Sashe 36
Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
auren idan namiji ne yake da wannan matsalar har arshen rayuwarsa zai zame wa matarsa tamka bawa, haka idan macen ce ta rasa budurcinta ita ma za ta zame wa mijinta tamkar baiwa sai yadda ya ga damar sarrafa ta. Inna wuro ta gama duk wasu ayyukan da Fulani Umaima ta saka ta don haka ganin ta kammala ya sa ta rafka sallama daga bakin ofar akinta. Shiru ne ya biyo baya hakan ya sa ta sake yin sallama, sai dai can asa- asa ta jiyo muryar Fulani Umaima. Tana son shiga cikin akin amma tsoron kada ta yi laifi ya sa ta ha ura don a yadda kunnuwanta suke jiyo mata kamar Fulani Umaima ba ta da lafiya. "Ranki shi da e shin akwai wani abu da kike bu ata?" Inna wuro ta yanke shawarar fa ar haka ko ta ji daga bakinta. "Maza shigo ina son ganinki." Fulani Umaima ta fa a murya can ciki alamun ta fara galabaita. Jiki na karkarwa Inna wuro ta shigar har uwar akin Fulani Umaima, tana tafe tana kalle-kalle don tun da take ba ta ta a shiga ciki ba. A zuciyarta tana mamakin irin ruwan dukiyar da aka narka saboda tsadaddun kumbayen da ke akin. "Allah ya taimaki uwar akina ko za a sanar da Takawa halin da kike ciki?" Girgiza kai Fulani ta yi, "Ba bu atar haka Inna wuro, daga ke babu wanda yasan halin da nake ciki don haka ban ba da umarnin a sanar da kowa ba." Jinjina kai Inna wuro ta yi ta shiga jera wa Fulani Umaima sannu, ita kuwa ban da numfarfashi babu abin da take yi da sumbatu sama-sam. Da kanta ta nuna wa Inna wuro wurin da ta ajiye reza, zare da wata atuwar ledar sugar. Da sauri Inna wuro ta auko ta shimfi a, ta taimaka wa Fulani Umaima ta hau kai ta tsugunna. Yuuuu haka ta fara jin jiri na arin aukanta, da sauri ta ru afafuwan Inna wuro sannan ta fara jin wasu irin surutai a saman kanta wa anda ta gagar fahimtar abin da ake fa a. Tana daga dur ushe ta ga kamar gilmawar mutum da sauri ta ru o Inna wuro ta ce. "Inna wuro kin ga gilmawar wani?" "A gafarce ni uwar gijiyata babu abin da na gani. Sannu Gimbiyar mata In shaa Allahu, Allah zai bu i ido lafiya." Fulani Umaima ba ta iya amsawa ba sakamakon jin nishi ya taho mata, sai kuma ta ji tamkar an saka farata masu tsini ana fisgar asanta hakan ya sa ta sake ri e Inna wuro nan take jariri ya fa o babu jimawa mabiya ta biyo baya. Inna wuro na kai idonta kan jaririn irrr ta ga ya zuba mata ido yana kallonta babu ko iftawa, sai kuma idanunsa na juya mata kamar ana gara wallo, a haka ta ga ya mayar da idonsa kan Fulani Umaima yana hararta ita ma fuskarsa tamkar ba ta jariri ba, lokaci aya Inna wuro ta ji wani irin tsoro ya kamata da sauri ta kawar da kanta gefe. Babu yadda ta iya haka ta sa hannu ta yanke mabiyar ta na e ta gyara wurin, sai dai idan ba gizau idonta ya yi mata ba har gani ta yi yanayin surar fuskar jaririn tana riki a daga wannan kammanin zuwa wani, a zabure ta sake kai idonta kansa don yadda ta ji faratan hannuwansa sun karce da arfi har sai da wurin ya yi shati, don haka ta yi saurin kawar da kanta gefe gabanta na matsanancin bugawa. Duk wani aiki da Ungozoma take aiwatarwa Inna wuro ce ta gudanar a cikin daren, kafin wani lokaci Fulani Umaima ta fito shar ita da jaririnta. Tun da Inna wuro ta fita wankin kayan da aka ata Fulani Umaima ta auki jaririn ta ura masa idanu, fuskarsa faffa a ce mai auke da an bu an hanci da manyan idanuwansa ma su ban tsoro. Kuma jarirantakarsa ba ta oye jajayen idanunsa ba, lokaci aya ta ji gabanta ya yi mummunar fa uwa don babu ta inda jaririn nan ya auko kamannin Sarki Abdul'aziz ko kuma kammaninta. "Kar dai a ce wannan an Boka Shaddas ne?" Fulani Umaima ta fa a a hankali irjinta na bugawa. Ba ta da amsar tambayarta don haka ta ja bakinta ta tsuke, suna ha a ido da jaririn sai ta ga tamkar harara yake wurga mata, a angare guda kuma yadda kansa yake su al babu ko igon gashi a jiki. Sai da Inna wuro ta gama komai sannan Fulani Umaima ta ba ta umarnin zuwa ta sanar a lungu da sa on cikin masarautar, har zuwa wurin Jakadiya don ta sanar da Sarki Abdul'aziz. Idan lokacin bikin ya zo mutanen Rumzu kan auki kwanaki biyar suna shagali, kuma kowacce rana da kalar dabbar da za su yanka su yi watanda da ita. Sai dai daga amarya har ango ana gasa musu naman tantabaru kullin, don su ba sa cin naman da 'yan biki za su ci. Ana gobe za su tare sai a kai su bakin bishiyar kukar da suke bautawa su yi tsirara su kwana a haka domin ta saka albarka, a kan sabuwar rayuwar da za su fara gudanarwa. Washegari da sassafe sai duka 'yan garin sun taru a bakin bishiyar don yi wa abar bauta godiya sannan a kai amarya da ango akinsu. Tun daren ranar Jawahir ban da tsala kuka babu abin da take yi, duk yadda aka kai ga rarrashinta abin ya ci tura. Haka Mai gado ta saka ta a gaba ita ma ta fara zubar da walla don a tsammaninta wani abu ne yake damun Jawahir. Sai kusan doshin asuba sannan ta samu bacci ya yi awon gaba da ita. Ayarin wa ansu ba en mutane ya gani tafe sun dunfaru sashen Mai martaba hannuwansu auke da miyagun makamai, cikin san a yake biye da su da zarar ya ga za su waigo sai ya yi saurin la ewa a wani lungun. Yana biye da su har suka shiga akin Mai martaba, ta gefen da yake hangarsu wani jariri ya gani fuskarsa sam ba ta yi kama da ta ainihin jarirai ba. Yana nan tsaye ya ga jaririn ya dira a gaban Takawa. "Ni ne ajalinka wallahi sai na kashe ka na kashe duka mutanen masarautar nan! Sai mun kafa sabuwar da'ira ni da mahaifina domin wannan masarautar ba ta dace da shi ko kai ba. Mahaifiyata Fulani Umaima ce, ita ma ba zan bar ta ba har sai na hallaka domin na tabbata nan gaba tana iya hallaka mahaifina." Yana gama fa ar haka ya bushe da wata irin dariya, daga cikin bakina wani ba in jini ne ya fara iga. Jin motsin Kamalu ya sa gaba aya suka kallo wurin da yake oye, suka dunfaro shi gadan-gadan da niyyar hallaka shi. "Kamalu! Kamalu me yake damunka?" Kalaman Baffajo suka tashe shi daga mummunan mafarkin da yake yi. Ya ha a gumi sharkaf jikinsa sai karkawa yake, tsoro arara ya bayyana a idonsa. Da sauri Baffajo ya rungume shi a jikinsa ya fara tofa masa addu'a sai da ya ga Kamalu ya dawo cikin nutsuwarsa sannan ya ago shi ya ce. "Mafarki ka yi ne Kamalu? Kullin fa ina gaya maka idan za ka kwanta ka auko wannan layar da na baka ka saka ta a asan kanka. Dubi hannunka kamar ka Kamalu a ce ko guru babu a jikinka, an ya kamalu rayuwa za ta tafi haka?" "Baffajo za su kashe Mai martaba, wallahi har mutanen masarautar nan gaba aya ni ma gab nake da su kashe ni. Kuma jaririn ya ce mini wai an Fulani Umaima ne, shi ne yake fesar da jini wallahi har kaina ya nufo zai hallaka ni." Ya arasa maganar yana cusa kansa a cikin afafuwansa. A wannan karon jikin Baffajo ba aramin sanyi ya yi ba, fargaba ta dirar masa da jin kamalan Kamalu na arshe. Ya dafa kafa arsa. "Ka yi shiru Kamalu kada ka saka mu a matsala, ka daina ambatar sunan iyayen gidanmu idan aka ji kashinmu ya bushe. Babu wata halitta da za ta iya cutar da mu In shaa Allah. Idan Allah ya kai mu gobe zan shiga dawa na ha o maka turaren miyagu da wamai ka ji." Kai kawai Kamalu ya iya gya awa amma har lokacin irjinsa bugawa yake. Tun a cikin daren Inna wuro ta fita ta sakin gu a tana shelar haihuwar Fulani Umaima, kafin wani lokaci gaba aya maganar ta kara e cikin masarautar. Mai martaba da ya ji maganar ya nuna farincikinsa sai dai babu wani oki da nuna zumu in irin wanda ya yi a lokacin da ta haifi Muhsin. A yanzu babba burinsa bai wuce ya ga Allah ya sauki Sailubansa lafiya ba. Bayan Inna wuro ta gama shelar tana komawa wurin Fulani Umaima ta sallame ta tare da yi mata al awarin babbar kyauta zuwa wayewar gari. Tun da farar safiya Inna wuro da sauran Bayin Fulani Umaima suka shiga yi mata hidimar ora ruwan wanka da abin da ba a rasa ba, Fulani babba ma tun da wuri ta shiga yi mata barka sai dai ita kanta Fulani Umaima a asan zuciyarta kunyar nuna wa mutane jaririn take don gani take kamar wani zai yi mata wata fassarar, ko a gano jaririn ba jinin Takawa ba ne. Tun a ranar da ta haife shi wani abu ya nemi aure mata kai, idan ta fita zuwa ban aki ko yin wani uzurin, tana dawowa za ta ci karo da oyayyun kayan tsafinta a gefen jaririn. Wani lokacin ma har akwatin da ta ajiye littafin da Bamaguje ya ba ta take ganin a kawo ta tsakiyar akin, idan zuma ta ajiye ko nono da kunu suma haka za ta zo tarar an shanye kusan rabi ko fi ma. Wani lokacin kuma a yi mata faca-faca da shi a ata mata aki, tsoro-tsoro ta fara ji don idan take bin jaririn da kallo kuma ir haka za ta ga ya kafe ta da ido yana kallo. *Fulani Umaima ta samo daidai da ita.* SHU'UMAR MASARAUTA *Littafin ku i ne 500 idan kina bu ata za ki biya ta wannan Account in Aisha Adam 3090957579 First bank