidan nan cikin rijiya gaba dubu, da babu rai aya da zai iya tsalle ballantana ya fito. Burinsu su ci gaba da zama tare da kai domin su ri a cin gajiyarka, amma na tabbata ko ba da e ko ba jima akwai lokacin da gaskiya za ta yi halinta. Ina mai ha urtar da kai mummunan lamarin da zai afka wa rayuwarka babu tsammani, sai dai ina mai shawartarka da ka sanyaya zuciyarka a lokacin da komai zai bayyanar maka." Gama jin kalamansa ya sa Kamalu ya ago a sanyaye, ko ka an bai fahimci kalamansa ba don haka ya sake sunkuyar da kai ha e da fa a wa duniyar tunani. Jakadiya ta matu ar tsorata da ganin yadda Fulani babba ta koma a cikin kwana aya jal tamkar wacce ta shekara guda tana jinya. "Jakadiya ki dubi Allah ki ce wa Takawa ina bu atar ganinsa, akwai kalaman sirrin da suke cikin zuciyata da nake son sanar da shi, kalaman da shi ka ai ya cancanci saninsu don a ganina watarana za su yi masa amfani." Fulani babba ta yi maganar murya can asa idaununta har sun fara shanyewa. "Idan gemun an'uwanka ya kama da wuta maza yi saurin yayyafawa naka ruwa." Jakadiya ta yi maganar a zuciyarta, saboda ganin jikin Fulani babba ba aramin tsoratata ya yi ba. Jiki a sanyaye ta fice kai tsaye ta nufi sashen Takawa a wannan karon tausayin Fulani babba ne arara a zuciyarta. "Allah ya taimaki ubangidana wani muhimmin sa o ne tafe da ni ranka shi da e." Jakadiya ta furta cikin girmamawa. "Muna sauraronki Jakadiya." "Allah ya taimake ka Fulani ta wayi gari cikin matsananciyar jinya har ta kai tana son ganinka domin ta ba ka wasiyya." Take annurin fuskarsa ya auke har sai da Jakadiya ta sha jinin jiminta. "Jakadiya a fice a ba mu wuri muna tattaunawar sirri da manyan ba i, a je a ce wa Fulani Umaima ta yi duk abin da ta ga ya dace game da magungunan da za a aika mata, idan da hali a gaggauta aikawa sashen ma'ajiyar magunguna idan mun kammala za mu san abin yi." "Ai na san dama biri ya yi kama da mutum, kallo aya na yi wa Fulani na fahimci tsafin Umaima ne ya ci ta, ya zame mini dole na tashi tsaye a kan Sailuba." Jakafiya ta yi maganar a cikin zuciyarta. "Jakadiya muna bu atar a ba mu wuri, ba ma bu atar sake ganin kowa a sashenmu." Kalaman Sarki Abdul'aziz suka sauka ra au a saman kunnuwan Jakadiya, ba inciki da ya cika ta kai tsaye sai ta koma sashen Fulani babba ta sanarwa da Mai gado sa on Mai martaba sannan ta wuce sashen Sailuba don hankalinta ba aramin tashi ya yi ba. Wani irin zafi Fulani babba take ji a cikin jikinta tamkar ana ana mata rodin da ke cikin wuta, daga afarta zuwa irjinta wani abu ne take jin yana yi mata yawo duk inda ta ji abin ya sauka a jikinta sai dai ta ji tamkar yana yagar fatar jikinta. A galabaice murya can asa ta furta. "Mai gado ki taimaka miki, jikina zafi yake don Allah ki taimaka mini mutuwa zan yi." Mai gado ta goge hawayen idonta, "Ranki shi da e ba za ki mutu ba In shaa Allah za ki samu lafiya." Da Baiwa Zainaba ta ebo garwashi ta auko wani turaren miyagu, aka fara turarawa a cikin akin. "Mai gado asana zazzagowa yake ki taimaka za su yage mini asana." Fulani ta yi maganar tana sa hannuwa biyu a asanta tana dannewa, wani irin zuuu ta ji saman mamanta. Ta walla ara cikin azaba tana kai hannu irjinta. " irjina Mai gado, don Allah ki kira mini Takawa ki kawo mini Abubakar zan yi masa kallon arshe." *Littafin ku i ne 500 idan kina bu ata za ki biya ta wannan Account in Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.* Dafa kafa arsa Dattijo Maharaz ya yi sannan ya furta. "Kada ka sare!" Kamalu da kwanyarsa ke barazanar tarwatsewa ya furta. "Don Allah ka rabu da ni na ji da abin da yake damuna." Shiru Dattijon ya yi har zuwa an wani lokaci. "Da alama fushin zuciya na iya yin galaba a kanka wanda hakan zai iya kai ka ga turbar danasani. Da sannu, za ka fahimci abin da nake son nusar da kai." Daga haka Dajjito Mahraz sai ya yi gaba abin sa, har ya an yi wa Kamalu nisa sai kuma Kamalu ya ga rashin dacewar abin da ya yi masa, da sauri ya mi e ya rufa masa baya. Bai san dalili ba amma haka kawai yake jin gaba aya wunin ranar jikinsa babu da i ga wata irin fa uwar gaba da ta saka shi a gaba, ilahirin jikinsa a mace yake don haka koda ya arasa wurin Dattijo Maharaz ya an jingina da wata bishiyar darbejiya kansa na wani irin sara masa. Bayan fitar Jakadiya da kansa Sarki Abdul'aziz ya tashi ya ara gyara rufin labulen akin, haka kawai ya ji wata irin tsanar Fulani babba ta mamaye zuciyarsa. A angare guda kuma rashin kuzarin da ke tare da shi ya haddasa masa ciwon jiki, bayan sun gama tattaunawa da ba in wurinsa ya ji ilahirin jikinsa ya mutu ciwon kai ya lullu e shi, bayan sun tafi kwanciya ya yi saboda yadda tsagin kansa yake ciwo tamkar zai tarwatse masa. Lokaci-lokaci irjinsa na bugawa bai san dalili ba, yana nan kwance bacci ya yi awon gaba da shi. A ranar da Fulani babba ta samu labarin auren Sarki Abdul'aziz da Umaima ba aramin damuwa ta shiga, take kishin mijinta ya mamaye ta amma gudun kada magautanta su fahimci lagonta ya sa ta nuna tamkar abin bai dame ta ba. Lokacin da aka aura auren Fulani Umaima da Sarki Abdul'aziz a sannan Fulani Babba tana da 'ya aya wato Khadija sai kuma tsohon cikin Sakina, don haka Fulani Umaima tun farko ta shiga da niyyar salwantar da abin da yake cikin Fulani babba. Amma da
Chapter 40 · 0% Book details