← Book details Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 89

Sashe 14

Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

an matashin ne mai kimanin shekara goma zaune a cikin fadar Sarki Abdul'aziz a kan shimfi iyar shimfi ar alfarma yana sanye da rantsattsiyar alkyabba. Kallon mutane yake yi ai fuska a murtuke babu walwala, kallo aya za ka yi masa ka tabbatar da mulkin gadarsa ya yi ba taka-haye ba. Gajiyar da ya yi da zaman cikin fadar ya sa ya mi e cike da izza yana taku kamar ba zai taka asar ba. "Takawarka lafiya Yariman masarauta, a huta lafiya sarkin gobe da yardar Allah." Fadawa suka auka a lokacin da suka lura Muhsin ya mi e da niyyar fita daga fadar, wasu daga ciki suka arasa suna take masa ba. Hannu ya aga ha e da tsayawa wuri aya cak, ya kusa minti aya a haka sannan ya furta. "Ba na bu atar rakiya." Lokaci aya suka ja da baya sannan ya ci gaba da taku, duk hanyar da ya bi haka bayi da fadawa suke zubewa suna kwasar gaisuwa amma ko kallansu ba ya yi ballanta su saka ran zai tanka musu. Yana gab da shiga sashen mahaifiyarsa bisa tsautsayi wata baiwa ta fito da sauri don isar da sa on Fulani Umaima, a rashin sani ta bangaje shi har sandar hannunsa ta fa asa. Jiki na karkarwa ta zube asa. "Tuba nake shugabana, a gafarce ni uban gidana ni mai laifi ce ba tare da..." Marin da ya auke kuncinta da shi ya sa ha oranta suka datse harshenta har sai da bakinta ya fashe, idanunta suka fara zubar da walla ta sake zube wa a asa tana fa in. "Godiya nake Sarkin gobe." aga kansa ya yi ya hango wani Bafade hannunsa auke da murtukekiyar bulala ya furta, "A hora ta na tsawon wuni guda da alama ba ta gama sanin a gidan masarauta take rayuwa ba tun da ba ta san aikinta ba." Yana gama maganar ya wuce ba tare da ya jira cewarsu ba. A kishingi e ya tarar da mahaifiyarsa tana huatawa, wasu 'yan matan Bayi na tsugunne wurin afarta suna yi mata tausa. Ganin yanayinsa ya sa ta tashi zaune ha e da sallamarsu. "Wa ya ata ranka Muhsin?" Fulani Umaima ta tambaye shi. Bai tanka mata ba sai da ya zauna. "Wata baiwarki ce ta ata mini rai amma komai ya wuce." "Wace ce ita na sa a hukuntata?" Muhsin ya fara rage kayan jikinsa. "Na sa a hukuntata, ina Ru ayya ban ganta ba?" Fulani Umaima ta yamutsa fuska, "Za ta wuce sashen Fulani babba ne, yarinya sai ba in nacin tsiya kamar tsohuwar mayya." Take idanunsa suka yi jawur rai a matu ace ya saki guntun tsaki, ba tare da furta komai ba. Ihun da Ru ayya ke wallawa ne ya ja hankalin Fulani babba da sauran bayin da ke harabar gidan, turus bayin suka yi suna kallon juna duk da ba yau ce rana ta farko da suka ga Abubakar na kama gashin duk wani mutum da ya kusance shi ba ciki kuwa har da mahaifiyarsa. Ru ayya anwar Muhsin ce ita take binsa shekararta bakwai a duniya, Allah ya ha a jininta da Abubakar ba ta iya wuni guda cir ba tare da je sashen Fulani babba ta shiga akin Abubakar ta tsaya yana yi mata gwaranci tana mayar masa ba. Babbar matsalar da ke damun Fulani Babba bai wuce yadda Abubakar yake cizgar gashin kansa yana ci ba, idan na kansa ya are kuma duk wanda yake da tsautsayi idan ya dam e ka haka zai dinga cizga har sai an kwace ka. Abubakar ya shiga shekara ta goma sha aya, sai dai har lokacin a zaune yake ko motsi ba ya iya yi komai sai an yi masa. Fari ne sol kamar mahafiyarsa sai dai kammaninsa sak da Sarki Abdul'aziz, tun da ya taso ba ya iya magana sai dai gwaranci kuma har kawo lokacin yawu na dalala daga bakinsa. Idanunwansa duka biyun a juye suke, hannuwa da afafuwansa suma a shanye suke babu abin da yake iya aikatawa hatta wanka da tsarki yi masa ake yi. Fulani Babba da sauri ta arasa gaban Abubakar ta sa hannu cike da unan rai ta auke fuskarsa da mari, wannan ne karo na farko da ta ta a sanya hannu a jikinsa da sunan duka. Zafin marin ya ratsa shi hakan ya sa ya arasa cizge kitson kan Ru ayya da ke bakinsa, sai kuma ya fashe da kuka yana gwara kansa da asa. Cikin azaba ta sake walla ara take numfashinta ya auke ta sume a wurin. Tamkar mayuwancin zakin da ya samu nama haka Abubakar ya tura sillin jelar kitson kan Ru ayya da ya cizge cikin bakinsa ya fara tauna kafin wani lokaci ya ha iye shi gaba aya. A firgice Fulani Babba ta shiga yayyafa wa Ru ayya ruwa ta jima a kanta sannan ta sauke ajiyar zuciya a galabaice, ganin ta bu e ido ya sa Fulani Babba ta ji farinciki har cikin ranta sai dai kuma wurin da ya aye mata kitson tuni gefen kan ya kumbura suntum. Wani irin sara ta ji kan yana yi mata a daddafe ta iya mi ewa ganin haka ya sa Fulani ta ba wa Bayin da ke gefe umarnin su auke ta zuwa cikin turakarta. Duk dauriya irin ta Ru ayya sai da ta dinga zubda walla sakamakon yadda take jin kanta na sara mata kamar zai tsage gida biyu. Duk yadda Fulani babba ta so zaman Ru ayya a akin zuwa lokacin da zugin zai sarara mata fir ta i yarda, don haka ta sake saka Bayi suka auke ta tana gaba suna biye da ita a baya har cikin sashen Fulani Umaima. Ganin a halin da aka shiga da Ru ayya ya sa Fulani Umaima mi ewa zumbur! Bakinta har rawa yake ta furta. "Me ya faru da ita?" "Laifi ne yayanta Sadik ya yi mata, wallahi tsatsayi ne Fulani don haka na zo da kaina ba sa o ba..." "Dakata Fulani! Hawainiyarki ta kiyayi ramata. Ba tun yau ba na lura da take-takenki dangane da kiranyen da kika yi wa Ru ayya. Lokaci aya kin sa an lashe kurwar yarinya ba ta aunar zaman wurin mahaifiyarta, wannan fa ba shi ne karo na farko na ji labarin wancen shagirigirbau in ya ma ure ta yana yi mata amshin mutuwa ba. Amma an yi ta yanke ta gille, wannan shi ne karo na farko kuma na arshe da zai sake ta a kowanne bil'adama a sashenki." Fulani Umaima ta arasa maganar tana kai kallonta wurin bayin da ke ri e da Ru aya. "A samu Jakadiya ta gaggauta sanar da Mai martaba ina bu atar wararrun masu magani, don ban san dafin da ha oransa suke auke da shi ba." Da sauri suka shimfi ar da ita suka fice, Fulani Babba ta arasa gabanta ido cike da walla ta furta. "Wallahi ko a mafarki ban ta a jin Ru ayya ba 'yata ba ce, tamkar yadda na auki su Khadija haka nake jin ta, ta ya ina sane zan bari Abubakar ya illatata." Sai da Fulani Umaima ta saki murmushin takaici ta furta, "Me ya sa bai kama Khadija ko Sakina ya illata ba, saboda kina ba incikin kin haifi sauna, wawa, shashasha shi ne ni ma kike burin arfi da yaji na rasa wa annan biyun da Allah ya ba ni." Tsoron hukuncin da Fulani Umaima za ta yanke ya sake mamaye Fulani babba, ta tsugunna bisa gwiwoyinta don ta san kome Fulani ta gaya wa Takawa hawa yake ya zauna aram. Ba tun yanzu ba ta jima da dawowa daga rakiyarta, don ta lura sai abin da Fulani Umaima take so Takawa yake zartarwa. "Tabbas Abubakar bai kyauta ba amma ki dubi girman Allah ki yi ha uri..." "Idan ba ki yi gaggawar fita daga sashena ba wallahi sai na shayar da ke ruwan mamaki." Fulani Umaima na gama magana ta yi ciki cike da zafin rai. Fulani babba ta sunkuyar da kanta asa tana zubar da walla, dama ya ya lafiyar kura ballantana ta yi zawo. Gari banza ma Takawa ba aunar Abubakar yake ba ina ga an ce ya ta a 'ya'yan gaban goshi. Cike da zullimi ta fara yun urin tashi, daga bayanta ta hangi Muhsin na zaune yana aika mata da sa on harara cikin kallon tsana. A haka ta arasa sashenta gwiwoyinta a sanyaye, ta windo ta le a Abubukar da ke zaune yawu na dalala. Sai a lokacin ta samu damar fashe wa da matsanancin kuka duk da tana da tabbacin bayin da ke zagaye da ita suna sauraronta. "Ya Allah ba don ba ka so ko aunata ka jarabce ni da wannan bawa Naka ba, Ya Ubangiji ina godiya bisa baiwa da wannan ni'imar da ka yi mini domin dubbunaina na bu atar ko da makamancinsa ne. Ya Allah idan rayuwar wannan bawa naka mai tsayi ce Ubangiji ka yalwace shi da lafiyar ya zama kamar kowa, sa anin halin da yake ciki. Idan kuma mai gajeren kwana ne Ubangiji ka gaggauta aukar kwanakinsa ko na samu salama a rayuwata..." Kukan da ya ci arfinta ne ya datse ragowar kalamanta. "Allah ya sanyaya zuciyar uwar akina Ubangiji ya ara wa Yarima lafiya." Baiwa Zainaba ta furta jiki a sanyaye kamar kazar da tono wu "Zainaba na auka ko kowa zai furta son ransa ke mai fa a mini gaskiyar abin da ke cikin zuciyarki ne? A haka kike kiran Abubakar da Yarima kina ga ko a mafarki za a dam a wa Abubakar karagar mulki ne." Tabbas kalaman Fulani Babba a turba suke domin kowa ya san halin da Abubakar yake ciki kuma ko a garin ga a-ga a babu wanda zai dam a masa kujerar sarauta, ina ya san kansa ma balle ya san matsalolin talakawa? Sai da ta ara rissinawa ta furta. "Tuba nake ranki shi da e, In shaa Allahu Allah zai ba shi lafiya." Fulani babba ta amsa mata sannan ta wuce cikin sashenta. Ganin har zuwa dare babu wani sa o ya sa Fulani babba ta an fara sakin zuciyarta, har ta zauna su Khadija na soko mata hira wani ta amsa musu wani kuma ta yi musu shiru. Suna cikin wannan yanayin Jakadiya ta iso
Chapter 14 · 0% Book details