Sashe 2
Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: irarran labari ne bai faru a gaske ba. Ban yi shi don cin zarafin kowacce abila da Masarautunsu ba. SHAFI NA Masarautar Zazzau (1953) Wani irin zafi take ji yana ratsa ta tun daga tafin afarta har zuwa tsakiyar kwanyarta, dalilin haka ya sabbaba mata karkarwar jiki tamkar wacce ta ji ki an gangi. Wanda hakan ne ya haifar mata gumin da ke tsatssafowa daga kowacce kafar da ke cikin ilahirin jikinta. Ba yau ne karo na farko da haka ya ta a faruwa da ita ba, sai dai a wannan ranar ji take tamkar an saka ta a tukunya ana dafa naman jikinta da ruwan zafi. A hankali ta cije baki tana yarfe hannu ha e da lumshe idanu. Baiwa Maimuna da ke bayanta tana mata fifita cikin warewa a makirci ta fakaice ta, ta yanki asan jelar gashin kanta ani ta yadda ba za ta fahimci hakan ba. Da sauri ta soke shi a jikinta ha e da sauke ajiyar zuciya don ko babu komai ta san ta tsira daga sira in Fulani Umaima. Ta an numfasa a hankali. "Ki gafarce ni uwar akina zan arasa sashen Takawa na ce Jakadiya ta kar o miki magani kamar yadda na ji kin ambata a baya, ranki shi da e lamarin ciwon nan na ki ara amari yake yi amma tuba nake idan da kuskure a kalamaina uwar akina." Ta so musa mata kamar yadda ta yi kafin zafin jikin ya fara galabaitar da ita, dalilinta na yin haka bai wuce yadda take gudun kada Bayin cikin masarautar su fuskanci zaman doya da manjar da ke tsakaninta da Mai martaba ba. Gya a mata kai ta yi ha e da ru o hannunta ta furta, "Idan kin fita Maimuna ki turo mini Baiwa Zainaba." Cike da girmamawa ta russana, "Allah ya ara wa Fulani lafiya, Ubangiji ya bu i ido lafiya ya kawo mana Yarima mai jiran gado cikin yalwar arizi i da oshin lafiya." Da hanzari ta fice a gaggauce don ko ka an ba ta son wargaza shirin oyayyar uwar akinta. Sai da ta turo wa Fulani babba Zainaba sannan ta wuce sashen Fulani Umaima cike da firgici, tana tafe tana waige kamar sabuwar munafukar da ta yi gulma a fada. Da yake Fulani Umaima ta kwana da sanin shirinsu, tun da doshin magriba ta sallami bayinta suka wuce sashensu na bayi. Tamkar wacce aka jefo daga sama haka ta fa akin Fulani Umaima da ke tsaye tana kai kawo don gudun samun matsala a shirinsu, duk da tana da ya inin Baiwa Maimuna ba za ta iya shallake wa umarninta ba. asa ta zube tana sauke numfashi ta furta, "Hutawarki lafiya Fulani mai magajin masarauta, zinariyar Mai martana haskenki bai tsaya iya shi ka ai ba kin haske lungu da sa on cikin Masarauta. Ina gwanar wani ga tawa? Kin yi taki kin yi ta kowa, garna in dutse kike kowa ya ja da ke shi zai fa i..." Fulani Umaima ta katse ta da cewar, "Ina fatan komai ya tafi yadda ya kamata?" Baiwa Maimauna ta saki murmushi, dalilin haka ya sa Fulani Umaima ta sauke ajiyar zuciya duk da ba ta kai ga jin amsar Maimuna ba amma ta fahimci sun yi nasara domin kuwa labarin zuciya a tambayi fuska. "Ranki shi da e an gama aiwatar da komai, ga wannan." Maimuna ta arasa maganar tana kunto gashin kan Fulani Babba ta mi a wa Fulani Umaima. Wani yalwataccen murmushi Fulani ta saki, Baiwa Maimuna ta ci gaba. "Yanzu haka tana can magashiyan har ta umarce ni da na aika Jakadiya ta kar o mata ragowar maganinta a wurin Mai martaba." Wata irin dariya ce ta su uce wa Fulani Umaima wacce ba ta tsammace ta ba, tuna wacce take gabanta ya sa ta tsuke fuska ha e da furta. "Ki jira ni." Uwar akinta ta shiga can ashin gado ta zura hannunta, ta auko wani on kan warangwal. Wani garin magani ta ebo a ciki ta kulle a cikin wata 'yar busasshiyar aramar fata. Ta fito zuciyarta fes cike da takun isa da asaita. Sai da ta koma kan asaitacciyar kujerarta ta zauna sannan ta mi a wa Maimuna. "Ki fara zuwa ki kar o maganin wurin Mai martaba, amma ki tabbata wannan kika ba ta ta yi amfani da shi, za ki zuba mata a ruwa ko abinci kuma ki tabbatar da ta shafe jikinta da shi. Duk dare ina bu atar ganinki domin akwai fitar sirrin da nake so mu yi." Cike da girmamawa Maimuna ta russuna. "An gama ranki shi da e, fansar kaina gare ki ya shugabata domin kai da kaya duka mallakar wuyane. Ki sa a ranki na aiwatar da duk abin kika bu ata na gama, Allah ya taimaki giwar Takawa awusu mai yawan ado." Fulani Umaima ta gya a kai sannan Baiwa Maimuna ta mi e, har ta je bakin ofa Fulani ta furta. "Ki tabbata ba a samu matsala ba, idan aka samu matsala ki kuka da kanki." Baiwa Maimuna ta russuna. "Godiya nake uwar gijiyata." Sai da Maimuna ta aure maganin wurin Fulani Umaima sannan ta nufi sashen Mai martaba, Jakadiya ta samu ta sanar da ita sa on Fulani Babba. Kai tsaye Jakadiya ta tunkari turakar Takawa. Sai da ranga a sallama ha e da kirarin girmamawa sannan ta isar da sa on Fulani Babba. Kamar ba zai amsa mata sai kuma ya mi e ya nufi wata jakar fata da ke sa ale a jikin bango ya zura hannunsa, wasu ullin magunguna biyu ya ciro ya mi a wa Jakadiya, ta kar a tana godiya. Har ta fara tafiya ya furta. "Daga yau a sanar da ita ta ri a kar ar magani kafin almuru, ba a koyaushe muke da bu atar hakan ba." Jakadiya ta amsa sannan ta fice ta dam a wa Baiwa Maimuna tana jaddada mata sa on Mai martaba. Maimuna na shiga sashen Fulani Babba ta same ta kamar yadda ta bar ta, Baiwa Zainaba na gefe tana matsa mata afafuwanta da suka an kumbura. Cike da girmamawa ta mi a mata maganin da Fulani Umaima ta bata sannan ta furta, "Allah ya ara wa Fulani lafiya, Ubangiji ya shiga lamuranki uwar akina. Mai martaba ya ce a ji a rabi, rabi kuma a shafe miki jiki da shi." Idanun Fulani jawur kamar sabon barkono ta bu e su a hankali ta furta. "A yi yadda ya da ce Maimuna." Zuciyar Maimuna al ta tashi jiki na rawa ta ji a maganin kamar yadda Fulani Umaima ta gaya mata, ta taimaka wa Fulani Babba ta tashi zaune ha e da kai mata on bakinta. Tas ta shanye shi sannan Maimuna ta shiga shafe mata a jiki gaba aya, sannu a hankali ta ji wata sassanyar iska na ratsata. Ta koma ta kwanta sakamakon jin da in jikinta da ta fara yi. Ta dubi su Baiwa Maimuna. "Maimuna za ku iya tafiya, Zainaba a tabbata an gyara makwanci su Khadija." Cikin girmamawa suka zube asa, "An gama ranki shi da e, Allah ya ara lafiya ya kawo mana Yarima lafiya." Ba ta iya amsa musu ba sai ma runtse ido da ta yi sakamakon jin wata irin hayaniya da ta yi a tsakar kanta, ga wani irin jiri da ke aukanta. A angare aya kuma wani abu mai tsini ya fara fusgar can cikin asanta. A gurguje Maimuna ta fice ha e da sake ba wa Zainaba umarnin gyaran akin su Khadija da yake ita ce gaba da ita, ta juya ta fice daga angaren 'yayan Fulani Babba. A sanyaye Baiwa Zainaba ta bi Maimuna da kallo don haka kawai take jin zuciyarta na wasuwasi a kan Baiwa Maimuna tun da ta ta a ganinta ta shiga sashen Fulani Umaima sau biyu. Kai tsaye sashen Fulani Umaima ta fa a, kuma a wurin da ta tafi a nan ta koma ta same ta. Fulani Umaima na ganin Baiwa Maimuna ta fa a uwar aki, wani sirrintaccen akwatinta ta auko ta bu e cikinsa. Kamar kullin idan za ta ziyarce shi haka take saka wannan sihirtacciyar rigar da Boka Bamagujen dutse ya bata, a lokacin ma sai da ta tube kayanta gaba aya sannan ta zura rigar mai auke da launin ja, ba i, ruwan orawa da launin ruwan asa. Rigar inke take da wa ansu ananan layu sai kuma wasu ananun rubutu da aka yi da larabci, wani aho ta ri e a hannunta sannan ta fito wurin da ta bar Baiwa Maimuna. Hannu ta mi a wa Maimuna babu musu da yake ta san kwanan zancen ta ora tafin hannunta a saman na Fulani Umaima, wanda ta tabbata ba don wannan sirrintacciyar tafiyar da suke yi ba babu dalilin da zai kai hannunta jikin Fulani Umaima, musamman yadda take nuna yamar bayi da talakawa arara a fili. Saka hannun Maimuna cikin na Fulani babu jimawa, ta runtse idanunta ta aga hannunta da ta ke ri e da ahon ta busa sau uku sannan ta kira sunan Bamagujen dutse sau uku. Wata irin guguwa ce ta kara e cikin akin kamar iftawar ido sai ga su a bakin wani aton farin dutse mai aukar ido, wurin kamar rana tarwai babu abin da ba ka iya gani. Kamar yadda yake bisa al'ada a duk lokacin da suka ziyarce shi, sai da suka saka afarsu ta hagu a tare a kan wani jini da ke malale a gabansu. Sun auki kamar minti biyu a haka sannan suka ji an bushe da wata irin dariya wacce take alamta musu aikin da ya da ce su yi a gaba. afarsu suka sake agawa suka ora a kan wani kabari da ke gaban wannan jinin sannan suka fara takawa suka haye can sama dutse. Zaune suka hango shi babu ko igon sutura a jikinsa, Maimuna ta kawar da kanta gefe don har cikin zuciyarta ba ta son ziyartar wannan shu'umin bokon don dai ba ta da yadda za ta yi ne. Suna arasawa wurin wata aramar bishiyar kuka Maimuna ta russuna tana fa in, "Fatan nasara a kodayaushe ya shugabata." Fulani Umaima ta ci gaba da tafiya don Maimuna ta san ko karen hauka ne ya cije ta